💧💧 *TAWA K'ADDARAR....💥*
💥
*HASKE WRITER'S ASSO💡*
(Home of expert & perfect writers)*NA FEEDOM*💞
*Wattpad:Feedohm11**Bestowed to Aunty Sis💕*
*05*Still girgiza mata kai tayi tare da mikewa ta fita falon ……
Granny na ganinta ta tab'e baki don ta san sarai Anup ba zama zata yi ba !Yarinya ce mai kullafar iyayenta ……Kusa Da Uncle Jawwad ta zauna tana kallonshi tare da share hawayen da dukkan hannayenta !banza ya mata kamar bai ganta ta ……Kuka ta fara rairawa a hankali tana kallon Fadila dake tsaye bakin kofa ……
"Jawwad me yasa ka dauko man wannan yar banzan yarinyar bayan kasan shegen kwallafa ne da ita……"Granny ta fad'a tana hararan Anup din ……Shima hararan ya watsa mata yana fad'in "Barta granny wallahi sae ta kwana a nan yau !Sae dae ta mutu……"
"Kayi Hakuri ……" ta fada cikin kuka……
"Shut up!Dukanki akayi……?ya fad'a tare da sake mata harara……Fadila ta matso ta ja hannunta amma taki mikewa ta tsaya tana kallonsu ……
Takaici ya ishi granny ta mike ta bar masu falon yayin da Uncle Jawwad ma ya haye upstair ya barsu tsaye……Duk yarda Fadila taso ta lallashi Anup kin yin shirun tayi sae ma bin Jawwad da tayi dakinshi ……Bude kofar tayi a hankali ta shiga sannan ta mayar ta rufe ta zauna jikin kofar ta had'e kafafunta tare da tallabe kumatunta ta har lokacin tana hawaye ……Kallon daya ya mata ya watsar ya dauki towel a hannunshi ya shige toilet ya barta !wani sabon kukan ta sake a hankali har da shashsheka ……Yana wanka amma sam hankalinshi naga Kukanta da yake ji har cikin ranshi ……Fitowa yayi daure da towel ya dauki jallabiya fara ya koma toilet din ya sanya sannan ya fito ya tsaya gaban mirrow ya shafa lotion !Kallonta yayi ta gefen ido yaga shi take kallon tana rera kukanta ……
Takowa yayi a hankali ya tsugunna gabanta ya riko hannayenta cikin sanyin murya ya kira sunanta "Jawahir……""Uncle Jawwad……"ita ta fad'a tana girgiza kai a hankali
"Me aka maki Jawahir…?
"Gurin Ummi zan je……"ta fad'a tana goge hawayenta
"To naji ki bari sae da safe na mayar dake kin ji ko!kinga yanzu dare yayi kada muje motar ya kife damu tunda ban iya driving da daddare ba ko……" ya fad'a cikin sigar lallashi……
Kura mashi ido tayi sannan tace"To Ummi da wa zata kwana?
Murmushi ya mata yana fad'in"Ga Unborn dinta a cikinta……"
A Hankali ta sakar mashi murmushi tana share hawayenta …
Dafa kanta yayi ya mikar da ita "Good girl!Muje na rakaki gurin Fadila……"
Gyada kai tayi ya kama hannunta har dakin fadilan sannan ya dawo !Bayan isha'i Fadilan ga janyo hannunta suka fito dinner yayin da granny ke ta kallon Anup din ganin ta yarda ta zauna harda surutu takewa Fadilan ……
Sae da suka gama dinner sannan granny ta rakasu har dak'i ta masu addu'a ta rufesu ta koma nata dak'in……Shima Jawwad nashi dak'in ya shiga ya kwanta ……Hannun Fadilan Anup ta janyo ta daura kanta a bisa sae juyi take ta kasa bacci !Fadila kam baccinta take hankali kwance ……
Tsaki ta sake ta mike tana makawa Fadilan harara sannan ta sauka daga kan gadon ta bude d'akin ta fita ……Dakin Uncle Jawwad ta nufa ta tura a hankali ta shige tana laluben gado ……Cikin sa'a ta laluba fuskar Uncle jawwad d'in ya bude ido ta sauri ya kunna lamp yana kallonta "Jawahir……"ya fad'a cike da mamaki
Tabe baki tayi ta haye saman gadon ta shige cikin bargo ……
"Menene Jawahir?ina fadilan?me ya hanaki bacci?Me kike so?……ya tambayeta yana kallonta
Kanta ta rufe ruf tana fadin"Uncle Jawwad bata da komae sae k'ashi……""Bangane bata da komae ba Jawahir ……Wace ma bata da komae?
