KASAITATTUN MATA
(Labarin Mata Ukku)Mallakar.
BILKISU BILYAMINUSunyi sayayya mai yawa ta kayan kicin da kuma kayan bukatu na Wanda zaiyi zaman wucen gadi, bakin kofar shiga kasuwar sukayi parking bayan tayi waya da saleem yace mata ta jira zai kaita gidan da aka samu idan yayi mata"Idan yayi mata banda matsala, tunda kasan bawai zaman dun sun zanyi ba, just a moment ne kawai, ina jiranka dai a wajan kawai"
Hannunshi yabdan dura saman nata yace"ina zaki kuma?"
"Zan canza wajan zama ne, zaman hotel is not deserved to me, so zan kuma gida ne, naga zaife save"
"Good idea saboda kinsan yanzo babu tsaro sosai"
"Kusan hakan"
Dan shafa kai yayi sannan ya kalle cikin idanta bayan ya shafe fuskarta yace"Amman dai yau za'a debe mani kewa ko"
"Ban gani abinda kake nufi ba"
"Nasan kinsan abinda nake nufi baby please tun sanda na fara ganinki nake kadayinki dabkaunarki, please ina so"
"Bansan me kake so ba fa"
Murmushi yayi sannan ya buge sityarin motar sannan yace"I mean ina sonki da sha'awarki a hade lokaci guda, kin gane ai"
"Ayi making deal, nawa zaka biya?"
Murmushi yayi yace"nawa zan bada kiyi mani tsadar bala'i zan biya"
"Baka da kudin da zan iya mallaka maka kaina, tsada gari ne, bana tsamani kana da kudin biyan kaina"
"Hmmm hajiya kinsan waye ne kuwa, sannan kinsan iya adadin abinda na mallaka da kai tsaye zaki yanke hukuncin bana iya biyanki, baby tsadarki nawa ne just say it kawai"
"Miliyan goma" ta fada sannan ta kauda kai taci magani, dariya ya fasa sannan ya kamu hannunta yace"yan mata baki da tsada zaki ce"
"Million goma ai ba kudi bane to me dai, zan bada ninkin haka"
"Fine, zaka samu feye da yanda kake so, but for known dai sai zuwa na samu sukuni na gama parking kumai a saban gidan da zan kuma"
"Maganar gaskiya bazan iya hakurin yau bama, bqllantana gobe Ku zuwa sanda zaki samu sukuni ba"
"Inaga hakan za'ayi dan ban shirya amsar kuwa na a irin sannan lokacin"
"Biya zanyi ba kyauta za'a bani ba, duk da dai abin akwai arha"
"Murmushi tayi sannan tace"na yadda kuma me zaka fada"
Shima dariya yayi yace"Mubar maganar wasa, baby ya za'ayi yau a sama nake ina bukatarki a cikin rikona kiban damar hakan please"
Wayarta ce ta fara kuka, dagawa tayi sannan tace"Daga bakin kofa zakaga ash din Mercedes"
Wata yar kwana ya shigo sannan ya hangeta motar da take mashi kwatanci da ita, nuna ma Mujaheed, Saleem tayi tace ya bishi duk inda ya nufa, motar ya tada yana bin duk inda Saleem yabi.
Sun isa gidan babu laifi zai kayatar da mai bukatar abu mai kyau idan akayi duba da gidan kanshi karami ne. Amman kuma yana da kyau da kyan fasali sosai ya burge Aisha a dai zamanta ita daya.
"Babu laifi yayi kyau Saleem"
"Yayi maki wannan kinan?"
"It look nice"
"Haka ake so ai"
Bort din motarsu ta bude ta dinga fiddo kayan da suka siya a kasuwa ita da Mujaheed, Saleem da wani matashi wanda bata san ku waye ba suka dinga shiga da kayan cikin gidan, jikin Motar Mujaheed ya jingina yana danna wayarshi daga bisani kuma ya kanga saman kunne, sannan ya dan matsa gefe yana wayarshi wanda shi kadai yasan mai yake tattaunawa, bayan su Saleem sun gama Shiga da kayan sai ya tsaya kusa da Aisha yace"By all means inasan barin garin nan, ina nufin gobe insha Allahu"
Dan juyawa tayi sannan ta rike kugu tace"I don't no what rosh you to kd fa Saleem"
"Bazaki gane bane, but am in need of sometine"
"Like what, kudi na sayanshi, idan yana saye nawa?"
