ƊAUKAR FANSA

2.1K 215 44
                                    






zanyi farin ciki idan kuka fahimci ina buƙatar ganin voting dinku da comment, rashin ganin hakan sai in ɗauka kamar baku da bukatar duk wani labari da nake zama inyi dan jin daɗinku da nishaɗantuwarku, nasan tsakanina daku soyayyace mai girma gaske.

Ina aanku har cikin zuciyata.





Idanuwanshi ya saka cikin nata, sosai ya ɗauki mintika yana kallan ƙwayar idanta. Bai taɓa tabbatar ma zuciyarshi namiji na rasa abin cewa idan yana gaban mace ba sai yau, da yake gurfane gaban macen da yake kasa tabbatar ma kanshi cewa ta gama samunshi, gaba ɗaya ta kama kai da ƙafa hadda ma gangar jiki, zuciya da ruhi, a wani lokacin ma yana hasashen bai taɓa jin san wata mace a ƙasan zuciyarshi ba idan aka ɗauke ta ita, ita ɗaya. Ya rasa ya zaiyi da rayuwarshi ya rasa ya zai tanƙwasa zuciyarshi ta dinga taɓuka wani abun azo a gani idan yana gaban wannan halittar da take tafiya da dukkan wani kaifin tunaninshi da basirarashi da Allah yayi mashi baiwarsu, idan yana gabanta yana  zartas da umarni da ita da kanta ta zartas dashi, bayan bai taɓa ji ku ganin haka  zata faru da shi ba, da zai samu wanda zai faɗa mashi haka ma, bazai yadda da dukkan wani furuci nashi ba, sai dai lokuta da yawa yana danganta haka da shi kalar tashi ƙaddarar kinan shafinshi daya tashi buɗewa da haka ya bude mashi. MACE itace ƙaddarashi ya kuma amsa da dukkan hannuwanshi guda biyu,  sai dai kuma wata zuciya can ƙasan ruhinshi tana yunƙurawa da ya tasarma kanshi da addu'a da neman mafita,  dan ire-iren waɗan nan matan haɗarinsu yafi alkhairinsu yawa.

      Idanuwanshi ya sauke daga nata, ya kauda kai yana jin ƙasan zuciyarshi na mashi wani irin matsewar da bai taɓa tseintar kanshi a irin wannan yanayin ba, hannunta ya damƙe ya ƙara matsawa a hankali yake san buɗe bakinshi yayi magana amman ga almma yasan da wuya abinda yake san furtawar ya samu karɓuwa duba da duk sanda zai kasance tare da ita sai ta jad-dada mashi bata da buri a duniyarta bayan ganin ta tuɓe Sanatan daya fi ƙauna feye da sauran Sanatocinshi daga kan kujerarshi, tana sakin jikinta ta jiyar dashi ingantaccen daɗin da yake jin zai iya sauka daga kujerar gwamnan da yake indai zai dauwama da ita har gaban abada ne, sosai yake amfanuwa da abinda Allah ya ajeye a jikinta dan nishaɗin maza, ya yarda kuma ya amince itace jin daɗinshi, har yana tabbatar ma kanshi ita kaɗai yake jin nishaɗantuwa da ita a farkon haɗuwarshi da ita, feye da mata biyun da ya adana a cikin gidanshi da sunan ikonshi kayanshi, mallakinshi kayan jin daɗinshi, haduwarshi da ita sai kumai ya canza har yake jin babu wani gishiri ku suga dake jikinsu, sosai yake fahimtar an kusa kama kafar ma da zai daina amfanuwa da kumai nasu, dan duk lokacin da zai ƙwamushe su ji yake kamar yana ɓata lokacinshi ne.

