SOYAYYA.

2.4K 265 27
                                    

    Shafin Abdulwahees da Aisha Beauty, Soyayya mai taɓa zuciya da shauƙin so, kuyi hakuri ayuka namin yawa ne, ina sanku har cikin xuciyata.

  

A gurguje take aiyukanta dan taje taga mutunin da ya fara shiga cikin zuciyarta ba tare da tayi tunanin san wata halitta a gaba ɗaya dunuyarta ba, a wannan lokacin, sosai ta gyara kanta sai tayi kyau na musamman sabo da yanda tayi rama kaɗan, yau ma brown din jallabiya ta saka sannan ta yane kanta da dan kwalin jallabiyar, sosai kyanta ya fita na bugawa a jarida, motarta wadda Abdulwaheed yasa aka maidu mata jiya ta shiga, AC motar ta kunna kamshin sai ya haɗu da kalar turarukan Oud din da ta shafa ya bata wani ni'emantaccen kamshi da natsuwa, wakar binladin ta saka na badman tana tafiya tana jin wani nishadi na zagaya dukkan ilahirin ruhinta, daga gefe tayi parkin sannan ta fito cikin takon ƙasaitar da ka kalleta kaga mace mai izza da isa musamman yanayinta da yanda take tafiya cikin tsantsane da gamsuwa da cewa ita din mace ce mai aje da isa, bugun zuciyarshi ke ƙaruwa musamman yanda yaga ta dusu tana tafiya sosai ya ke jinta a sama da ƙasan zuciyarshi, ji tayi kamar ana kallanta daga kai tayi saman binan da yake jingine, idanuwansu ne suka sarƙe cikin na juna, murmushi suka aikama junansu a lokaci guda ba tare da kuwannensu ya ankara da yanda ya wurgama dan uwanshi kallan ƙauna, baisan yaushe ya kamu da shahararran santa ba har yake jin ita din wata ginshiƙi ce a gaba ɗaya duniyarshi kuma yana bukatarta a zaga yanshi.

    Ta aminci kuma ta gamsu bata da abinso a yanzo idan ba mutumin da take ƙarƙashin ikonshi ba, tayi imani zata watsar da makaman dasuka kawota kusa dashi dan bata tunanin zata iya cutar dashi dan shi ɗin bai cancanci haka ba a gaba ɗaya tunaninta, cutarshi yana nufin dana sani a gaba ɗaya duniyarta kuma tayi imani ba zata taɓa yafe ma kanta ba idan ta aikata wannan zunubin gareshi.

    A hankali take taka matakalar da zata sadata da inda yake tsaye ya harde hannuwanshi saman kirji idanuwa ya zuba mata yan san ƙara sarƙe idanuwansu a karo na biyu dan ya ƙara bata damar hangu kanta cikin idanuwanshi da dukkan kuzarinshi.

   Kanta a ƙasa take tafiya dan bata da bukatar kara gigin saka idanuwanta a cikin idanuwanshi mutumin da take jin sanshi na bugawa da dukkan wani bugu na zuciyarta.

    Wucewa zatayi amman babu isashshiyar hanyar da zata sada kanta  da cikin office ɗin, dole sai ta inda yake, tsayawa tayi sannn ta ɗago kanta cikin wani irin yanayi idanuwanta ta aza cikin nashi sannan ta juyasu da wani kalar salanta, idanuwanta yake kallo da dukkan wani kuzarinshi itace macen da yake su ta kasance cikin kulawarshi macen da bata shayin. Kallan tsakiyar idanuwanshi. Idanuwanshi ya lumshe sannan ya matsa gefe a hankali tawuce tana aje wani murmushi saman fuskarta.

   Kamshinta ya aje mashi wata kasala mai bukatar agaje, jingina yayi da jikin ƙarfen binan yana maida numfashi da jinyar kanshi na wani lokaci, murmushi saman fuskarshi sannan idanuwanshi rufe yana jin yanayinshi na canzawa.

     Da murmushi ta shiga office din idanuwanta ta aje samn tangameme potanshi wanda yake tare da iyalinshi idanuwanta ta aje asaman fuskar Adda Maryam wanda ta ƙwakumeshi kamar wani zai kwace mata, shi kuma ya aza mata kyakykyawan murmushi kamar daga ita babu wata da zata shigo duniyarshi, tsintar kanta tayi da jin haushi a ƙasan zuciyarta musamman yanda suka tabbata masoyan asali a cikin ƙatakon photan.

      Hucen numfashin shi take je a saman kafadarta turaranshi da ya tabbatar mata da cewa shine a bayanta, hannuwanshi yasa ya zagaye kugunta dai dai saitin kunnanta yace"Kin min kyau har na kasa bayyana maki irin yanda kika tafi da dukkan kuzari na"

     Hannunta ta dauka ta dura saman nashi ta haɗa ta danke sannan tayi magana ƙasa ƙasa kamar mai raɗa"Ngd da yabawarka a gareni, amman kasan kai din mai kyau ne feye dani"

KASAITAATTUN MATAWhere stories live. Discover now