"Kin gama sayan abubuwan da zaki saya?"
"Something like yes, but am not sure"
"Think, daga nan zuwa gobe karfe sha biyu zan bar garin ga"
"Really?"
"Yah, I mean it, ina da gaggarumin abun yi wallahi, abubuwanki suka tsaidani nasan abubuwa sun kusa zama normal sai ki idasa da kanki"
"OK, babu damuwa Mr Saleem"
"Yah, Hajiya maikyau"
"Inasan kwasu kayana daga Hotel din nan, ya za'ayi?"
"Lest go together mana" Mujaheed yace Wanda zuwanshi kinan daga Indi ya tsaya yana wayarshi ta sirri.
Gidan Saleem ya kulle ya mika mata makullen yace"Sai naji kiranki"
"Kasan zan nemeka ai"
"Nasan haka"
Murmushi ta sakarma Saleem, shima ya maida mata dukkansu sun san ma'anar murmushin, amman a kasan zuciyar Mujaheed yana mamakin yanda wannan saurayin nata ya zama bawanta, tana ta sashi aiki, shi kam baya iya wa idan bai sata ba, bata isa ta sashi ba baki ya taba yace" Muje ko?"
"Yah"
Waven Saleem ya mata itama ta maida mashi sannan ta Shiga cikin Motar Mujaheed suka nufi hanyar Hotel din da zata dauku kayanta.
"Amman ya zaki dani da nake da butaku a kanki yau, sosai nake san kasancewa tare dake Baby"
"Na fada maka kayi hakuri bazan iya amsar kumai ba a yau"
"Ki agaza mani Dan Allah nifa ba gwanin kwashe kwashe bani, tunda na bakunci wannan garin banga wata wadda ta kwanta mani ba sai ke saboda haka nifa duk wayanki yau sai kin debe mani kewa"
"Hmmm babu dole fa malam"
"Na fiki sanin haka, malama" a tare suka saki dariya mai kayatarwa.
Sun isa hotel din ta kwasu abubuwan da tasan mallakinta ne sannan tazo tayi handing over na makullin ga mamallaka wajan, bayan tasa hannu suma sun san ya, Mujaheed ya amshi jikkar dake hannunta yaje ya sanya a Mota, sannan ya dawo ya tayata rike wasu abubuwa trowely dinta ya amsa yana ja ita kuma tana sargafe da jikkar laptop a kafadarta, daya hannun kuma tana rike da wata jikka madai dai ciya, kumai sun saka shi a mota sannan ya bude ya shiga ita ma ta bude ta shiga, motar tint glass ne gaba daya ya daga su, sannan ya saki ac, key yayi ma motar sannan suka tafi a wajan gate din da zai fiddaka Hotel din suka tsaya domin bada card din da ake badawa idan zaka shiga, haka idan zaka fita zaka basu abinsu, dai dai zai tsaya ya bada sai kuma ya lura da wata mota wadda batayi parking dai dai ba, idan zai fita zai iya buga mata.
"Please a minute Baby, bari in ma mai motan nan magana ya gyra parking dinshi"
"OK, a dawo lafiya"
Fita yayi ya isa Inda motar su Mejo take ya dan kwankwasa ta saitin Inda Mejo yake yace"Kudan gyara parking dinku kamar kun dan tare hanya"
Tsananin kwarjinin da ya hanga a tsakanin idanuwan Mejo Almustapha shiya zaburar dashi da sanin babban mutum ne mai kamala sannan ga wani hasken annuri dake kwance a saman fuskarshi, fuskarshi babu yabo babu fallasa yace"OK, sorry bamu san mun kashe hanya bane, Abokin gyara please"
Tsintar kanshi yayi da cewa"Babu kumai ranka ya dadi"
Kumawa yayi inda motarshi take parke yana tsananin mamakin ire iren wadan nan mutanan masu mugun kwarjinin tsiya.