    "Ban san me yayi ba har haka da kike ƙuƙarin lalata rayuwarshi, kiyi hakuri da dukkan abinda yayi maki,  ki yafe mashi, na maki alƙawarin kasancewa tare dake har karshan rayuwarki, zan baki kuɗin da har ki gama rayuwarki zasu yi maki amfani, amman kiyi hakuri kibar maganar nan"

    Idanuwa ta ƙanƙance sannan ta janye hannunta dake cikin nashi, sosai tayi azamar janyu mayaudarin kukan da bata ma san yanda akai yayi gaggawar zuwa ba da sauri haka, ta fara kuka cikin yanayin kissa da kisisina"Nayi maka duk wani ninkin farin cikin da mace zata ma namiji dan na kayi mani abinda nake so, kuma kamin alkawarin hakan, sai yanzo zaka ce inyi hakuri kasan ai baka min adalci ba, tun da kaga nayi ruƙon wannan alfarmar kasan ba ƙaramin tabo ya aje a rayuwata ba, amman babu kumai nagode da dukkan abinda kai mani, sai dai shugaba an sanshi da cika alkawari, amman mai yasa kai ka kasa?"

     kai ya dafe yana jin kukan har ƙasan zuciyarshi, baisan ya akai tayi gaggawar shigo da rigima cikin lamarin ba, kukanta yana taɓa kumai na duniyarshi"Ok ya isa na fahimta, yi shiru bana san wannan hawayan, zu kusa dani"

    Kai ta ɗauke, tana ƙara farashin kukanta, tashi yayi tsam ya kuma jikinta sosai ya shige jikinta yana lallashinta ta hanyar kwantar da ita a saman faffaɗan ƙirjinshi bayanta yake bubbugawa yana lallashinta, a hankali ta fara sakin ajiyar zuciyar da a natse idan ka fahimta ƙirƙirarta akai, Sai dai mai girma gwamna bai fahimci haka ba dan sosai ya kaɗu da duk wata kwarara da ruwan hawayan zasuyi"Faɗa min mai ya haɗaki da shi, amman kiyi yanda zan saurin fahimta, kuma in yadda zan iya yin kumai dan farin cikin ki, nasan kin san shirye nake da yin abinda zai kawo farin ciki a duniyarki"

   Lafewa tayi ta ƙara narke mashi, sannan ta fara kura bayanan ƙarya wanda tayi imanin zasuyi tasiri a zuciyar mutumin dake gabanta take cikin rikonshi"Na dade ina neman hanyar da zanyi ɗaukar fansa akanshi ban samu ba, ya zalunci ne kuma ya yaudaran kuma shine mutun na farko daya fara........"

   Kukan ta ƙara lalubuwa ta saka mai tsayawa a zuciya, kuma mai ƙuna ruhi"Ina fahimtarki muje ina sauraranki"

   Sai da ta ɗanyi kuka na mintika sannan ta ƙara chakumarshi ta ƙara shigewa jikinshi, sai da ta tabbatar ta guga mashi kirjinta sosai saman jikinshi, sai tin kunanshi ta tsaya hucin numfashinta na sauka cikin kunnanshi sannan tace"Ina shekara goma sha ukku yayi mani fyade, ya lalata mani rayuwa kuma yaci mutuncina"

    Kuka ta ƙara sakawa, hadda jijjiga jiki, da kumai ya dawo mata na rayuwar da tayi a baya da yanda Mijin yayarta ya keta mutuncinta kuka sai ya zama na gaske sosai take kuka kamar ranta zai fita, idanuwanshi ne suka canza kala sosai ya shiga ɓacin rai na jin abinda baiso jinshi ba yanzo, yarinyar da yake jin ƙaunarta har cikin ruhinshi itace yayi ma haka aikuwa ya cancanci kumai ma bayan kura zai tabbatar yayi mashi hukunci mai wuyar kwatance.

    "Na fahimta zanyi yanda kike so, ki haƙura da kumai ki manta da kumai zan baki farincikin da kika rasa"

     Kai ta ɗaga tace "Nagode sosai"



#BILKISUBILYAMINU
#ANATARE
#KM
#VOTE
#COMMENT

KASAITAATTUN MATAWhere stories live. Discover now