28

2.7K 180 11
                                    

KASAITATTUN MATA
(Labarin Mata Ukku)

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION.

Mallakar.
BILKISU BILYAMINU




      Nannauyar Ajiyar zuciya Mejo yayi sannan ya dafa kafaɗar Abakar sannan yace"Dan Allah ko zaka iya tuna wata yarinya dake nan wajan wata matashiya haka?"

   "Ban gane abinda kake nufi ba, matashiya kamar ya?  kuma mai ya haɗaka da ita?"

    "Kai dai nasan ba ɗan harka bane tunda,  amman bansan ko ka canza hali ba?"

   "Ban canza ba daga yanda ka sanni da kyamar mu'amala irin taku, Allah ya kare ni sosai da izininsa"

    "To wa kake nema a waje irin wannan?"

    Da sauri Habib ya isa kusa da Abakar yace"ƙanwar wani abokin mu ce kasan yanzu duniyar ta lalace yara babu yanda za'a tanƙwara su, sai sun maida rayuwarsu wata iri, to shine muka ce zamu duba mashi tunda yace ance tana bauchi ɗin nan, so amman sanda suka yi maganar bana nan sai Mejo ne suka yi da shi so Mejo sai ka faɗa mashi yanda kamaninta suke wata ƙila ya gane"

    Kyakyawan murmushi Mejo ya sauke a saman fuskar Habib dan badan shi ba da bai san yanda za'ayi da tambayoyin da Abakar yake ajewa a saitinshi ba, wassafa ma Abakar kamaninta ya dingayi a sannan ya ɗora da cewa"Allah yasa ka taɓa ganinta"

    "Yanda ka misalta kamaninta ai bansan yazan ce na taba ganinta ba"

    Kai Mejo ya dafe yana tunanin ya zai misalta mashi ita, duk yanda ake ciki yana san ya tabbatar mashi da ya ganta, sannan ya fara nemanta a nan hotel din. Habib ne ya koma cikin motarshi ya ɗauko littafi da biro sannan yazo ya ɗura saman inda suke zaune ya tura gaban Mejo, kallanshi Mejo yayi, Habib ya ɗaga mashi kai.

    A hankali ya ɗauko biron idanuwanshi ya lumshe sannan ya  aza biron saman takaddar, kumai na suffanta ya yanzu a gare shi a hankali yake Jan biran yana wassafa kamaninta da yanda take a yanayin da tazo mashi, minti biyar ya ɗauke shi sannan ya bude idanuwanshi sosai zanan yayi kyau duk da da biro yayi wata kila hakan nada nasaba da Allah zai taimake shi ya ganta ne,  ɗaukar takardar Habib yayi yace"Yanda aka wasafta maka surarta kenan, right?"

    Kai Mejo ya ɗaga mashi, shi kuma Habib ya mika ma Abakar yace"Take a look"

   Amsa Abakar yayi ya natsu yana kallan photan sosai macen dake jikin photan ta tafi da dukkan imaninshi a wani dare da ya ganta zaune a babban falon Hotel din ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kurbar lemo, tsananin kwarjininta ya hanashi karasawa inda take, ga alama ba irin matan barikin da ya saba gani ce ba dan wannan fuskarta a murtuke take, lokacin daya wurga mata murmushi haɗe rai tayi sannan ta ɗauke kai, ba tare da tayi na'am da buƙatar shi ba, karshe ma ta ankarar da shi ya kiyaye ta da wani mugun kallo da ta aje a saitin idanuwanshi.

     Baki ya taɓa sannan yace"Na ganta kusan sau biyu, kuma naga kamar daga sama take saukowa amman gaskiya bansan ɗakin da take ba"

    "Yanzu ya kake ganin zamu fara nemanta?"inji Habib.

    "Ko wannan zanan zai iya bada gudun muwa wajan bincikota muje wajan ma'aikatan kila su gane ta"

    Gaba ɗaya suka tashi suka isa inda reception yake wannan matar dai suka ƙara iskewa, Abakar ya miƙa mata zanan fuskarta yace"Nasan kinsan wannan, tayi rayuwa a nan Hotel din, to ɗakin da take muke san sani"

    Ta dauke yan mintuna tana kallon takardar dage gabanta sannan tace"Na santa amman mai yasa zan faɗa maku ɗakin da take?"

    Mejo ya wurga mata  kyawawan idanuwanshi da suka rine da bacin rai, yace" Kada ki ɓata mana lokaci zaki faɗa ku bazaki faɗa ba?"

KASAITAATTUN MATAWhere stories live. Discover now