Cikakkiyar ƙarfin addu'ar daya dage dayi ne yasa ya fara samun sauƙin damuwa da ƙuncin dake ƙasan zuciyarshi zuwa yanzo ya fara samun sa'ida har ya kuma dai-dai kamar da amman bawai dan ya manta da abinda yafi ƙauna a gaba ɗaya duniyarshi ba, shi kadai yasan yanda yake jin matar dake zuwa mashi a mafarki take a ƙasan ruhinshi zuwa yanzo ya aminci ganinta da kuma mallakarta shine kawai abinda zai sama mashi wanzuwar farin ciki, amman idan har bai ƙara ganinta a karo na biyu ba yasan yayi banƙwana da farin ciki zai dai kawai sai-sai ta kanshi domin farin cikin iyalinshi bawai dan shi kanshi farin cikin zai dauwama a duniyarshi ba.
Idanuwanshi ya lumshi sannan ya jingina da kujerar dake girke a officin da aka tana da domin babban Mejo General Al'mustapha, surarta ce ta fara bayyana a cikin ɓoyayyun idanuwanshi sannan kuma da zahirin zuciyarshi sosai tayi kyan da baisan ya zai misalta yanda tazo mashi a wannan lokacin ba, kanshi ta shafa sannan ta sakar mashi wani murmushi mai wuyar fassarawa, daga bisani ta ranƙwafa ta sumbaci saman leɓanshi, sai tin kunnanshi ta aje mashi wani furucin da yake kamar bala'i ku rubutu yake yawancin kalmar takan faɗo mashi"Be my husban"
Juyawa tayi zata tafi ya chafko hannunta sannan yace"Ina san ganin ki, ki bayyana kanki a gareni idan kin fahimta ina nufin kice rayuwata"
Hannunta ta janye daga nashi sannan tace"Zamu kasance tare amman kuma...."
Wayarshi ce take kuka, a hankali ya buɗe rinannun idanuwanshi da suka
Kaɗa sukayi wata kalar da bansan yanda zan bayyana al'amarin ba, a hankali ya kai hannunshi ya ɗauka sunan da ya sani ne saman wayar ya sa babu yanda zaiyi dole ya ɗauka, cikin natsuwa ya kanga wayar dai-dai saitin kunnanshi, daga ɓangaranshi yace"Habib ya?"Daga can ɓangaran ya amsa da"Lafiya lau Musty ya aikin?"
"Muna ma Allah godiya"
"Masha Allahu, daman naje porta cort ne, shine zan biyu sai mu wuce tare, ban sani ba ko zaka weak end, sai mu wuce tunda gobe Friday ƙurarran lokaci ne"
Kanshi ya shafa da daya hannun sannan ya lumshi ido yace"Babu damuwa ayi hakan"
"Babu matsala?"
"Babu, sai kazo, ka kusa shigowa Abujar ne?"
"Insha Allahu sauran kaɗan da izinin Allah"
"Allah ya iso min da kai lafiya, friend inded"
"Mejo akwai tambayoyi bakina a kanka, nasan kasan haka"
"Na sani Habib nima akwai amsoshinka bakina, zan buɗa maka kumai nasan zan samu mafita"
"Sai na iso ɗin dai, Abokina keep praying nasan kana da damuwa"
"Sosai ma har bansan ya zanyi da rayuwata ba, har ina jin daman Allah bai haliccine a duran duniya ba Habib"
"Subhanallahi Abokina muyi magana idan na iso din"
"A iso lafiya"
"Aha mutumina"
Dariya sukayi gaba ɗayansu sannan suka aje wayar a lokaci guda, sosai suke san junansu suke kuma ƙaunar junansu har ankai munzalin da dan Adam bai isa ya bayyana amincin dake tsakaninsu ba, aminta ce ake tamkar ƴan uwa. ƴan uwan ma kamar na ciki ɗaya rayuwa kinan idan wani ya ƙeka wani sai ya maidaka ɗan uwanshi na jini sosai, dan ma wannan duniyar amana tayi wuya, ka yadda da mutum yaci a manarka, ka bashi amana yaci ta abinda yafi sauƙi kinan a wannan duniyar, musamman duniyarsu malam bahaushe, Allah ka haɗamu da aminai na kwarai Ameen.
