kasaitattun mata

2.3K 201 11
                                    


     Jingina yayi da bayan kujerar sannan ya cika hannunahi yabdauku wani file ya mika ma Aliyu yace"Nagode Aliyu"

   Mikewa Aliyu yayi sannan ya kame yace"Tnx you Sir"

   Murmushi Mejo ya aje mashi sannan ya daga mashi hannu ya tafi amman akwai abubuwan da dama a kasan zuciyarshi amman babu halin saninsu dan ba'a hurumin yake ba.

   Kuma meye ki damun Oganshi yana mashi addu'ar Allah ya sausauta mashi dan sosai yake san Ogan mashi duba da ba daya yake da sauran Oganinshi da yake aiki da su ba.

    *KADUNA, GOVERNMENT HOUSE.*

    Tun ranar da Laila ta gwaɗa kalar barikinta wajan _Excellency_ abubuwan suka canza mashi sosai yake san ƙara ganin ta wannan kaɗan da wata irin buƙatuwa yake da muradin sake haɗuwa da ita, ɗaya daga cikin baiwar da Allah yayi masu kinan baka isa su lasa maka wani abu na daga wajansu ba kace ka kyalesu idan ba suɗin suka buƙaci haka ba, mai yewuwa akwai wani sinadari da bokansu ya haɗa masu ko kuma kawai tsabar halittar da Allah yayi masu ne oho, amman dai a yanzo kuma a wannan lokacin babu abinda _Excellency_ yake da muradi sai Laila, hular kanshi ya shafa sannan ya kalle PA dinshi yace"Idan babu damuwa duk wani _Appointement_ dake da akwai mu bari zuwa gobe"

    _"OK, Sir_ amman akwai wani mahimmin _appointment_ wanda ya kamata a ganshi yau"

   "Wa kinan?"

   _"The minister, what I mean is the minister of health"_

   _"Cancelled the appointment_ kawai sai zuwa gobe, akwai mahimmin abun da zanyi a yammacin yau"

   Wayar ya ɗaga ya kanga saman kunnanshi sannan yace"Yauwa zan maka tex din wani Adrees yanzo, _drop her at My Guest House"_

   Ƙara _balance_ yayi saman kujerar sannan ya ƙara _dialing number_ Laila daga daya bangaran tace"Allah ya taimaki _Excellency_"

   Murmushi yayi wanda daga Inda take tuna jin yanda yake fita yace"Nasan a yanzo baki da wani uzuri, ina nufin za'a zo a daukar mani ke, sosai nake san abokiyar fira sai na zabi amsar bakuncinki ina fatan zan samu yanda nake so"

   Wata mayaudariyar dariya ta saka sannan tace"Kuda ina da uzurin yi tabbas zan ajeyishi inyi naka dan kai din ka faye mani kumai, ina nufin kana da babban matsayi a duniya ta,so zan shirya din"

    "To madalla babu damuwa, a bani adreshi"

    "Yanzo kuwa Sir"

    A lokaci guda suka aje waya, da sauri ta aika mashi da adreshinta sannan ta tashi daga hotel din da ta kama na tsawan kwana biyar saboda aikin da take a kan Sanata, ta shiga motarta ta nufi gida dan adreshin gidan ta bada, minti ukku da isarta aka shaida mata ana jiranta, a gurguje ta fada bayi ta dan saki ruwa a karkashin shawa sannan ta fito ta murza kalolin mayokanta, turaranta da boka ya hada mata ta dauke ta shafa kasan mararta da kuma kasan mamanunanta, wata drower ta bude ta dauku wata jarka wadda take cike da wani magani ta kada kai ta kurba, sannan ta dauku auduga ta bude wata yar ruba ta dangwali wani magani ciki ta daga kafarta daya ta saka cikin gabanta sannan ta bar shi hadda audigar, karamar handbag dinta ta dauka sannan ta jefa wata matsiyaciyar rigar bacci cikinta da yan abubuwan da ba zata rasa ba, ta kulle dakinta ta fito falo ta iske Nuwaira da Minal suna kwakwular juna kamar zasu maida juna ciki tsaki tayi ta dauke kai ta kama hanyar fita, da sauri Nuwaira ta tashi tace"Laila I need to talk to you"

    Ko sauraranta batayi ba tace"Bani da lokaci gaskiya"

    Ta fita gidan gaba daya, da mamaki Nuwaira ta tsaya tana tunanin yanda akai Laila ta bijeru mata da wannan mugayen halayan kawai dan ta aje Minal a cikin gidan shiyasa take mata haka.

KASAITAATTUN MATAWhere stories live. Discover now