Mai laifi ce ni, idan an min hakuri zan gode sosai da sosai, ina maku soyayyya ta fisabilillahi, soyayyata daki Mai amanace ina Sannu har kasan zuciyata.
"A Gurguje nake san gama duk wasu aiyukan dana fara zuwa juma'a nake san barin garin nan tarukan ayyuka sun min yawa Habib, har nakan kasa yanda zan shawu kan al'amuran"
"Kada ka damu zan tafiyar da kumai kamar kana nan, nasan kasan zan iya abinda yafi wanda zakayi, kana manta ni da kai duk daya ne meye amfanin abotar idan har bazan iya zartass da wasu daga cikin al'amuranka ba? saboda haka kada kumai ya zama damuwarka abokina"
"Habib na yadda kai wani bango ne a gaba daya duniyata ina jinka kamar mun fita ciki daya ne, ina godiya da dukkan karamcinka a gareni, sosai nake godiya sosai har bansan iyakar adadin godiyar da zan maka ba, Allah ya biyaka da mafificin alkhairi, ya inganta wanna abota tamu, sosai nake danganta alakata da kai da jinina sannan ina ajeyika a matsayin amini kuma dan uwa"
Murmushi Habib ya aje a saitin Mejo sannann yace"Kana bani mamaki wasu lokuta, kana manta wayeni a wajanka kana manta abotar da aka gina da amana da alkawarin duk rintsi ana tare, to har zaka dinga tuna wani abu, bana tsammanin haka daga wajanka gaskiya, zuwa yanzo ya kamata ka yadda mun wuce wanna babin Allajina"
Kai Mejo ya jinjina yace"Na yadda kuma na gamsu kai ginshikine a duniyata da kumai nawa."
Hannunshi Habib ya kama suka nufi motar Mejo, sannan ya bude mashi ya shiga sai da ya zauna sannann ya rufe mashi mota yana murmushi, kunnanshi ya nuna mashi sannann yace"Muyi waya ko"
Hannuwa suka daga ma junansu sannan shima Habib yaje wajan motarshi yana jin dadin yanda abokinshi ya fara manta kumai dake dawainiya da zuciyarshi, shi dai kuda yana dannewane hakan ya feye mashi da ganin damuwa kwance Saman kykyakyawar fuskar sojan abokinshi.
"Oh Adda Maryam bansanki da wanna kurafin ba har yaushe kika fahimci ina boye make wani abu, idan ma akwai kinsan zan fada maki, please kiyi hakuri babu kumai fa, kuda ma da akwai ina tunanin alkhairi ne fa"
Hannuwanshi ta kama sannann tace"Shi alkhairin ba za'ayi farin cikin nashi dani ba? ku meye ka fada mani mana kasan zan taya ka farin cikinshi fa"
"Na sani amman ki bani lokaci kinji, zaki san kumai, musammamn da ki din abokiyar kumai nawa ce"
"Wai harma lokaci ake ba abin alkhairi kinan, to babu damuwa bamu Saba tursasa juna jin damuwar wani ba, nasan kuma meye zamuyi maganar da kai kuda zuwa nan da shekara nawa ne dole zan sani babu damuwa ni kam na hakura"
"Haka ne sweet, Isman sunyi bacci ne?"
"Eh tun dazon sun gaji da jiranka suka kwanta, har yana cewa baka Saba kai dare haka ba, nace Kila wani akin ya rike ka, tunda ba saba kai dare kake haka ba"
Murmushi yayi baisan ya zai fara fada mata zai kara aure ba, bai kuma san kalar kishinta ba, idan taji wanna labarin yasan duk mace tana kishin mijinta, amman bai san kalar nata kishin ba, Allah yasa tana cikin mata masu saukin kai da hangen nisa"
"Tashi muje kaci abinci nasan akwai yunwa tare da kai, kuma nasan mijina baya cin abinci har sai ya dawo gida, am proud of you, Ni mace ce mai sa'a, kumai na mijina daban yake dana sauran maza, Ya Abdul kasan me?
