KASAITATTUN MATA
(Labarin Mata Ukku)Tasan tana da bukatu a aljihunshi shiyasa tayi saurin maida mashi da amsa.
*_Bani minti kadan Ina zuwa Alhajina, inasan in shirya maka kumai yanda ya kamata ne._*
Ta tura mashi sannan ta kara maida hankalinta akan abinda Saleem ya kawo mata, photon farko na wani Dattijon farin mutum ne wanda shikarunshi zasu iya kaiwa 45 zuwa Hamsin, yana da kyau da kwarjine kaken sojane jikinshi dakakken mutum ne mai kwarjine da haiba.
Photo na biyun kuma kyakykyawan matashin saurayin da zai iya kaiwa shikara talatin da biyar zuwa arba'in, cikin dakakkiyar shadda mai ruwan toka an mashi aikin surfani mai kudi da tsada ga hularshi kamar ruwan toka amman bata cizaba kamar shaddar jikinshi.
Kai ta gyada sannan ta maida hankali akan Saleem tace "Meye bayanin kumai nasu?"
Mika mata takaddun hannunshi yayi yace"Kumai akwaishi cikin wannan takardun idan kika duba"
Amsa tayi sannan tace"Zamu dibasu idan na dawo amman kafin nan bare in kirasu su fara dibawa ina da abinyi"
Waya ta dauka, tayi yan danne dannenta, sai tace"Sako zai shigo maka, sai ka fara amfani dasu kafin in bukace ka"
Kafin ta gama maganar wayar Saleem tayi kara alamar sako ya shigo mashi, dubawa yayi yaga ta tura mashi da kudi, murmushi yayi yace"Beauty aikin ki na kyau, shiyasa nake matukar san aiki dake"
"Kana iya tafiya tunda ka isar da bukatuna"
Tashi yayi a saman kafafuwanshi sannan ya tura hannuwa cikin aljihun wandanshi jeans yace"Akwai wata harkalla amman sai mun zauna, bansani ba ku tunaninki ya taba kaiwa nan, akwai samu feye da wannan sana'ar taku"
Ku kallanshi batayi ba ta daga waya tana kira tace"Ina kasa, zan fitane kuna iya bayyana a falo Saleem yazo da kumai"
"Ok sai mun zauna din Saleem"
Tafiya yayi da zummar zuwa club yau yasha giya san ranshi ya dauke duk kalar macen da tai mashi tunda ma'ajiyar kudinshi da nauyi babu laifi, minti ukku tsakani suka bayyana cikin falon kuwacce ta samu waje ta zauna, foton Dattijan mutumin Aisha ta mika ma Laila dayan kuma na matashin saurayin ta mika ma Nuwaira, amsa sukayi suka fara dubawa, sannan ta kara masu da takaddun dake hannunta"Akwai bayanin kumai, anace ya shigo gari zanje in damfari garan in dawo"
Laila tace"Yaushe ya dawo inace sai jibi kukayi dashi zai shigo"
Nuwaira tace"Ai baya iyawa kinsan akwai amenci tsakaninsu da bunsuru"
Aisha tace"kuwaccen ku tanaci da amfanuwa daga abinda yake mallakinshi, saboda haka bashi suna a wajanku bawai gwaninta bane"
Daga haka ta tashi ta haura sama, a kukarinta na shiryama Alhaji Rufa'i kanta, musamman tunda tana da bukatu a wajan shi.
Sosai suka dukufa wajan fahimtar abubuwan da suka kunshi wadannan mutanan na jikin photo, sun fahimci kumai kuma sun gane kumai.
Cikin shirinta ta fito jallabiyace ta Sanya sannan ta yane kanta da dankwalen jallabiyar sannan tayi kwalliya mai sauke, amman tayi masifar yin kyau musamman da yake ita din mai kyance, oud wood,White oud, Alharamaine madina kawai suke tashi jikinta, saukuwa tayi ta samesu saman suna tattauna yanda suka fahimci kumai cikin sauke.
Laila tace"Wannan mission din baida wata wahala gaskiya"
Aisha tace"Bana tsamanin baida wahala hidimar fa haddasu masu kake anya kuwa ace babu wahala,Kuma dai menene idan na dawo sai mu kara zama"
Nuwaira tace"Shikinan sai kin dawo, a yayu mana da yawa maikyau"
Baki ta taba tace"ke bana ma baki tausaye yanda zan amshe kuwace wahala daga hannun wannan mutumin, kinsan dai hidimarshi babu sauke kwana ake abu daya, ina mamakin yanda zuwa yanzo da tsofa ya kamashi bai rage kumai ba daga jarumtarshi"
Nuwaira tace"Hajiya ke tafi kawai kada ki bata mashi rai, inda wuya ai akwai yayan banki"
Tafiya take tana rangaji, duk wanda ya ganta yasan babu maganar rashin aji da ji da kai, yanayin tafiyarta ma ya isa ya wadatar da mai kukarin cusa kanshi wajanta, rijiya ba wajan wasan makahu bane.
Laila tace" Beauty baki dauka key ba"
"A dai daita zan shiga banshirya ma amsar wasu sakarkarin ba yau, amman idan na shiga a dai daita babu wanda ma yasan da zamana"
"Hakane kuma, a dawo lafiya"
"Allah yasa"
Bana ganin comment dinku da voting, kamar littqfin bai maku ba kinan.
Inasanko domin Allah.