TAWA K'ADDARAR 6

1.5K 95 10
                                    

💧💧 *TAWA K'ADDARAR....💥*

                      💥

*HASKE WRITER'S ASSO💡*
(Home of expert & perfect writers)

     *NA FEEDOM*💞
   *Wattpad:Feedohm11*

     *Bestowed to Aunty Sis💕*

           
                     *06*

Soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu kasancewar itama ma Abbanta a FAAN din yake aiki kuma Al mustaphan na yawan zuwa gidansu!Basu sha wahala ba gurin yin aure saboda su duka suna da toshe mai kyau……

Bayan sunyi aurene suka zauna a Asokoro zaman su gwanin ban sha'awa suna kokarin kyautatawa juna……Lokacin ummi tana matakin karshe a karatun a School of nursing ta Abuja don haka tana gawamawa ta samu Aiki a Turkish internation hospital Abuja……A Shekara ta daya da aurensu Allah ya bawa Ummi ciki ……Farin ciki gurin family din ba sae an tona ba……

  Tunda Uncle Jawwad ya kyal ido yaga Ummi na da ciki ya sauki son duniya ya daurawa cikin Tun cikin nada Wata biyu akayi scanning aka ce macace a ciki!Ranar Uncle Jawwad kasa cin abinci yayi wai shima zai samu dauhgter saboda ba'a tab'a samun jika a family d'insu ba! haka yayi ta bincike sae ya samo sunan mace mai irin sunanshi an sa mata idan Ummi ta haihu !Hajiya ta kirashi tace ta samo mashi JAWAHIR ya kwantar da hankali ……

  Shekarar su biyu da Aure Allah ya azurtasu da yar d'iyarsu kyakykyawa JAWAHIR suke kiranta da ANUP Ma'ana Happiness……Tunda aka haifi yarinyar Uncle Jawwad ya dauki son duniya ya daura mata !Bai yarda Anup tayi kuka ba indae yana gurin in kuwa akayi rashin sa'a yaji kukanta to shima zaka ga yan guntun hawaye a idonshi!Tun ana mashi fad'a har aka daina don komae Jawwad ya samo to na Anup ne !Lokacin yana secondary school ko kudin break Granny ta bashi to baya iya kashe ko naira biyar haka zai kwaso mata biscuit da sweet ya kawo mata sannan ya wuce gida ita kanta Anup din bata yarda da kowa sae Jawwad don kusan dawowa yayi gidan yana rainonta……

  A Lokacin har janshi ake da ya shigo gidan sae Ummi ta matsa wata teedy ta dinga tsuwa shi kuma sae yayi tunanin Anup din ce ke kuka haka zai ta bala'i har sae ya shigo ya ga teddy ce sannan ya juya ya bar gidan ……

  Shakuwarsu ta rage lokacin da ya tafi karatu Capella University USA inda yayo Mastering in criminology shekara 5 sannan ya wuce yayi training na Air marshal a Mexico na shekara 2 inda ya fito da THREE STAR AIR OFFICER AS A AIR CHIEF MARSHAL……A Lokacin da ya dawo Anup ta girma tana shekara 8 da wata Hudu sannan ga wata kwallafa ta iyayenta da Allah ya daura mata ko kad'an bata iya nisa da iyayen nata kullun tana like dasu!Yarinyar ta tashi cikin gata ta tarairaya bata san menene babu ba A rayuwarta amma hakan bai hana iyayenta bata tarbiyya ba……

Don Akwae lokacin Dad ya dauketa ya kaita Kaduna ta masu sati daya amma washe gari Malan yayo mashi wayar Anup na asibiti kwance haka suka bi private jet suka koma Kaduna suka daukota !Gidan Hajiya da Granny kam iya karta su je da Ummi su dawo ranar bata yarda a barota !Lokacin har cewa akayi a nema mata magani ko aljanun k'alale suka shafeta amma aka ce akwae irin wad'anda Allah ke daurawa kwallafar iyayensu ……Tun abun na damun Ummi har ya daina damunta……

  Lokacin da aka sakata makaranta ranar farko da ta wuni bata ga iyayenta ba sae da tayi zazzabi na tsawon kwana uku!Duka family din suna mamakin Kwallafa irin ta yarinyar ga shegen wayau da Allah ya zuba mata ……

  Dawowar Uncle Jawwad ce ta sata zama a school saboda komawa yayi kamar teacher a school saboda ya kan fidda lokacin ya je school din har ya dan shiga class dinsu da yake yana da friends a teacher din kuma duk sun sanshi sae dae idan yana da aikine sossae yake tafiya office din ……Ko a makarantar Allah ya zuba mata ruwan farin jini matsalar kawae bata maida hankali ……
  Idan aka bada result to ka tsammaci Anup a last ko second to the last !Tun Iyayenta na jin haushi har suka daina!Uncle Jawwad kam takan sha rankwashi duk ranar da aka bada result ……da ta k'ara wayau sae ta fara goge number farko ta result dinta ko ta karshe ……

