kuyi min aikin gafara da jinkirin zuwan wanan labari, idan kuna fahimtar kurafina ayyuka ke min yawa sosai, amman ina tare daku kuma ina sanku har cikin zuciyata, abokai na abin alfaharina, ina maku fatan alkhairi.
"Ok Habib ina jiranka to"
Wayar da ya gama yanzo ya riƙe a hannunshi yana ci gaba da dannawa, gefen gado yasamu ya zauna ƙirjinshi ya dafe yana jin wata zufa na ketuwa a dukkan wata ƙofa dake jikinshi, baisan wani irin yanayi yake ciki ba, baisan maike faruwa da al'amuranshi na safiyar yau ba, ya akai yake cikin wanan matsen, da bugawar zuciya a dukkan wani sakan da numfashi zai fita da bugawar zuciyarshi, addu'a yake maimaitawa a ƙasan zuciyarshi yana neman tsare da duk ma abinda zai faru dashi yana du'ae wajan lillahi daya zama mafi alkairi ga duniyarshi.
Kafaɗunshi ta dafa ta baya, sannan taɗan matsa su"Sojana mai ke faruwa da kai ne, kayi wani kala kamar ba sojana ba"
"Hannunta ya kamu sannan ya zagayu da ita ta zauna a saman kafafuwanshi, kan shi ya ɗura saman kafaɗarta hannuwanta dukka biyu ya kama ya matse"Bansan meke damuna ba Khadeena haka nan nake jin faɗuwar gaba, kiyi min addu'a idan sharri ne ya nisanta damu, idan alkhaire ne muna maraba dashi, soaai nake jin zuciyata na bugawa da dukkan wani sakan da zai buga na lokaci"
"Kuma meye nayi imani alkhairi ne, Allah yasa mafarkin ka ne zai zama gaskiya Sojana, ina san mu dukkanmu samu farin ciki, dan sosai nake shiga cikin matse da samun naƙasu a mu'amalarmu da mijina farin cikina"
"Bani da wani mafarki bayan kasancewa tare da ku, a karkashina har karshan duniyarmu"
"Hmmmm ni dai nayi addu'a Allah ya sanya mafarkinka ya zama gaskiya, a kanta kadai na taɓa ganin kumai na rashin kuzarinka, ni dai nasan sojan mijina tun bansan kumai na rayuwa ba, a kanta kadai nasan kana shiga matsaen rayuwa, kaga kuwa bayyananarta alkairine ta shigo kuwa ya huta in samu kulawar mijina feye da dama"
Wayarshi ce ta fara kuka, janyeta yayi daga jikinshi yana dariya ƙasa ƙasa yace"Habib ne yazo, zamu fita"
"Ka kula min da kanka, sosai ina maka fatan samun alkhairin dake cikin wannan ranar"
Laɓɓanshi ya aje mata a saman goshi "Ina alfahari dake matata"
Fita yayi saman kafafuwanshi da suke aje kuwacce ƙara a dukkan inda ya saka kafarshi ya ɗauke, sosai ta ajeye ajiyar zuciya bayan ya rufe ƙofar babban falon sashin shi, hawayan da take rukewa suka zubu ta goge, bata san wace kalar ƙaddara ce ke bibiyar ta ba, tasa ku wacece a duniyar Mejo Almustapha babban matsayi gareta dan ba da wasa yake azaftuwa da dukkan rashin ta ba, a ma bai gama ganinta ba, idan ya ganta ta zama mallakinshi bata san ya zata kasance ba, hawayan ta kara sharewa da tayi ammanna da zai kamanta adalci tsakaninsu.
Da dan kuzarinta take kumai dan sosai take jin wani farin ciki wanda bata san daga ina ya fito ba, sosai tayi kyan da ta daɗi batayi irinshi ba, motarta ta ɗauka sai da ta biya super maket ta siya wasu yan abubuwan buƙata na gida, dan sanda zata tashi daga wajan aiki bata da lokacin tsayawa, da ɗan saurinta take hawa matakalar binan, sannan wani nishadi na yawo a duniyarta, shiga tayi office din da yar sallama a saman bakinta, idanuwa ya dago suka haɗa idanuwansy dana juna murmushi ya sakar mata, hanyar wajan zamanta tayi tana murmushi ita ma, hannu ya nuna mata tazo inda yake, da ɗan hanzari take tafiya saman ƙafafuwanta har ta isa wajan zamanshi, hannunta ya kamu ya aje labbanshi saman hannunta ya sakar mata sumba, idanuwanta ta lumshe tana jin wani nishaɗi na sauka a dukkan wata ƙafa ta jikinta, ta gama imanin cewa Abdulwaheed shine mafarkinta kuma ta saduda da dukkan wani ƙudurin da ya kawota garin domin shi, ta tabbatar shine mutumin dake cikin mafarkinta dan ya wargaza kumai da take da niyya a kanshi, bayan ma baisan mai ya kawota garin na bauchi ba.
"Daga jiya zuwa safiyar yau nayi matukar kewar wannan fuskar mai yalwar fara'a da sanya zuciyata natsuwa"
Murmushi tayi sannan ta rausayar da idanuwanta sosai ta tafida dukkan ɗan kuzarin da yayi mashi saura a jiki, kai ya kauda yana ajeye wata ajiyar zuciyar da ta fito fili sosai"Idan kin yadda ire iren waɗan nan abubuwan ki adana mani su har sai sanda kika zama cikin kulawar Abdulwaheed, ina bukatarsu a lokacin, kima zasu fi maki amfani a wannan lokacin, amman a irin wannan yanayin ayi min hakuri bana iya ɗaukarsu"
Dariya tayi sosai sannan tace"Kadai riga ka fassara duk wani mutse da zanyi a zuwan da gangan nake maka, ban taɓa kumai dan inja ra'ayinka a kaina ba, kawai haka nake"
"To lallai akwai damuwa, dan duk ranar da kikayi da zuwan jan ra'ayin nawa zaki tafi da rayuwata ne kawai"
"To ba zanyi ba, nasan ma ba zamu zama a inuwa ɗaya ba ni da kai"
Yanayinshi ne ya canza bayan ya tamke fuska sosai, yanda zata fahimci abinda yake faɗa yana faɗa ne da dukkan gaskiyarshi"Ko meye dalilinki da tun yanzo kika nisanta kanki da abin alkhairi, kin san kuwa abinda kika faɗa me yake nufi?"
Idanuwanta ne suka canza kala daga farare tas zuwa kalar jaja, da kuma ruwan hawaye"Baka san wacece ni ba shiyasa ma kake kukarin faɗawa tarkon sona"
"Ok kukari ma nake kinan bawai na faɗa ba, to nagode da yanayina da kika bata yanzo babu jimawa, sai dai kada ki manta ki rike wannan a zuciyarki, babu abinda zai canzani daga ƙudurina a kanki sai dai idan mutuwa, kuma ku wacece ke zan zauna dake da dukkan adalci da amanata, kuda kuwa baki da kuwa a duniyarnan ki ɗaya ce, ina sonki a haka Aisha"
#BILKISUBILYAMINU.
#ANATARE.
#FISABILILLAH.