💧💧 *TAWA K'ADDARAR....💥*
💥
*HASKE WRITER'S ASSO💡*
(Home of expert & perfect writers)*NA FEEDOM*💞
*Wattpad:Feedohm11**Bestowed to Aunty Sis💕*
*04*Matashin yayi gyaran murya yace "Farouk kasan Abunda Abba ya aikata?
Girgiza kai yayi a hankali yana kallonshi……
"Kasan pastor'n nan dake kallon gidana ?Bro ya tambayeshi……Gyad'a kai yayi yana fad'in "Na sanshi Bro ba dad din su patricia ba?
"Farouku jiya wajen karfe 10 na dare aka kirani wae anga Dady yana shiga gidan idan mijinta ya fita kullun sannan har ake fad'a man cewa neman matar aure yake da zina !Farouk zina fa !Imagine Zinar ma da matar aure christan?
Dafe Kai yayi kamar gaske sannan ya dago idanunshi yana fad'in"Subhanallah ……!
Sun fi tsawon minti goma babu wanda yayi magana sannan Bro ya katse shirun ta hanyar tambayarshi mafita ……
Sun dade suna tattauna maganar sannan ya dauko kud'i masu yawa ya bashi ya mike !Har zaya fita Matar Bro din ta fita cikin jallabiya bak'a ……Cikin fara'a suka gaisa da Farouk sannan ta shiga kitchen ta dauko mashi lemu da ruwa ……Sae da suka d'an tab'a fira sossae sannan ya mike ya mashi bankwana ……Da yake suma cikin GRA din suke cikin minti 5 ya isa gida !Shima k'aton gidane kamar na Bro banbancin kawae babu sojoji irin nashi da yake shi bro din Major general ne……
Maigadi ya bude mashi gate yana daga mashi hannu amma ya dauke kai ba tare da ya kalleshi ba !Cikin gidan ya nufa ya fara iske katon falo sannan yayi gaba kad'an ya isa wata yar siririyar hanya da ta sadashi da wani part dake tsakiyar hanya ……Knocking yayi kamar zaya balle door din daga ciki aka ce "Come in……"
Sannan ya bud'e kofar ya shiga ba tare da sallama ba !Wani dattijo mai yawan shekaru ke zaune tsakiyar falon saman rug daga shi sai boxer baki……Yayin da kwalbar Wine ke aje a gefenshi ……Zube wayarshi yayi saman kujera sannan ya zauna shima a rug din ya ja kwalbar wine din ya tsitsiya a cup ya sha ……
Idon dattijon na rufe yace "Deebo……"
Amsawa yayi sannan ya jingina da kujera yana fad'in "Brother Ali ya kirani dady……"Dady ya bud'e idonshi tangaram yana jefa mashi harara yace "Me yace maka……"
Tabe baki yayi sannan yace "Shareshi dady……"
"Nak'i na sharen dan ubanki ! Wato Deebo har da kai ake zagina ko……?"Yo wa yace zaginka akayi……" ya fada yana tamke fuska
"Idan ba zagina kukayi ba Uban me zai hana ka fad'a man abunda yace ……"ya fad'a cikin d'aga murya……
Yar dariya Deebo yayi k'asa k'asa sannan yace "Kawae yana fada man wae kana neman matar pastor chuku ne ……"
Tsaki dady yayi yana fad'in "Wallahi Sae na ci Uban Ali ……Banda yana shegen yaro taya zai dinga saka man ido kamar shi ya haifeni……"Deebo kam yatsina fuska yayi sannan yace "Kar ka ce ni na fad'a maka gaskia ……"
Banza yayi dashi ya mike ya dauki rigarshi ya saka ya fita……
【】Kwanan Fadila biyu gidansu Anup sannan Uncle Jawwad yazo daukarta Suna jin horn din motarshi Anup ta jata da gudu suka shige dakinta ...
Uncle Jawwad kam sae da ya tsaya suka gaisa da Ummi dake falo tana masu dariya sannan yace "Zan tafi da Anup ..."Cikin mamaki ummi tace "Anup fa Jawwad!kasanta sarai kai da kanka zaka maidota..."
Murmushi yayi mike ya nufi dakin...
