kasaitattun mata

2.5K 185 5
                                    

KASAITATTUN MATA
Labarin Mata Ukku

 
     A gurguje ta faɗa wanka ta shiga ƙarƙashin shawa ta dirje duk wani gaɓɓa na jikinta da Allah ya halitta dan yau fitar da zatayi mai zafi ce, saboda gwamna take san kulla babbar alaƙa da shi domin samun cikar burinta na ɗaukar fansa. Bata sani ba ko tarkon ta zaiyi dai dai saboda an tabbatar mata da mata ba damuwar shi bace, amman zata gwada insha Allahu domin shi kadai ne jigonta a abinda ta kuduri niyyar yi, a ɓangare ɗaya kuma ta jadadda ma _Breaker_ abinda take da buƙata ya wakana a gidan mutumin da take ganin yayi ganganci da rayuwarshi wajan yunƙurin yi mata wulaƴanci bayan ta ɗauke dukkan wani santa ta dura a kanshi duk da ba auranshi zatayi ba amman yayi mata, bata ture dukkan wani buƙata daya zo mata da shi, sosai yake ƙishin ruwanta, a dukkan mazan da suka gurje juna ita da su babu wanda ya iya maida kwadayinta irinshi wata kila Allah ya halittasu a matsunne guda ne, kuma sun kasance nau'insu ɗaya.

    Sosai ta gyara jikinta sannan ta saka jallabiya kalar ɓaka mai kyan gaske samfarin ƙasar saudiyya sannan tayi _rolling_ da ƙaramin farin gyale, farin takalmi _flat_ ta saka ma ƙafarta sannan ta ɗauke farar ƙaramar jikka mai kyau samfarin HTZ, kalolin _Oud Collection_ ta watsa ma jikinta tabi da sihirtaccen turaranta wanda boka jajatau yake haɗa mata idan buƙatar irin wannan haɗuwar ta tasu, rigarta ta ɗaga ta shafa ƙasan mararta da ƙasan nashanunta, wayoyinta ta ɗauka guda biyu waɗan da kuɗinsu zasu ishe wani talaka jali, agogon hannunta ta duba taga huɗu sauran minti kaɗan kuma huɗu dai-dai shine alƙawarin _appointment_ dinga da gwamna, motarta kirar  COROLA LE kalar  blue  ta shiga  plate number din an rubuta Ƙasaitattun Mata .... 7, horn tayi mai gadi ya buɗe mata ta ɗaga mashi hannu sannan ta rufe tint glass din motar fita tayi daga gidan kamar wadda aka biyu da gudu, daga gefe malam Amadu mai case daga ɗan nesa ya ƙurama yanda motar take cilla uban gudu a saman ƙwaltar da aka ɗan maƙala a titin shiga GRA din ta masu hannu da maiƙo, kai ya girgiza ya kalle wani dattejo shima dake kusa da shi suna fira saman ɗan dakalin ƙofar shagwan yace"Allah ya shirya mata zuri'a malam Ummaru"

    "Ameen Malam Amadu mai yasa kayi wannan maganar?"

    "Yanda yaran wancan gidan masu zaman kansu suke ɗaukar mota kamar cikin gidan su shine yake bani mamaki"

    Dariya Malam Ummaru yayi sannan yace"Bansan dalilin da yasa kake yawan damuwa da rayuwasu waɗan nan yaran ba"

    "Ina tausaya ma rayuwarsu ne kawai, da suka banzatar da kansu ake ta amfani da abinda Allah ya halitta masu"

    "Abinda nake gudar masu ma cutar wannan zamanin"

    "Hmmm ai su wadan nan yaran abinda suka dugara dashi kinan bana tunanin zasu yadda su ɗauke wata cuta"

    "Allah ya kyauta amman dai wannan rayuwar ba mai ɓullewa bace"

     "Malam Ummaru aureni yayi dai dai da rayuwarsu, amman yara masu nagari kamar wadan nan ace karuwanci suka saka gaba, ai kuwa ya za'ayi mutane su zauna lafiya"

    "Allah ya shirya mana zuri'a kawai, ya kuma shiryar dasu"

     "Ameen Malam Amadu"

     Sai da ta sai-sai ta kanta saman titi sannan ta ɗauke ɗaya daga cikin wayoyinta tayi _dialing_ wata _number_ ta kanga saman kunnenta daga ɗaya mangaran aka ce"Ina jinki Hajiya"

    "Yauwa ina saman hanya insha Allahu _in minute_ na shigo govment _house_ din"

     "Till you came"

    "On my way insha Allahu"

  Ta katse wayar ta wurga cikin abinda aka tana da domin ajiyar abubuwan kamar wayar, speed ɗin motar ta ƙara sannan ta tasamma gidan gwamnatin.

KASAITAATTUN MATAWhere stories live. Discover now