02

3.9K 173 4
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*



0⃣2⃣


Karfe Uku daidai agogon dakin yabuga, lokachin ne yayi daidai da farkawar shukuriyya daga bacchi , Umma da abba nagani xaune akan kujera sai wani saurayi dake gefen gadon ah zaune wanda zai kai kaman shekara ashirin da biyu yana riqe da hannun shukuriyya, wasu yara na hango mache da namiji, machen tana kan godon itama wajen kafar shukuriyya ah zaune, yarinyache wadda bazata haura shekara takwas aduniya bah, namijin kuma yana kan wata kujerar roba dake gefah daya, shima shekarunsa baza sufi goma bah, kana ganinsu kasan yan uwan juna ne dan duk kamarsu daya, duk sunyi jugum kamar gidan mutuwa

Saurayin da yake rike da hannun shukuriyya wato mashkur, naga yayi saurin juyawa gurin da umma take yana chewa umma tafarka, dasauri suka taso sukayi kanta fuskokinsu chike da damuwa kowa da kalar tambayar da yake mata, murmushi tayi mushi ta miqe zaune da taimakon yayanta mashkur tane me yimusu murmushin karfin hali, Umma tasan halin'yar tata, tasan tayi hakan ne dan su rage damuwa aransu badan yafito daga zuchiyarta bah


Abinchi umma ta dauko dasuri ta zubawa shukuriyya yayinda mashkur yakarba yanabata abaki dakansa, balaifi tadan chi kadan sannan tasha magani, yanzu kam tanajin karfin jikinta hanif da hanifah wato kannenta sai surutu sukeyi mata musamman ma hanifah wadda takeda shegen surutun tsiya, tuntana jinsu tana sharewa har suka fara bata dariya, mashkur kam da abba ba karamin jin dadi suka yiba ganin tana dariya atunanisu tafara chire komai daga ranta, umma kuwa tasan'yarta chiki da waje tasan na dole takeyi dan batasan taga kowa achikin damuwa, amma dukda haka taji dadin ganinta ahaka koba komai tayi dariyar kuma mutumin dazaiyi dariya koda ache ta dole che akwai guntun farinchiki aransa, bayan dogon lokachi da aka dauka ahaka zuwa karfe biyar na yamma likita yabasu takardar sallama suka tafi dan taji karfin jikinta matuqa, kuma ga magungunanta nan zata chigaba dasha, saidai likita ya tabbatar musu dachewa zasu dawo bayan wata daya domin kara duba lafiyartata .


Bayan sun fita daga hospital dinne abba yawuche dasu wani gurin ice-cream dan yasan shukuriyya tanasan ice-cream din wajen yanasan farinchikin iyalansa, yanajinsu aransa, burinsa bai wauche sukasanche awannan yanayin bah koda yaushe, tunda shukuriyya taga annufi gurin aikuwa tafara murna harda tsokanar mashkur tache
"ya mashkur nikadai abba zai siyawa kuma bazan sammaka bah saboda haka karkasaka rai fah"
kowa dariya yakeyi har akaje aka siya aka wuche Gida, ai tunda aka dauki hanyar gida gaban shukuriyya yahau faduwa, tuni annurin fuskarta ya dauke jikinta har rawa yafara yi, suna isa gida kowa yazube ah falo itakam hankakinta duk ah tashe yake kowa yadauki nashi ice cream d'in yana sha, shukuriyya kam kadan tasha ta ajje tache ta koshi ( first tym in history ).


Umma kuwa kitchen ta wuche dan daura abinchin dare, anata hira sama-sama ah falo har maghribah tayi , abba, mashkur da hanif suka tafi masallachi, shukuriyya da hanifah kuwa dakin su suka wuche dan gabatarda tasu sallar, shukuriyya na nufar dakin gabanta yana faduwa, dannewa takeyi kawai take tafiya, tana shiga ta wuche bandaki tayi wanka sannan ta dauro alwala tafito, amma me? takasa zama ah dakin ballantana tayi sallah, tsoransa takeyi sosai, falo tafito tatayarda sallahrta awurin, Umma che tafito daga kitchen taga shukuriyya na sallah ah falo tsayawa tayi tana kallanta kawai, abunda bata taba gani bah Keenan, kodayake tasan dalili tasan za'a runa, girgiza kanta kawai tayi tawuche daki chike da damuwa fal aranta, itama zuwa tayi tagabatar da tata sallar .

