🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳
Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘
🌳🌺😘
_wannan shafin nakune gaba d'ayanshi @ *hadeeza mukhtar, Ummu hayat, Sa'adatu j, Maman sudais nd fannah,,,* from cuttiee novels group2, ur lurv and encouragement is what keeps me blowing, ina sanku sosai fiyeda yanda kuke sona, trust me,,,, 😃 Allah yabar zumunchi, ya d'aukaka rayuwanku fiyeda yanxu, yabaku tsawan rai mai amfani,,,, amen_
_*I lurv u*_ 💖
4⃣4⃣
Da safe haiydar yana tashi ah bacchi yaje ya kintsa kanshi sannan yaje ya sami inna ah daka sukayi maganar aurenshi, sosai suka zanta da ita gameda yanda xasu 6ullowa al'amarin, kuma sungama tattaunawarsu kan komi baxai gagara ba da yardar Allah,,,suna chikin tattaunawarsu malam yashigo chikin gidan, daka gidan mai gari yake, zama yayi shima aka somayin hirar dashi, sun yanke hukunchin xa'a gyara dakin haiydar dake chikin gidan sannan sai yakuma gina daki akusa da wurin, sai yayi mata rumfar kitchen idan yaso sai akewayemata wurinta yaxama and'an yi katanga tsakaninta da wurin sirikannata,,,,
haiydar yaji dad'in lissafin da inna tayi domin yasan ginin baxe mishi wahala ba tunda daki dayane zai gina, nashi kawai gyarawa xa'ayi, kuma qarin dad'in shine ya iya gini saboda haka abokanshi kawai zai kira su had'u su gina tare, kuma block baxe mishi wahala ba, saboda yasan da zarar yabawa almajiran malam abun sadaka yasan zasuje babban rami sushiga suhad'a mishi block achiki, idan ya bushe sai su d'ebo sukawo mishi shikuma sai yaxo da abokanshi su gina, so yasan chewar wannan baxe chi mishi kud'i bah,,,,,
Maganan sadaki kuwa tunda dad'ewa daman yasan chewar mai gari yayi mishi alqawarin sadaki, don maigari dabakinshi yafurta chewar duk ranarda auren shi yatashi to shine zai biya sadakin shi, sannan har wasiya ya bayar chewar koda ya mutu kafin auren haiydar to lallai kafin araba gadanshi achirewa haiydar sadakinshi abashi ya ajje, idan yaso duk sanda yatashi yin aure sai yabiya da kud'in, wannan dalilin yasa haiydar bashida wata fargaba ta fannin sadaki, abu d'ayane yake d'aga mishi hankali shine lefe, wanda duk sanda yatuna saiyayi lefe gabanshi har mummunar fad'uwa yakeyi amma ahakan yayi alqawarin zeyi mata komi daidai qarfinshi,,,,,
Tohhhh!! Bayan sungama shawarwarinsu na chikin gida sukayi concluding chewan zasuje nema mishi aure kamar yarda addinin Allah ya tsara, malam yache zaije yasamu mai gari yagaya mishi maganan, idan yaso saisu d'unguma tareda mutanen fada aje anemo mishi aure, dan haiydar d'ane ga kowa tunda dai maigari ya tsaya mishi a matsayin uba,,
dahaka suka yanke magana malam yafiche daka gidan yakoma wurin mai gari, yayinda shikuma haiydar yasa kai yafiche yatafi neman kud'inshi, yanajin malam da inna har chikin zuchiyarshi, kullum qaunarsu qara yawaita yakeyi achikin zuchiyarshi, bashida wani burin daya wuche yagansu chikin farinchiki, kullum burinshi be wuche yasasu chikin jin dad'i bah, saidai gashi haryanxu rayuwa taqi bashi damar yin hakan, gashi kullum lokachi tafiya yakeyi, amma ahakan be fitarda rai bah, yana saka ran wataran jin dad'in zezo kuma zai jiyar dasuu.....
Da yamma liqis gabannin maghriba haiydar yaje gidansu shukuriyya, tafito kamar kullum chikin fara'a taje suka gaisa sannan agurguje ya sanar da ita chewar iyayenshi zasuje wurin iyayenta ayi maganar aurensu, ba qaramun dad'i maganar tayimata bah hartake ganin albishir d'in yana chikin records d'in dayakamata ache ta ajje, sosai tayi farinchiki da maganan har yakasa 6oyuwa, hakan ba qaramun dad'i yayiwa haiydar ba danshi bashida burin dayawuche yaga shukuriyya chikin farinchiki, da haka sukayi sallama ya wuche gida abunshi.....
Bayan sallar isha shukuriyya na zaune atsakar gida suna hira da kaka, sotakeyi tafad'i mata maganar amma sam takasa, da qyar ta tattara nutsuwanta ta ajje kunya agefe ta fad'awa kaka maganar haiydar d'in, tsaban jin dad'i kaka yi tayi kamar ta taka rawa awurin, wayarta ta miqawa shukuriyya tache ta kira mata babanta achikin layin, babu musu shukuriyya ta kar6a takira abba, yayita ringing amma ba'a d'aga ba har ya katse, sai bayan ya katse sannan abba ya kira layin kakar, yana kira shukuriyya ta danna wurin answer sannan ta miqawa kaka tasaka wayar akunnenta, gaisawa sukayi chikin girma da arziqi irinna uwa da d'a sannan kaka tafad'i mishi qudirin masu neman auren shukuriyya d'in, shima abba yaji dad'in zanchen sai kawai yache Allah ya kawosu lafiya ahaka harsukayi sallama, shukuriyya murna fal chiki tayi d'aki abunta bayan tagama jin hirar babannata dakuma kaka......