Idanuwanshi ya saka cikin nata yana kara karantar yanda zataji idan taji zai kara auro mata wata su zauna su biyu a karkashin ikonshi"Ina jinki"
"Ina jin kamar ni kadai Allah ya halitta da kasancewa matarka, Ina jin dadin yanda kake kula dani inaji ni daya macen da tayi sa'a a rayuwa da samun miji tamkar kai, Inajin zan iya kumai domin ganin farin cikin ka, Inajin kai wani haskeni a kasan zuciyata, Ya Abdul wallahi kai kadai duniyata take so, nasan idan na rasaka bazan iya rayuwa ba, bansan kuwa ba sai kai, da soyayyarka na girma na gina duniyata kai kadai na iya so, dan Allah kada ka shigo da abinda zai tsarwatsa farin cikinmu ni da kai mahadin jin dadin juna ne, idan babu kai nasan nayi sallama da duk wani jin dadin duniya sosai nake amsar duk wata kaddarar soyayyarka da hannuwa biyu, Ya Abdul ina sanka nasan ka san haka dan Allah kada ka bada kofar rugujewar kaunar da aka gina tun kafin a yadda a amsa kaunar ce"
Hawaye ne ya zubu daga kwarmin idanta, a hankali ta share tana sakar mashi kayataccen murmushi tasa hannunshi ta goge hawayen daya xuba daga kwarmin idanta, sosai ya kadu da dukkan wani furuci dake fita daga bakinta bai ta6a zullumin wanna abinda yake ganin shine kwanciyar hankalinshi ba sai yau, sosai ya hango soyayyarshi kwance saman idanuwan Adda Maryam yasan duk wata magana dake fita daga bakinta tana furtawa ne da dukkan gaskiyarta da kuma amanna, baisan ya zai bulluma kumai dake neman kwance mashi ba, rasa Aisha a rayuwarshi dai dai yake da dauwama cikin kuncin rayuwa dan ya gama yadda itace macen dake jiran duniyarshi, ita kadai ce macen da ku idanuwansu suka hadu waje guda yake jin zai iya rasa natsuwarshi saboda irin dunbin kaunarta dake daskare a kasan ruhinshi, gefe daya kuma yana jinjina yanda zai fahimtar da Adda maryam ta fahimceshi yana sonta kuma Karin auran ba zai hanashi bayyana mata soyayya da yake bayyana matan ba, kawai dai A'isha cikin farin cikin shi ce .
"Me kake tunani Ya Abdul? "
"Kawai ina tuna maganganunki na yanzo ne, sai inga ki dan rangwanta, idan babu mutuwa akwai halin rayuwa, idan na karu maki kanwa kuma ya zakiyi kinan"
Murmushi tayi sannann tace"Nasan baka da wanna ra'ayin Ya Abdul nasan kai kanka ba zaka su illata rayuwata ba nasan haka, amman Nasan zaka iya canza tunani ku kuma zaka iya haduwa da kaddara karawan. "
"Kara aure illata rayuwa ne Maryam, bana tunanin haka yana da illah, to idan kuma haka shafin kadddarata ya bude fa? Na dole sai na kara"
A Dan firgece ta kalleshi jin ya fadi sunanta kai tsaye haka kuma da dan wani sautin kamar yana cikin fushi, ita ma da Kwaren gwaiwa tace"Sosai ma saboda ba zan iya hada soyayyata da wata ba, kasan ma bazai yewu ba kai kadai nake so kuma da kai kadai zan rayuwata, shi shafin kaddarar ba zai taba bude maka ba sai dai idan budashi akayi. "
Hannuwanta ya kama sannann ya mikar da ita, yana jin faduwar gaba"Muje a bani abincin bana san maganar ma gaba daya kada ta kawo mana bacin rai"
"Wannan maganar ba Zara taba kawo matsala tsakanin da kai ba Insha Allahu."
"Allahu yasa Babby girl."