48

1.1K 79 5
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳



Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘






4⃣8⃣



Gaba d'aya hankalinta yatashi gameda maganan skul da mashkur yamata, she felt so sorry to him, itakam tahaqura da skul kwata-kwata, kuma batajin akwai dalilin daxaisa ta tursasa kanta yin hakan,,,,

Hakanan kwanaki sukayita tafiya, kullum mashkur yanata qoqarin fahimtar da shukuriyya amfanin yin karatu achikin rayuwarta amma taqi fahimtarsa, sosai yayi qoqarin nuna mata chewar bokon daxatayi shine kad'ai xesa rayuwar aurensu da haiydar d'in tayi dad'i dasu da yaransu, tunda dai shi haiydar ba karatun yayi bah, karsuxo su xama uwa kwanche 'ya kwanche,, kuma shi kasuwanchi wani lokachin ba tabbas nerh dashi bah,,
babu hujjoji da shawarwari da mashkur be bawa shukuriyya ba amma sam taqiji taqi gani, shi sam besan haka shukuriyya take da taurin kai bah ma sai wannan karan, saboda basu ta6a artabu da ita kaman haka bah, wani lokachin ma har nuna mata yakeyi yayi fushi da ita amma hakanan zataje tayita bashi haquri har ya haqura sannan ta kawo unnessary reasons d'inta,,,,

Wani lokachin sai yayita tunanin kodai haiydar nerh yake zugata, amma ahankali ya fahimchi chewan babu wanda yasaka mata ra'ayin hakan ah zuchiyarta, ra'ayin kanta nerh kawai ta Samar...

Hakanan yahaqura ya qyaleta na wannan lokachin, yabari chewan bayan tayi aure komai nata ya daidaita saiya kaimata maganar yaji idan zata yarda tayi karatun .....


                         🌳🌺😘

_A week to the wedding_

Ankawo lefen shukuriyya daka gidansu haiydar, saidai gidan kaka aka kai, domin umma chewa tayi kawai zasu zo KT sai su kar6i kayan anan, saboda su hutarda masu kawowa, idan yaso su saisu d'auka sukai KD d'in.....

   Maza nerh suka kawo lefen kuma maza nerh suka kar6a, lefen was poorly poor, kana gani kasan babu che tabayarda gudummawa gurin had'ashi, kana kallan kayan kasan wanda yahad'ashi yana ganin RAYUWA, atamfofin gasunan kalar babu, kana kallan colour da design d'insu ma kasan babu che,, hakanan suka kar6a mashkur yabada tukuichi me kauri wanda seya kusan siye kayan lefen, sukayi godiya suma suka tafi, akayi komai chikin mutunchi, bayan anshigar da kayan kowa se sambarka yakeyi, dukda sukansu mutanen qauyen sunsan ko yarinyar chikin qauyen ze aura tawuche wannan lefen, bare kuma y'ar birni, hakan yasa suke ganin kaman kyautar shukuriyya kawai aka bashi, haka kowa yagama kalla da yamma su umma suka zuba kaya amota suka taho KD....

  itakuwa shukuriyya duk ranar kusan wuni sukayi suna waya da haiydar, kafin bayan dawowar su umma suka saurara,,, haka tafito ta kalli lefenta yayinda mashkur yake nuna mata, ita sam bataga aibun lefen ba, saima qara jinjinawa haiydar datakeyi nayin wannan lefe dayayi, dan sosai kayan suka zarche arzikinsa, shima mashkur yabiye mata kawai suna yaba kayan, azuchiyarshi kuwa yana mamakin irin san da shukuriyya takewa haiydar, ahaka suka gama ganin kayan aka rufesu aka kaisu dakin umma, kowa yana sanbarka, banda hanifah datake ganin dama ita aka ba kayan, ita atunaninta kayan wasu duniya nerh (lol)

    Bayan shukuriyya takoma daki haka takira haiydar awaya tanata nuna mishi kyan kayan da qoqarinshi akai, shikuma sai fasa mishi kai takeyi yana dariya har sukayiwa juna sallama....


                          🌳🌺😘

Gidansu shukuriyya shiri sukeyi gdan-gadan kaman wannan shine aurenta na farko, yanda akeyin komai ma baxaka ta6a tunanin ta ta6a yin aure bah, umma tabayarda manyan kud'i ayiwa shukuriyya humra da turaren wuta masu zafi na amare, ga kullum shiryata datake qarayi, halawa kam da dilka na gyaran jiki tun jiya suka farayi, wata mata ke zuwa hargida ta mata, daman ita ba fita takeyi ba bare ache wani wurin xe kod'e, sosai umma ke gyara yarinyar tata babu sanya, itakuwa shukuriyya komai sukeyi saidai ta bisu da ido, babu um babu um'um....

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now