  Fadila kam Diyar kanin Abban su Uncle jawwad ce !Babanta bae dade da rasuwa ba Uncle Jawwad ya maidota gidansu gurin Granny sannan aka mayar da ita school din su Anup! da farko Anup ta fara jin haushinta ganin Uncle Jawwad na mata magana saboda bata kaunar ta ga koma na kula mata Uncle dinta a school……Sae da taje gidan granny ta ga Fadilan sannan suka kulle ……
  Sosaae Uncle Jawwad ke taka rawa a rayuwar Anup expecially ta bangaren school!Duk da irin son da yake mata hakan bai hana ya mata duka a school idan tayi rashin ji ba……

  Haka suke rayuwa gwanin ban shaawa har Ummi ta sake samun wani cikin !Wannan karon Murnar ta Anup ce don duk mutanen da take magana dasu sae da suka san Umminta na da Unborn……

《》《》《》
 
  360 Ya danno hancin motarshi dae dae bakin gate ya tsaya sae Uban horn yake kafin ya bude motar a fusace ya shiga gidan yana kiran "Barau!Barau!!

  Barau ya fito daga toilet zariyar wandoshi a hannu ya zube kasa yana a rude yana fadin"Dan girman Allah kayi hakuri wallahi gudawa ta kamoni sam banji karar motarka ba……"

Mari ya daukeshi dashi a fusace yana fad'in" Gudawa aka kawoka kayi koko gadi……?

  Dafe gurin Barau yayi ya sadda kai k'asa ……
A Wulakance Deeboo ya wulla mashi keys din motar ya tsallakeshi ya shige ciki……Matashiyar budurwace wanda kallo daya zaka mata ka gano Kamarta da Deeboo din zaune ita da friend d'inta a falon!Tana ganinshi ta mike tare juya mashi baya ……

  Murmushi yayi Mai sauti kafin ya karasa ya rungomota ta baya yana fad'in "Pardon!
Shiru ta masa sae turo baki take ya juyo da ita tana kallonshi " Kalleni Meela kina tunanin yayanki zai manta dake ne……?

  A Shagwabe tace "Amma Ai na fada maka yau zan dawo shine baka je ka dauko ni ba!ka ja man raini gurin Friends dina suna tunanin ma karya nake banda kai……"

  Hade hannayenshi yayi yana fad'in "Afuwan Meela wallahi wani committee muka hada za'aje da'awa wani kauye so duk yau acan na wuni ……"

  Waro ido tayi tana murmushi "Wow Bro Farouk ashe har yanzu kana nan da son addininka "
  Murmushi ya mata ya juya gurin kawar ya daga mata hannu yana fad'in "Hey……"
Sannan ya wuce……
Kitchen ya shiga ya tarad da wata dattijuwa na yankan fruits Kallo daya zaka mata ka tabbatar da gogewarta ta duniya!Skin dinnan ansha bleaching har wani furu furu take!Ga uwar H a saman goshinta da hujen hanci da yasha ado da stone na gold……

  Kallon raini suka watsawa juna kafin yace "Aunty me zan samu……?
  A Banzace ta kalleshi kamar yarda ya mata tace " Bisi bata nan!Hinde ma batta nan!
  Karamin tsaki ya saki sannan yace "Huh……"
Kai tsaye tace "Sae a tafi ko?tunda babu baiwa a gidan!

  Dariya ya saki mai cin rai yana mata kallon uku saura kwanta !Yayin da ya tsayar da idonshi a kan kirjinta dake shafe kamar silifas ya tun tsire da dariya harda rike ciki yana fad'in" Dady da kwashe kwashe har da Kwaila a ciki!

  Kamar ta saki ihu ta jehoshi da knife din dake hannunta yayi tsalle ya matsa yana dariyar mugunta……

  *FAROUK DEEBOO……*

UMAR FAROUK YUSUF EZIKWE……Shine asalin sunanshi !Yan asalin garin Kebbi ne aiki ya kawo Ubansu ILORIN……Mahaifinsu attajiri sae dae irin wadannan gogaggun yan duniyar ne wadanda suka mayar da mace ba abakin komae ba……Yana da ya'ya a kalla sunfi ashirin wadanda ko wane da uwarsa ABUBAKAR DA FAROUK SAE JAMEELA Su kadaene suke uwa daya uba daya amma sauran ya yan ko wane da uwarsa saboda da zaran mace ta haihu yake sakinta !Ita Mahaifiyarsu Farouk Allah ya zuba mata ruwan hakuri shi yasa har ta haifi ya'ya uku a tare dashi kafin wahalar ta mata yawa ta fita ta bar mashi yayanshi sabanin sauran matan dake tafiya da nasu ya'yan !Dae dae gwargwado Mahaifiyarsu ta basu tarbiyya kafin ta fita amma tana barin gidan tarbiyyar yaran ta fara rawa!Abubakar da Jameela ne kadae suka rike tarbiyarsu sab'anin Farouk da ya dauki halin Ubanshi sak……

  Farouk irin mutannan ne da suke nuna su na Allah ne a gaban wasu amma a zahiri babu wanda ya kaisu iskanci!Farouk kyakykyawane ajin farko ga farin jinin yan mata da Allah ya daura mashi!Maganar ilimi kam ba'a nigeria sukayi karatu ba Abubakar kam ya tsaya yayi karatu sossae inda yanzu yake a matsayin Major general yayin da Farouk kam ko da ya tafi America karatun duniya yayo ya dawo a matsayin cikakken dan bariki ……!

Feedohm

TAWA K'ADDARAR......Where stories live. Discover now