Rinannun idanuwanshi ya ƙara lumshewa sannan ya cige leɓenshi na ƙasa yana jin wani radaɗi na wanzuwa a ƙasan zuciyarshi baisan ya zaiyi da rayuwarshi ba, abubuwan suna faruwa kamar wahayi, idan ya sa mu sukuni zuwa wani lokaci sai Allah ya ƙara jaraftarshi da wani saban al'amarin a kanta wannan wace irin rayuwa ce, hannuwanshi ya ɗaga sama bayan wasu siraran hawaye na zuba daga kwarmin idanuwanshi a bayyane yake cewa"Ya Allah idan wani laifi na maka Allah ka gafarta mani ka sauƙaƙa mani al'amuran rayuwata, tunda na mallaki hankalin kaina ban ƙara hutawa ba da dakon san abinda har zuwa yanzo ban gasgata akwaishi a duran duniya ba ko babu shi, ya Allah idan wannan baiwa taka mutunci Allah ka haɗamu idan ba mutum bace Allah ka fidda mani wannan uƙuba da nake ciki, ya Allah ka mallaka mani kuman kumai rayuwa amman Allah ka ɗauke farin ciki na, idan wannan al'amari wata kaddarace a shafin rayuwata Allah na tuba Allah ka sassauta mani Allah na tuba, Allah ban kasance ɗaya daga cikin masu aikata munannan ayuka ba, sai dai kuma wanda ajizanci na ɗan adam Allah ka rufa asirina ka sani cikin cikakkun mutane masu yanci, ya Allah nasan soyyar wannan baiwa taka itace ajalina.
Sosai yake kallan Ogan nashi bayan babban tashin hankali dake kwance a saman fuskarshi bai taɓa tsammanin babban soja namijin duniya mai zati da haiba, irin wannan zai zauna yana zuba oban kuka haka ba, sannan wasu kalamai daya tsinta a wannan addu'ar tashi sosai ya ɗaga mashi hankali wannan shi ya tabbatar mashi da cewa duk yanda mutum ke rayuwa akwai wani ɓoyayyan abu a cikin duniyarshi, lallai rayuwa akwai kalubalai, lallai ya kama ta mutane su kuma ga Allah subhanahu wata ala.
Da ƙyar ya samu yace"Sir files din nan nazo amsa na daɗi ina sallama amman ba'a amsa ba"
Bai damu da ya share hawayan dake zuba a fuskarshi ba, jajayen idanuwanshi ya aje cikin na Aliyu sannan yace"Zauna in tambayeka Aliyu"
Jikin Aliyu babu lakka ya ja jikinshi ya ɗaskwana saman kujerar dake gaban babban tebur din dake gaban Mejo Al'mustapha, kanshi ya sadda ƙasa yana kara jinjina rayuwa da tabbatar ma kanshi da duk wani abu dake duran duniya ba'a bakin kumai yake ba.
Kuma baida tabbas, duba da yanda gaba ɗaya kumai ya canza ma Oganshi da suke yanzo waje ɗaya.Idanuwa Mejo ya tsareshi dasu, Aliyu yayi da ya dago kanshi suka haɗa idanuwa da Mejo a hankali ya buɗe baki "Aliyu akwai wani abu da nake wanda bana dai-dai kuma yana daya daga cikin abinda Allah zai hukunta mutum dashi a iyakar zaman da mukayi da kai?"
Gaban Aliyu ne ya faɗi sannan hankalinshi ya tashi dan yasan waye yake zaune a gabanshi, duk da shi ba ma'abocin tsegume bane amman yana gudun ace wani abu aka faɗa ma Mejo kuma akace shi ya faɗi, jiɓi ne yake tsatsafuwa daga goshin shi sannan ya dan rissina yace"Sir, babu"
Kara aje kallanshi yayi na wasu mintika sannan yace"Aliyu dan Allah idan ina aikata wani laifi da na chan chanci Allah ya jaraftan da wannan rayuwar ka faɗa mani in hankalta in daina kuna samu sassaucin rayuwa irinku da kullum kuke cikin nishaɗi.
Zuwa yanzo bai gama fahimci Inda maganganunshi sukayi ba Amman cikin karfin hali yace"Sir, a iyakar adadin shekarun da nake aiki tare da kai wallahi ban taɓa samun cikakken mutum kamar ka ba, yawancin masu irin aikinmu da wuya a samu cikakken mutum amman Sir, na rantse maka da zatin Allah kana ɗaya daga cikin mutanan da wannan aiki namu yake da bukatar irinku da yawa, nayi imani kai nagartacce ni kuma Allah ya aminta da kai"
"Aliyu ka ƙara dubawa nasan akwai abinda nake wanda Allah ya aza wannan kaddarar a shafin rayuwata"
"Babu Sir, shi Allah yana jaraftar kyawawan bayinshi wadan da sukayi imani dashi kuma suka shaida babu abun bautawa da gaskiya sai shi kuma Annabi mohammadu manzansa ne, yakan zarrabi bawanshi da shafukan addara yaga zai iya jurewa ku zai iya chanza akalar tunaninshi ta wata hanya daban, Sir ka gode ma Allah irinku khalilian ne a wannan zamanin, kuwa ka gani da tasa kalar kaddarar wallahi idan ka bincika wani yana cikin kuncin da sai ka tausaya mashi, ina ganina addu'a itace abu mai mahimmanci"