"Fadila mana bata da komae sae k'ashi……"ta fad'a tana leko kanta daga bargon
Kallonta ya cigaba da yi don bai gane me take nufi ba ……Yatsina fuska tayi tace "Yo Uncle jawwad bisa hannun Ummi nake bacci !na kwanta hannun fadila naji babu komae sae k'ashi ni kuma nayi tasowata……"
Girgiza kai yayi a hankali yana murmushi sannan ya janyota ya daura saman hannunshi !ta kuwa saki ajiyar zuciya tare da murmushi lokaci guda ta lumshe ido tana fad'in "Uncle jawwad wane kalar mai kake shafawa……?"Ya'akai Jawahir……" ya fad'a lokacin da yake kashe lamp din
"Kamshin lemu naji hannunka nayi……"ta fada kai tsaye……
"Lemun nake shafawa……"ya bata amsa yana kallonta
Bude baki tayi zatayi magana yayi saurin daura hannunshi saman lips dinta "Sleep…… "ya fad'a a hankali tare da gyara mata kwanciyar ……Bata kuma cewa komae ba ta rufe idonta……Mintina kadan ya tabbatar da tayi bacci……sannan shima ya gyara ya kwanta sossae
,Karfe 2:00am ya mike ya daurata saman pillow yayi alwala ya fara nafila!sae kusan asuba ya mike !kallonta yayi sae uwar zufa take ya kai hannunshi ya shafi wuyanta cikin sauri ya janye hannunshi jin jikinta rau kamar wuta……
Kallonta ya tsaya yi ya tabbatar rashin umminta ne ya sake mata zazzabi!shi kam bai tab'a ganin yarinya mai kullafa irin Anup ba ……
Motsi ta fara cikin bacci take fadin"Ummina!Unborn yana tureni!ki cewa Dad Baran sake bin Fadila ba gidan granny take kaini nayi ta shan wahala……"Tausayinta ya kamashi ya janyota jikinshi ya rungume !da asuba a tare suka mike duk da tana yarinya haka ta fantsalo alwalla ba tazo ta yaye bedsheet din gadon ta lullube ta fara sallanta !Cikin Second 7 ta gama asuba har da nafila raka'a biyu sannan ta janyo wani karamin kur'ani da ta gani ta bude tana bisi bisi da baki ……
Shi kam kallonta ya tsaya yi yana da tabbacin Anup ko izif 1 bata had'e ba amma ta dauki kusan 30 tana karantawa sae da ayi kusan awa daya tana mulmula baki sannan ta mike ta isa gurinshi tace "Uncle Ina kwana……?Murmushi ya sake mata yace "Lafiya lau Jawahir"
Juya baya tayi tace "Ummina Ina kwana !Dad ina kwana !Unborn good morning……!ta fada tana harde hannuwa sannan ta bud'e murya irin ta maza tace "Morning Anup……"ta kuma mak'e murya irin ta ummi tace "Sabahul khairi Anup……"
Kallonta yake ta gefen ido ta juyo ta tsugunna kusa dashi ta bude kur'anin da ta gama karantawa tace "Uncle Jawwad dan Allah wane surane wannan na gama karantawa……?Murmushi yayi mai sauti yace "Jawahir baki san ma suran da kike karantawa ba ko?
Gyada kai tayi a hankali tana dafe bakinta da hannu……
"Suratul Ankabut ……"ya fad'a a hankali Sannan ya mike ya nufi kofa……
Bayanshi tabi suka sauka falo !Fadila ta gani sae neme neme take tana hawaye……tana ganin Anup din ta rungumeta tana tambayarta ina ta tafi ta barta ……Turo baki Anup tayi tace "Kece baki da komae Fadila sae k'ashi ni kuma na koma gun Uncle Jawwad na kwanta……" Harara ta watsa mata tare da kama hannunta suka nufi gurin granny……
Suna gama breakfast ta koma jikin Jawwad ta lafe sae zare idanu take alamun gida take so ,Duk bayan second tace "Uncle jawwad……"da ya tambayeta "Menene Jawahir……"sae ta washe baki tayi shiru ……
Granny ta gaji tace ya tashi ya mayar da ita gidansu ……_*TUSHIYAR LABARIN*_
Alh Al Mustapha kabir Babban Ma'aikacine a FAAN (Federal Airports Authority of Nigeria)Asalinshi dan kaduna ne a cikin unguwar kawo ……Mahaifinshi Malan Kabir limamin masallacin unguwarsu ne sannan dan kasuwa ne yayin da mahaifiyarshi take koyarwa a wata islamiyya dake gefen gidansu ,suna da rufin asiri dae dae gwargwado tunda basu tab'a tashi suka rasa abunda zasu ci ba ……Yana da yayye guda biyu duka mata Zahra'u da basira sae shi Auta!yayi karatunshi a zaria inda yayi masters dinshi cikin rufin asiri har ya gama.……Aiki ya kawoshi Abuja anan suka had'u da Aisha da yake ita iyayenta yan Abuja ne a cikin Maimata kuma suna da hali dae sosae Sunan mahaifiyarta Hadiza Abbanta kuma Abubakar ita kadae suka haifa sanadiyar family planing din da sukayi sae mahaifar ta lalace ……Da mahaifiyar Aisha da Mahaifiyar Jawwad (Granny)yan biyu ne Granny ce hasana sae Hadiza husaina wacce suke cewa Hajiya……Itama Granny Uncle Jawwad din kadai ta haifa saboda a tare suka dinga family planing din lokacin duniya na fad'a masu karya gani suke idan suka haihu zasu tsufa da wuri……
*Feedohm*💞
![](https://img.wattpad.com/cover/131794494-288-k314378.jpg)
YOU ARE READING
TAWA K'ADDARAR......
Roman d'amourLabari ne na wata Yarinya da ta tashi cikin gata da kulawar iyayenta lokaci guda duniyar ta juya mata yayin da ta hadu Kaddara ta rasa dukkan iyayenta Sanadiyyar gobar da ta cinyesu harda karamar kanwarta !ta dimauce ta rasa duk wani tunaninta!Ta ra...