ƘASAITATTUN MATA
(Labarin Mata Ukku)NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
_Mallakar_
*BILKISU BILYAMINU*People think that they are ignoring me, But Actually they are losing me.
29
Ɗan jingina yayi jikin motar yana tunanin yanda zasu fara nemanta a wannan hotel din, idanuwanshi ya aje a saitin Abokinshi Habib yace"Ta ina zamu fara?"
"Bansan mai kake san faɗa ba, bansan ta ina za'a fara ba tunda bansan yanda al'amuran suke ba"
Kai ya kaɗa sannan ya buɗe marfin motar ya fito sannan yayi mashi alama da hannu ya fito shima su Shiga ciki. Sosai ya kasa gane yanda abubuwan suke tafiya ma abokinshi idan bai manta ba bai taɓa riskarshi a irin wannan yanayin ba, sosai ya tausaya mashi duk da baisan mafarin abun ba, Amman kuma meye ya tabbatar gaggarumene a duniyar abokin nashi, zai mashi uzuri har zuwa lokacin da zai samu natsuwa dan baiga alamar na tsuwa ba a yanzo tattare da shi, sun shiga cikin Hotel din Amman kana ganinsu kasan bawai sun saba zuwa wajan bane dan sai da suka tambaye inda reception yake, dan ba wajan zuwansu bane ba zasu iya gane inda yake ba, sun isa wajan suka iske wata matashiyar budurwa zaune tana yan rubuce rubuce, kallan Habib Mejo yayi alamar yayi mata bayani, kai ya girgiza mashi alamar bai san mai zai ce ba tunda baisan maganar ba, a ɗimauce Mejo ya ɗan mata magana.
"Sannu ko?"
Kanta ta dago idanuwanta suka shiga cikin na Mejo, bata taɓa ganin dakakken namiji irin wannan dake tsaye a gabanta ba, sannan kuma da masifar ƙwarjini kwance a tsakiyar idanuwanshi.