💧💧 *TAWA K'ADDARAR....💥*
《K'azamar Rayuwa...》
💥® *HASKE WRITER'S ASSO💡*
(Home of expert & perfect writers)*NA FEEDOM*💞
*Wattpad:Feedohm11**Bestowed to Aunty Sis💕*
*If you can't say something nice to me Please don't say anything!If you can't talk to me respectively pleasa don't talk to me at all!If you need to be arrogant condescending or patronizing go elsewhere!Those are my standards If you can't Handled it go find someone else Who will tolerate Immature and rude Behaviours......I belong to no body......*
*10*Dagowa tayi tana kallonshi sauran hawayen dake makale a idonta suka zubo......
A Hankali ya juyar da kanshi ya kalli Fadila dake kokarin bude kofa......ya mata alamar da ta zagayo gefenshi ......
Cikin lallashi yace "Kin yi Laifine JAWAHIR?
A Hankali ta gyad'a mashi kai ......
"To kiyi shiru kinji!Zanwa teacher din magana kar ya dakeki......"Shiru tayi tana kallonshi sannan ta saka hannu ta bude motar ta fita!ko kallon Fadila batayi ba ta bude bayan motar ta dauki school bag dinta ta kama hanyar class dinsu...
Breakfast dinsu ya bawa fadilan ta tafi!ya dad'e zaune a mota sannan yaje ya tambayi Uncle Abba abunda ya faru......Ko da ya fad'a mashi kasa bawa Uncle hassan yayi hakuri saboda idan bai hukuntata ba bara ta gane tayi laifi ba......
Uncle Abban ne bayan Jawwad ya tafi ya samu Uncle Hasan ya bashi hakuri sannan ya hakura yace zai sassauta daga abunda yayi niyya......
Anup kam tunda ta shiga class ta hade kai da desk take kuka a hankali!Duk teacher da ya shigo bata dagowa Idan fadila tace "Anup ki tashi Note fa yake ......"
Sae tace "Zan karbi naki idan naje gida Dad zai tayani......"daga haka bara ta sake cewa komae ba
Daga karshe ma Fadila komawa tayi tana cewa teachers din bata lafiya!Ko da akayi break bata fita ba duk nacin Fadila sae dae ta kyaleta suka zubawa abincim ido su duka......
Ganin har lokacin bata bar kukan ba yasa Fadila ta fita neman Uncle Jawwad amma sae Uncle Abbah yace mata ya tafi kuma bai dawo ba......
Kusan Eleven Uncle Hassan ya shigo yana kwala mata kira ......Banza ta mashi tana girgiza kai a hankali tare da lumshe idanu......
Fadila ta tabo kafadarta tace "Anup baki jin Uncle Hassan na kiranki......"
"Na ji......" ta fada a takaice sannan ta mike tana isa gabanshi tayi kneeling......Bulala goma ya mata amma babu ko digon hawaye a ciki abunda ya bawa duk yan class din mamaki!Saboda indae zaka daki Anup to sae dukkan school din ta sani......
*2:00Pm*
Feshin ruwa akewa gida kamar bakin kwarya amma hakan bai saka wutar dake ci lafawa ba ......Motar Firefightet tafi biyar tana zuwa amma kamar k'ara kunna wutar akeyi......Ilahirin mutanen sake zagaye da gurin kallo daya zaka masu ka tabbatar da karayar zukatansu Masu videoting nayi masu salati da kuka sunayi......
"Akwae mutane ciki wallahi......" Abunda yawancin mutanen dake gurin suke fad'a kenan tare da dafe kai......
School Bus d'in da ta tsaya a gefen titi !yara yan makaranta na fitowa ita ta kuma jan hankalin mutanen dake gurin ......
A Hankali ta diro daga motar rataye da katuwar school bag dinta !yayin da ta juya baya tana d'agawa Fadila dake cikin motar hannu tare da fadin " Gobe zan taho maki da book in fa"
Dariya Fadilan ta saki a hankali tana fad'in "Sannu Mr Carrolux ba wani note d'in zakiyi...... "
Tabe baki tare da dukawa tana gyara sandals d'inta sannan tace " Daddy zai tayani note in "
Bata ba jira amsarta ba ta juya tana kallon dandazon mutanen dake tsaye suna kallonta !Cak ta tsaya tare da k'urawa gidan Ido kamar an tsikareta ta taho da sauri tana dube duben mutanen dake gurin tare da kiran " Ummina......"
Sam babu hawaye a fuskarta take tambayar wani dattijo "Ina Ummina!Ina dad da lil sis?Wa ya saka mana wuta a gida?
Lokacin Firefighters din suka samu nasarar kashe wutar tare da fiddo da gawar mutanen cikin gidan......
Cak ta tsayar da Idonta bisa hannu Ummi dake lilo kafin ta kife cikin kwatar dake kusa da ita......
Lokacin Su Uncle Jawwad suka iso a rude dasu Hajiya da granny......Kan Anup yayi ya daukota cikin kwatar yana kiranta da karfi tare da girgiza......
Hajiya ma Sumewa tayi a gurin !Kanta mutanen sukayo aka daukesu A ka sakata mota aka nufi Hospital dasu......
Sae a aka karbesu emergency sannan Uncle Jawwad ya koma asibitin da aka kai gawar Su Ummi!Duk wani mai imani bara ya so ya kara daura idonshi ba a gawar bayin Allah!Babu wanda zai jikin bil adam ne ya koma haka lil kuwa tokarta aka tattara cikin farin gyalle!Kusan awa biyu gawar tayi a asibitin wanda Sannan aka basu ita suka dawo da ita gidansu Ummi a lokacin duk wani family na mutanen babu wanda bai zo gurin ba......
Sallah aka masu tare da addo'o'i sannan aka tafi dasu gidansu na gaskia......【】
A Hankali ta bude idanunta dake tsaye ta daurasu saman Granny dake zaune kusa da su tana kuka......
Maida idanun tayi ta rufe tana fad'in "Na dawo school sae na iske a gidanmu a kone!da gaskene granny?
Hannunta ta kamo ta rike tana kokarin mayar da kukan da ke niyar kwace mata......Bude ido tayi tana kallon Granny tare da saka dayan hannunta ta rike na granny tana fad'in " Da wutar ta kama sae Ummi ta dauko lil sis da daddy suka fita?ko da gaskene Ummita na gani ta kone granny?Hawayen dake cike da idanunta suka fito......Juyar da kai tayi ta cigaba da fad'in " Dan Allah ki kira man Ummi da lil sis dita!Ki ce ma hajiya ta tashi mu tafi na gano Ummi ta......"
A Hankali Granny ta saki kuka tare da rungume Anup din!Tureta tayi tana fadin "Ki sakeni!ki kiraman Uncle Jawwad ......"
Sakinta tayi ta fita daga da gudu daga dakin tana toshe bakinta......
Tana fita Anup ta diro da kafafunta daga saman gadon ta juyo tare da kallon Hajiya sannan ta fita daga dakin itama!ba tare da hajiya ta lura da ita ba ta zagaye ta bayanta ta fita daga asibitin......
YOU ARE READING
TAWA K'ADDARAR......
RomanceLabari ne na wata Yarinya da ta tashi cikin gata da kulawar iyayenta lokaci guda duniyar ta juya mata yayin da ta hadu Kaddara ta rasa dukkan iyayenta Sanadiyyar gobar da ta cinyesu harda karamar kanwarta !ta dimauce ta rasa duk wani tunaninta!Ta ra...