Alhamdulillahi Nasan kuna hakuri ku kara da wanda kuke dashi, ina fahimtar yanda nake kasuwa wajan biyan bukatunki, kuyi min afawa ayuka kemin yawa, a hankali zamu kawo karshan abun.
"Wayarta ta dauka, saboda gaba daya bata yadda da kumai nata ba yanzo, sosai take san ta yadda ba amanarta take ci ba, bata san ta fara zarginta tun yanzo, tune ta yadda yarinyar itace kumai nata, kuma da gaske zata iya kumai akan yarinyar, kamar yanda ta fadi ciki hadda dauka rayuwar mutanan dake san shiga tsakaninsu, wancan password din da ta sanshi da wayar ta saka sai taga bai yi ba, kara dannawa tayi, sau ukku tanayi taga baiyi ba, hakan ya tabbatar mata da akwai matsala batai tsammanin haka ba, kai ta girgiza sannan ta ajeyi wayar da niyyar kuma meye zata tabbatar ta ganu a yau ba sai gobe ba.
Wanka ta fito tana goge fuskarta da towel din jikinta idanuwa Nuwaira ta kura mata tana jin wani zafi a kasan zuciyarta, sosai take zargin akwai wani abunda ita bata sani ba, kai ta kauda sannan tace" Minal"
Da sauri Minal ta juyu jin yanda Nuwaira ta kira sunanta kai tsaya kuma ga alama akwai wani karsashe a cikin muryarta. Da faduwar gaba ta amsa sannan ta maida towel din jikinta ta daura sannan ta zauna kusa da Nuwairar" Gani, love of my life"
"A shekarun da muka dauka dake nasha fada maki maganganu wadan da ya kamata ke ajeyi a kasan zuciyarki, na soki kamar ban taba kuwa a duniyata ba, haka kullum soyayyarki kara nunkuwa take a kasan zuciyata, banasan abinda zai zama ta kura a kanki, kinsan adadin mutanan dana bata dasu musamman saboda ke, kafin in zama wata a yanzo karkashen wasu nake, saboda sun ce dole sai kin zama cikin kungiya naki amincewa na 6ata da kuwa wanda sun taka mahimmiyar rawa a duniyata, Akan idanuwanki nama Laila kashedin ta fita harkar ki, idan zan iya ma Laila wannan kashedin to kinga babu wanda bazan iya ma waba a duran duniya, Inasan ki fadi mani abinda ni ban sani ba, kamar yanda na fada maki idan na ganu, abin bazai maki kyau ba, Na rantse maki da wanda raina ke hannunshi zanyi maki abu kamar idanuwana basu taba sauka a kanki ba"
Idanuwan Minal sun fito sosai zufa ke kwaranya ta tsakankanin gashinta, kai Nuwaira ta kauda sannan ta kara cewa" For d last time, ke fada mani halin da kike cike bana san in ganu mu samu matsala dake, dan abin bana tsammanin zai mana kyau dagani har ki din, gwamma ki fada mani sai kumai yanzo da sauki, kuma zan fahimce ke"
Wayar Minal din ta dauku ta mika mata"Bude min akwai abubuwa da nake san dubawa, tunda ban isa insan sirrinke ba kin rufe waya, wanda ni sama nake da ke, kuma karkashen ikona kike amman ban maki iyaka da kumai nawa ba amman gashi kina min iyaka da wayarki tuni na fahimce akwai abinda kike boye min yarinya"
Mika mata ta karayi tace" Bude min"
Sosai Minal taji tashin hankali da bata taba tsammanin akwishe a duran duniya ba, tayi imani yauce dubunta zata cika, wayan ta amsa musamman yanda ta saka idanuwanta cikin na Nuwaira ta tabbatar ma kanta babu sauki, bude wayan tayi sannan ta mika mata, gallery ta fara shiga ta duba duk abinda take san dubawa bata samu kumai ba, sannan ta kuma wajan message ta fara cin karu da wasu message wadan da gaba daya suka canza mata kwakwalwa cikin sakan biyu zuwa ukku.
Sosai ta kafe Lambar da mafi akasari Message dinta ne, kai ta girgiza wani uban jibi yana wanke gushinta kai ta dago ta saka renannun idanuwanta cikin na Minal tace"Tsawan yaushe kika dauka kina cin amana ta?"
Kuka Minal ta saka tace"Nasan ni mai laifi ce kada ki tambayeni ki hukunta ni, amman har yau na kasa yadda ni din da hankalina na aikata abinda na aikata.
