69

1.1K 65 9
                                    

🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳



written by 🌺 CUTTIEEMEERAH



6⃣9⃣

                       🌳🌺😘

    KANO

    
           Ko bayan sun dawo Kano katafaren liyafa abuu ya had'a musu ah the avenue dake opposite Daula hotel, sosai partyn ya qawatu domin an kashe kud'i sosai, mafi yawan mutanen dasuka halarta wurin families dinsune, saikuma kad'an daga chikin skul frnds dinsu wanda daman su ah Kano suke da zama, ansha pictures na tarihi awurin sosai sannan suka had'u dukansu akayi snapping nasu achikin picture d'aya, gaba d'aya familyn suna chiki banda nene wadda ko wurin event din bata je ba ballantana tashiga chikin picture d'in, babu yanda abiii beyi da ita kan tajeba amma ta che mishi ita baxataje bah, har hatsaniya nerh yaso yashiga tsakaninsu akan batun, saida abuu yamishi magana yache ya qyaleta kawai sannan yafita harkarta, sosai ta qona mishi rai akan abunda tayi, dan ko lokachin dasukayi events d'insu ah Abuja itache tache bazatajeba shiyasa shima yaqi zuwa, yayi hakanne dan yasan chewar matuqar yaje shikad'ai yaran zasu fahimchi chewar taqi zuwane, shikuma bayaso suchigaba da qinta azuchiyarsu shiyasa yaqi zuwa shima saboda suyi tunanin wani uzurinne ya riqesu, duk yayi hakanne dan ya rufa mata asiri ya kuma kwantar musu da hankali, domin yasan dole yaranta sunajin zafin abunda takemusu, kawai dai suna nunawa nerh afili kamar basu damuba amma yasan dole abun yana damunsu, gashi wannan karanma tache bazatajeba, yana sane ya shareta yayi tafiyarsa domin ya fahimchi idan yachigaba da bin yanda takeso to lallai yaranshi shima zasu fita harkarshi kaman yanda suka fita harkar mahaifiyar tasu......

                🌳🌺😘

 

A week after their party

          Duka yaran suna L&Z suna having lunch a wurin, yau kwanansu biyar kullum chan suke zuwa suyi lunch d'insu sannan sukoma gida, da daddare kuma wani chikin yayunsu saiyaje chicken castle yasiyomusu wani abun daza suchi, da safe dama kullum masu aikinsu ke musu breakfast, basasan chin abinchin masu aikin nasu shiyasa ma suke fita chin na rana ah waje, da yake ummi, abuu, abiii da goggo sun tafi umara two days bayan partyn su, itakuma Nene daman bawai tanayin girki bane bah, kuma koda ache zata dafa musu ko sunyi hauka bachi zasuyi bah, dan duka yaranta sunyi alqawarin chewar bazasu ta6a chin duk wani abu dazai fito ta hannunta bah, dan gani sukeyi rashin imaninta yakai tazuba musu guba suchi su mutu,,,,

      Suna gama chin abinchin suka fito suka shiga family bus d'insu driver yajasu suka d'auka hanyar gida....

     Tunda suka shigo layin nasu suka hango wani mutumi ah tsaye ah qofar gidansu, saida suka qaraso daf dashi sannan suka lura tsoho nerh domin ga furfura nan ah fuskarsa da kansa gaba d'aya, yana ganin motarsu ta doso gate d'in yayi sauri yamiqe yashige  gaban gate d'in ya tsaya yana musu alama da hannu su tsaya, kallan kallo dukansu sukayiwa junansu sannan suka juyarda kallansu ga wannan mutumin dake tsaye, kafinma waninsu yache komai gate man yabud'e gate d'in sakamakon horn da driver yake ta mishi, ana bud'e qofar yayiwa mutumin alama da hannu chewar ya matsa, ganin chewar mutumin bashida niyyar matsawa yasa ya finchiki motar yayi kamar zebi takanshi, sai mutumin yayi sauri yabar wurin sannan drivern yasaka motar chikin gidan, daman yasan dazarar yamishi haka dole ya matsa, qoqarin biyosu yakeyi chikin gidan amma gateman yadakatar dashi sannan yayi sauri ya rufe gate d'in, komawa yayi ya zauna ah wurin yazuba uban tagumi hawaye na zubo mishi daga chikin idanunshi....

   Achiki kuwa d'aya bayan d'aya suka fito daga chikin motar, kafin kowa yache komai usiii ya kira gate man da hannushi alamar yazo, yana zuwa yamusu sannu da zuwa sannan usiii yache

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now