FELLING

2.3K 159 18
                                    

Wayarshi ya daga ya kanga saman kunnanshi yace"Nasan kin san ki kadai nake jira ko? Bansan mi yasa kike wasa da zuciyata ba, come on baby ina jiranki yanzo"

Dariya yayi ya kashe wayar yana jin mugun santa na zuba a kasan zuciyarshi duk wani bayan sakan guda, yayi imani santa shine kumai mashi yana farin ciki da samun natsuwa Idan tana kewayanshi, ya tabbatar itace kumai na duniyarshi yana samun gamsuwa Idan yana tare da ita sosai yake san ganinta kusa dashi dan samun kwanciyar hankalinshi, ALLAH ne shidarshi da mugun san da yake mata, hasashe bai isa ya hasasu santa da yake ba.

Da sallama ta shiga office din, zaune yake yana jiran zuwanta ya kusa matuka ya ganta a kewayanshi, idanuwanshi tar duka ya aje dai dai lokacin da yake amsa sallamarta"Wannan ajiyar zucuyar kumata meye? "

"Tunda kinsan dalili babu amfanin tambayar, nasan kinsan kice, so mu barta a haka"

Kallanta ta aje a saitinshi sannan ta kara aje mashi murmushi a cikin idanuwanshi"Bansan yaushe zaka yadda da san da nake maka yafi Wanda kake ikirarin kana min ba"

"Hajiya mu bar wannan maganar zauna muyi magana kawai"

"To na zauna ranka ya dade, mijin Adda Maryam Baban Islam"

"Kin samu damuwa da yawa, Aisha, bani hankalinki nan ban san ya zan maki bayanin halin da nike ciki ba, amman kusa nake san mallakarki bawai nisa ba, nasan kin dade da sanin haka, saboda haka Idan an tashi niman auranki ina za'aje?"

Idanuwanta ne suka canza bata kawo wannan maganar kusa ba, baku ma tasan ta ya zata fara fada mashi cewa zaman kanta take bawai iyaye ni take zaune da su ba, asali ma tun tana shekara sha biyar ta bar garin da asalin inda aka haife ta, bama tasan ta ina zata fara zuwa garin nata ba, kai ta kauda sannan tace"Wa ya fada maka cewa aure zanyi yanzo, ina da sauran wani issues tukunna kafin in saka ranar da zanyi auran"

Kallan kasan ido yayi mata sannan yace"Na dauka kina da hankali ashe babu, bana tsammanin cewa baki da hankali da zaki iya gane menene zaiyi dai dai da rayuwarki ba, watau kinan kina san ki fada mani cewa shi auran sai an zaba mashi lokaci kinan"

"Yanzo mubar wannan maganar muyi wata zamuyi wannan Idan bukatar hakan ta tasu"

Sosai yasha mamakin yanda take gujema maganar aure mace kamarta tana gudun aure haka, to meye matsalar kudai tana da irin wadan nan aljanun da ake fada suna hana mata aure, fuska ya daure sannan yace"Wai meye haka Aisha wallahi da gaske nake maki sosai nake san mallakarki a sashena so please a bani hadin kai hajiyata"

"To shikinan babu damuwa zan fada maka bani dan lokaci, kadan ba da yawa ba, kasan ita maganar aure tana bukatar lokaci, so please ka dan bani lokacin kamar yanda na bukatar, Kaji hayateee"

"To kamar zuwa yaushe zan saurare ki, dan kinsan a matse nake da ganin mace kamarki a cikin ikona da kulawata, so ki fada mani zuwa wani lokaci zan kara tuntubarki, da zafi zafi ake bugun karfe"

"Kullum muna haduwa lokacin ba zai zama mai wuya ba, kada ka tada mana hankali"

Dariya ya saka sannan yace"Babu damuwa zan jiraka zuwa lokaci"

Aiki suka cigaba cikin farin ciki da soyayyar juna, bayan Abdulwaheed ya jaddada mata bawai lokaci mai tsawo zai dauka yana jiranta ba, Dan sosai yake jin baya samun natsuwa musamman da bata kasanci cikin ikonshi ba, kuma ba zai lamunce Ana kale mashi macen da yake jin ta kusa zama mallakinshi sh, shi daya kawai ba tare da wani ya kalle ta ba ku yayi tunin mallakarta ku furta mata wata kala sabanin gaisuwa kawai.

Ita kuma daga gefenta tana jin matsanancin tsoro dan tasan Abdulwaheed da kafiya da nace ma abinda yake so, tasan zaa kai ruwa rana dashin akan ya daga mata kafa ta shirya ma yanda zata tsarashi, kada ya gane ita mace ce wada take cin gashin kanta, bata shirya amsar wulakancin kuwanne da namiji ba, sosai zata gujema duk wata kwala da zai bullu da ita, dan bayyana mata soyayyarshi da kuma kwadayin auranta, zuwa yanzo tayi imani da san da yake mata, kuma ya yadda zai iya yin kumai dan mallakarta a matsayin mata, murmushi tayi data tuna mai ta fito yi ga kuma inda ta buge a kan wanda zatai aiki a kanshi.

KASAITAATTUN MATAWhere stories live. Discover now