"Fadila ki yi ta sallah har ya gaji ya tafi kin ji……"Cewar Anup tare da wulla mata katuwar hijab d'inta ……
Karb'a tayi ta sanya da sauri tare da kabbara sallan wanda yayi dae dae da shigowar Uncle Jawwad……
Kallo d'aya ya masu ya gane basu da gaskia yayin da ya tsaida idonshi akan fadila da ta zabga sujuda ……Cikin Sauri Anup ta tace "Raka'atanul fijir take Uncle jawwad..."ta karashe maganar tana washe baki ...
Spreading arms dinshi yayi hadi da tabe baki yace "Shikenan tunda sallah kike ,Gobe Abbas zai zo ya daukeki ! Jawahir bye……"ya karashe maganar yana daga mata hannu
Dage gira tayi tana washe baki tare da daga mashi hannu "Bye……a gayar da granny ……"
Har ya juya ya tsaya ya juyo yana kallon Anup da ta kasa tsayar da kafafunta guri daya ya kira sunanta "Jawahir……"Washe baki tayi tace "Uncle jawwad……"
"Is ok ma kawae……"ya fada tare da juyawa
Binshi tayi tana fad'in "Menene Uncle Jawwad?
Ba tare da ya juyo ba yace "Ku barsa kawae ……"Da yake tasan yana saya masu kayan zaki ko da yaushe sae ta bishi da nacin sae ya fad'a mata dalilin kiranta da yayi ……
Har ya kai bakin mota sannan ya tsaya hadi da dafe kai yace"Kinga karki dameni dan Allah !dama wata plaza ce dazu naga an bude kuma an,kawo chocolate masu yawa shine fa na kiraki ko zamu je sae,kuma naga Fadila na sallah ……So na fasa!
Waro Ido tayi tace "Bara na kirata muje……"
"No……"ya fada a takaice
Da Sauri ta koma cikin gidan tana fadin "Wallahi ba sallah take ba……"
Bayanta yabi da kallo har ta shige gidan !mintina kadan ta dawo janye da fadilan ta bude masu mota suka shige ba tare da sun mashi magana ba ……Gyada kai yayi ya shiga shima ya tada motar suka fita ……
"Uncle Jawwad a ina take……?ta fada tare da matsowa jikin kujeranshi ……"Gidan granny……" Ya bata amsa kai tsaye ……
Saurin kallon Fadila tayi kamar had'in baki suka kaiwa juna duka !
"Uncle jawwad dan Allah ka ajemu sae mu koma kasa……"Cewar Fadila kamar zatayi kuka……
Banza ya masu ya kure volume yana bin wakar a hankali yayin da sukayi tsuru tsuru ……Bakin cikinsu daya ba'a fita ko compound a gidan granny……Gidan ya wuce dasu tayi parking ya fito ya,barsu a mota sae da suka ci zamansu sannan,suka fito rike da hannun juna ……
A Falo suka iskeshi zaune harda granny ……Tana ganin Anup ta waro ido cike da mamaki don ta rabu da ganin Anup din
"Jawahir ……anya ke ce kuwa"
Gyada kai tayi kamar ta fasa kuka don ko,kadan bata kaunar tayi,nesa da Umminta kuma tana sane Uncle jawwad saboda mugunta ya taho da ita ……
Fadila kam zuburar baki tayi ta kama hannun Anup din tayi dakinta da ita !duk walwalarta ta bace yayin da ta koma kalar tausayi ……Rau rau tayi da ido tana kallon Fadila dake ta kwaso mata teddy don duk ta saki jikinta tace "Fadila Ummina……" ta karashe maganar idonta cike da hawaye
Cikin sanyin murya fadila tace "Anup zan kawo maki milk da zuma idan kika zauna kin ji"
A hankali ta girgiza mata kai tana share hawayen da suka zubo mata da bayan hannu !Kamar Fadilan tayi kuka tace "Anup dan Allah ki zauna……"*Feedohm*💞

YOU ARE READING
TAWA K'ADDARAR......
RomanceLabari ne na wata Yarinya da ta tashi cikin gata da kulawar iyayenta lokaci guda duniyar ta juya mata yayin da ta hadu Kaddara ta rasa dukkan iyayenta Sanadiyyar gobar da ta cinyesu harda karamar kanwarta !ta dimauce ta rasa duk wani tunaninta!Ta ra...