Bayan sallar issha'i duka family din na zaune ah falo umma ta gabatar da abinchi, kowa yachi kadan dan basuda kuzarin da zasuchi abinchi da yawa, dukda chewar babu walwala afuskar yan gidan kuma basuchi abinchin dayawa bah amma umma taji dadin ganinsu ah hakan dan batayi tsammanin samun hakan bah mah, ana gama chin abinchi abba yayi kyaran murya yache
" mashur"
mashkur yache
"na'am abba"
Abba yache
"inaso gobe idan Allah ya kaimu ka kira mun kamal ah waya inason magana dashi"
yana gama fadar haka shukuriyya ta tashi tabar falon hanifah ma binta tayi abaya suka nufi dakinsu, ya mashkur ransa babu dadi shima yamiqe yanajin yar'uwarsa aransa, yanajin abunda yasameta, yana tausayamata, kowani motsi nashi karfin hali kawai yakeyi, amma zuchiyarsa achunkushe take babu dadi, dakinsa yanufah shima hanif yabishi ah baya, Umma che ta tsaya tana kallansu daya bayan daya suna fichewa daga falon har suka gama fita sannan tajuyo da dubanta zuwa ga abban nasu dake zaune akan kujera shima yana binsu da kallo, suna hada ido yamiqe shima yabar falon yanufi dakinshi .

"innalillahi wa inna'ilaihirrajiun!!" Shine kurum abunda umma take iya furtawa, sai yanzu tasamu damar yin kukan dayake maqale awuyanta, kuka takeyi sosai amma Mara sauti
"wannan wani tsinannene? Wani matsiyachi ne wannan? wani la'anannan Allah ne wannan? Wannan wani mara imani ne? Zaizo ya lalata mun gidana, gidan Dana dauki kimanin shekaru ashirin da uku ina gyarashi gidan dayake chikin farin chiki koda yaushe, Allah ka saka mana"

shine kurum take iya fada, tadade tana abu daya daga bisani ta miqe ta nufi dakinta, wankan tayi itama sannan tayi naful-fulinta tayi addu'ah sosai iya iyawarta ta shafa sannan ta miqe tanufi dakin shukuriyya...


Ta sameta ido biyu kamar yarda tayi tsammani, tana kwanche kan gado idanunta na kallan sama, daman tasan idan bah barawo bcci bah babu abunda zai kawo bacchi gidanta yau, ta kalli agogo karfe shadaya da rabi harda minti biyar, tasan daman zai yi wahala ache tayi barchi, zuwa tayi ta zauna kusa da ita ta tayarda ita zaune sannan tariqe hannunta
"shukuriyya"
takira sunanta ah hankali, shukuriyya ta dago runannun idanunta ta zuba wa mahaifiyarta ido
" shukuriyya kiyi hakuri, akwai Allah kuma zai saka miki, kiyi sallah ki roqeshi zai amsa miki, manzon Allah (S.A.W) mah yache kaji tsoran addu'ar Wanda aka zalinta, domin tsakaninsa da ubangijinsa babu shinge, inaso kidage da addu'ah kibar wannan dogon tunanin dan babu abunda zai saka miki sai damuwa, damuwa kuma matsala zata zame miki, matsalolin kuma saisuyi miki yawa, kiyi hakuri ki kwanta yanzu"
takara kura mata ido chikin kallan tsanaki da tausayawa tache
"Allah ya saka miki 'yata"

"nagode"
shine abunda kawai shukuriyya ta iya fada, umma ta zare hannunta daga nata sannan ta kwantar da ita akan gadon, tamata addu'ah ta tofah mata sannan ta matsa gadon hanifah dake sharar bacchi itama tamata addu'ar sannan ta tashi tafita ta rufo musu dakin .

Shukuriyya kam takasa barchi ita kanta sotake tayi barchin, tanaso tahuta amma tunani yamata yawa, tana tunanin hukunchin da kamal zai yanke akanta, tana tuna abunda yafaru da ita, da zarar ta rufe idonta abunda yafaru ne yake dawo mata, su take gani ah idonta, bataso mah tarufe idanun nata saboda yanda suke wulga mata, takasa barchi kwata kwata, daga karshe tashi tayi daga kwanchiyar da takeyi tayi alwala tafara naful-fuli kaman yanda ummanta tache .

WACHECHE SHUKURIYYA ?
WANE FAMILY NE WANNAN ?
MEYA FARU DA ITA ?

Ku kasanche da ni meerah dan jin wadannan amsoshin

Dis just d beginning😍

*MEERAH

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now