TAWA K'ADDAR 23

4.1K 220 91
                                        

💧💧 *TAWA K'ADDARAR…*💥
            《K'azamar Rayuwa》

                         💥

® *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writers_

          *NA FEEDOHM💞*
       *Wattpad:Feedohm11*

     *Bestowed to Aunty Sis*💕

                   *23*

    *Fateema Usaini Mai doki, Fateema Moriki ,Ummi Finger Matar Deebo, Da yan Feedohm Novella wannan page din na kune💥*
 
                    

      Cike da tashin hankali Abba ke kallonshi da kyar ya bud'e baki yace "Kana nufin tayi loosing duk wani tunaninta?garin ya hakan ta faru…?Dan Allah kuyi wani abu mana wallahi ko nawa ne zamu bayar ku taimakemu wallahi zuciyar mutun biyu ce a tare da ita!

A Hankali yace "Try and calm down Sir, Ba'a sayen lafiya bare ku sayar mata, Wallahi da muna da abunda zamu iya mata da tuni an mata hakan bai faru ba!kanta ya bugu sosae ta yarda jijiyar dake kai sako a brain dinta ta samu matsala, addu'a ce kawae zaku mata in sha Allahu zata samu sauki, Sannan zamu daurata saman magunguna indae an kiyaye zata warke da yardar Allah "

"Dan Allah……!

Katseshi yayi yana fad'in "Iya abunda zamu iya mata kenan har ga Allah , Sannan abu mafi amfani dole ta zauna da mutanen da ta saba dasu kafin wannan abun ya faru hakan zai iya taimaka mata wajen dawowar  tunaninta, Allah ya basu Lafiya…"

  A sanyaye ya mike ya fita hakan yasa Deebo barin gurin ya koma jikin motarshi ya jingina yana murmushi,

  Ya dade tsaye bakin kofar doctor din yana tallabe da kanshi duk wata dauriya tashi ta barshi na dan lokaci yayin da zuciyarshi ta kare ya rasa me ya dace yayi ,sam baya iya jin zai fad'a masu ta samu matsalar mantau, lumshe ido yayi yana hango tashin hankalin da zai gani a kwayar idon Jawwad!Ganin baya da madafa ya sashi  komawa inda suke, Kamar kam jiranshi suke suka  tareshi suna tambayarshi "Me ke faruwa?

   Jawwad ya kalla dake tallabe da kumatu sannan ya sauke ajiyar zuciya yace "Ba wata matsala bace sosae zata warke in sha Allahu…!

Da sauri Jawwad ya mike ya zo inda suke tare da kamo hannun Abba yace "Amma har yanzu bata farka ba Abba…"

A Sanyaye yace "Zata farka Jawwad…"

"Ka tabbata Abba?bana so wani abu ya sameta…!ya fad'a idonshi cike da hawaye

Runtse ido yayi yace "Na tabbata Jawwad da yardar Allah zata farka, ina ji a jikina babu abunda zai sameta…"

Lumshe ido yayi ya sulale k'asa yayin da ya tallabe kanshi da hannu biyu, Sam baya iya jure komae akan Jawahir wani irin so yake mata mara misaltuwa…Lumshe ido yayi ya daura kanshi bisa cinyar hajiya dake zaune yayin da daura hannunta tana kwantar mashi da sumar kanshi……

  Babu wanda ya motsa a cikinsu yayin da sukayi zugum zugum suna jiran farkawar daya daga cikinau har sae da dare ya take sannan Abba ya fita ya samu Napep ta kaishi bank ya fitar da kudi sannan ya je ya sama masu hotel din da zasu kwana ya dawo yace su tashi su tafi, Da kyar su hajiya da fadila da granny suka tafi har sun tari Napep Deebo ya dawo daga shashancin shi yace su shiga ya kaisu, Duk a tunanin su Deebo abokin Jawwad ne don haka babu wanda yayi magana suka shige ya kaisu …

  Jawwad kam ko kalma d'aya bai furta ma Abba ba illah girgiza mashi kai da yayi alamun bara ya je ba…Ganin ba zuwa zaiyi ba yasa Abba zama a gurin kusa dashi yayin da ya daura kanshi saman kafadar Abban idonshi a lumshe , anan suka kwana zaune ido biyu wanda hakan da sukayi ba k'aramin b'atawa Deebo rai sukayi ba saboda a yarda ya tsara suna tafiya zai dawo ya dauketa illa iyaka idan sun je Ilorin sae ayi treating nata a asibitin Bro Abu ……sam yawan security d'in dake cikin asibitin bai dameshi ba yasan yarda zaiyi dasu don har hijabin da zai saka mata duguwa yarda bara a ganeta ba sae da ya sawo a fitar da yayi…

TAWA K'ADDARAR......Where stories live. Discover now