Habib ne zaune suna lissafin kumai na abinda yasan za,a bukata a gidan ya gama sayan shi, Abdulwaheed ya sanya daya daga cikin motocinshi masu kai kaya suka kai kayan gidan Mejo domin cigaba da aikin daya barmushi a matsayin jagoranshi.
A hankali ya lumshe idansa sannan ya cire barrette din kanshi ya shafa sumar kanshi, sosai yake azaftuwa da rashin bayyanarta yasan akwaita kuma ya tabbatar da zahirin ita din dai mutunci kuma a akwaita a duran duniya, a karshe ma da idanuwanshi ya ganta, Amman Allah bai iya bashi daman samun ya gana da ita ba, abinda har yau ya kasa yadda dashi shine, Shin da gaske ita din yar bariki ce musamman da ya ganta a hotel inda bai dace ba, shin me take a wajan da duk macen da ta amsa sunanta mace ba zata kasance a wajan ba, matan aure na zuwa taran kara ma juna sani, amman yanayin ta bai nuna tana da aure ba, Me ya kai ta wajan? Wa taje nema? Meye alakarta da wajan? Shi kanshi yasan bai isa ya ba kanshi wannan amsar ba, leban kasan bakinshi ya lasa, yana jin wani numfashi mai zafi yana fita a Kofofin hancin shi, wannan wacce irin kaddara ce, da aka jarafceshi da kuma mace, Macen ma ga alamun ba kamila bace shi dai yasan a tarihin duniyar shi bai ta6a amfani ko kusantar wata da sunan aikata abunda allah ya hana ba. amma shi Allah ya jarabeshi da san abinda yakasa gane madugararta da manufarta, tagumi yayi yace"Allah na tuba, Allah ka yafamin, Allah ka shiga lamurana, Allah na san ni dan Adam ne kuma ajizi, Allah kajarabeni da abinda kasan zan iya, Allah ka shiga lamurana in cinye wannan jarabawa, Allah kaji tausayina ka bayyana mani ita"
Da sallama ya shigo ya kame sanan yace"Sir na Aywatar da abinda kasani, sai dana tabbatar sun tafi, kuma sir bataliyar dana tura na tabbatar zasuyi abinda muke bukata"Idanuwa shi ya lumshe sannan ya bude su ya daura tsakanin idanuwan Aliyu sannan yace"Good work, zauna muyi magana da kai please"
"Ok, sir"
Gyara zamanshi yayi saman kujerar da yake sannan yace" Aliyu kasan Allah yana jaraftar Bawa ta kuwacce hanya da bai taba tunani ba ku hankalinshi ya kawo zai faru da shi, yana ajeyi kaddara a shafin kuwa, sai dai ta wani tana ninka ta wani a fagen jaraftuwa. Muminin bawa shi ake jarafta ya jure ya kuma yadda ya aminci bawai dan Allah baya sanshi bane, da yawan mutane sukan kasa hakuri da abinda Allah ya aje a shafin kaddararsu, sai su butulci mashi, da zan fada maka kalar tawa kaddarar Aliyu zaka tausaya mani zaka ga kai taka mai sauke ce, amman nayi hkuri na kuma yadda shi kumai yana da Lokaci banda Bautar ubangiji, Aliyu kaddarata bautace ta ubangiji, kuma insha Allahu inajin zan iya samun nasara, saboda Karin shiga ta damuwa ya fara ne daga lokacin da nasan akwaita a duran duniya kuma ita din mutunci bawai wani jinsi na daban ba, nasan kana fahimtar ina cikin damuwa, kumai zai zama tarihi nisha Allahu, ina ji a kasan zuciyata ta kusa zama cikin ikona"
"Allah ya kawo mana mafita Sir, amman ni kaina ina cikin wani hali, har zuwa yanzo sun kasa fahimtar na yadda na aikata kuskuren da zan dauwama ina nadama har gaban abada"
"Zuwa anjima ka shirya zamuje gidan sirikan naka
Insha Allahu zamu samu abinda muka je nema, basai na maka fada akan abinda kayi ba, wannan kadai ma hujjace da kuma amsar abinda zai iya kara faruwa idan haka ta kara kasancewa""Ina dauka kai Ubane a garin ban taba ajeka a gefen shugaba ba a wajan aiki ba, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi ngde sosai Allah ya kara bani cikin kyauta maka"
"Zan neme ka anjima sai Muje ka dage da addu'a"
"Tun daga ranar har zuwa yau addu'a nake, zan kuma dauwama inayi har karshen rayuwata"
"Fine, Allahu yayi mana jagura"