71

1K 108 14
                                    

🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳


Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH



7⃣1⃣

                     🌳🌺😘

         Gaba d'aya mutanen gidan suna zaune akan dining table dake side d'in goggo sunachin abinchi, su zarah sai surutun yaushe gamo sukewa parents d'innasu yayinda sukechin abinchin, jefi jefi abiii yake ansasu, hirar tasu tafi yawa da goggo da abuu, Itakuwa ummi tana zaune neeh kawai akan kujerar riqeda spoon ah hannunta, takasayin koda spoon d'aya nerh ballantana ta tankawa hirar tasu, gaba d'aya she's not in the mood, gashi duk bayan wasu seconds saitaji zuchiyanta na harbawa, abuu ya lurada yanayinta amma ya fuske be tanka bah, sukuwa su sadiiq sunzata fushin tafiyarsu nerh yasa duk take 6ata ranta, hakan yasa suma sukayi  shiru awurin basuche komai bah, wurinne yayi  shiru for some minutes kafin ummi tache

    "Ina kukaje?"

Qarfin hali kawai tayi tamusu magana saboda taji babu wanda ya tambayesu, wanda tasan dole yakamata ache an tambayesu, idanma da hukunchi ah hukuntasu, domin basuda dalilin dazaisa sufita subar gida harna tsawan wasu kwanaki batareda sun fad'awa kowa komai bah, ah zuchiyarta ma tausayin yaranta takeji, ta inda ta qara godewa Allah ma shine yanda Allah yabata tsahon rai dahar suka rayu da ita har wannan lokachin, dabadan haka ba batasan wache iriyar rayuwa yaran nata zasuyibah, batasan dawata iriyar tarbiya zasu taso bah, hakan yasa suke bata tausayi, amma idan ta tuna chewar yanzu sun girma saitaji wani 6angare na zuchiyarta ya kwanta...

   "Ummi!!! Ba abuu nerh yache muje Abuja muyi hutu bah"
Zarah ta ansata da mamakin tambayar data musu

Abuu nerh yabud'e idanshi waje yana ajje spoon din dake hannunshi

    "When?"
Ya tambayi zarah yana kallanta

Wara hannuwanta tayi alamar bata sani ba sannan ta maida kallanta kan brothers d'inta, ganin babu wanda yache komai yasa biily tache

     "Abuu muma bamu sani bah, kawai wanchan ranar sadiiq yache muhad'a kayanmu ah trolley zamu tafi Abuja, kuma yache kaine kache muje"

Shiru wurin yayi yayinda sadiiq yayi zuru da idanunshi, ko kallan abuu yaqiyi saboda tsoran abunda zeje yadawo, yasan dole sai ummi ta hukuntashi dan ta tsani suyi qarya, usiii ganin kowa yaqi magana yasa yache

     "Abuu...... "

Komai daya faru wanchan ranar ya kwashe ya fad'a musu, harma da baqon dayazo chikin gidan, sosai abuu da abiii sukayi musu dariya, ita kanta ummi saidata yi dariya  kad'an, dukda chewar she's not in the mood, Nene kuwa da haushin labarin nasu yagama tirniqeta tashi tayi ta musu tsaki sannan tabar table d'in, she just hate stupidity, ko kallanta ma basuyi ba suka chigaba da maganar su

     "Wannan be kai dalilin dazaisa kubar gida ba sadiiq, bakuda dalilin barin gida batareda kun sanar damu bah, in fact abunda kuka aikata is more of risk than abunda kuka bari agidan, u guys have to take care, kar inqarajin irin haka ya faru,, OK!!!"
Chewan ummi

    "OK ummi, we are sorry"
Duka yaran suka had'a baki suka fad'a

     "It's owk"
Ummi tafad'a tana murmushi

     "Mutumin yana ina yanxu?"
Abuu ya tambaya yana kallan sadiiq

    "I don't know actually, tun ranar da muka bar gidan ban qara jin labarinshi bah"
Sadiiq ya ansashi

Usiii nerh yayi karaf yache

     "Yana boys quarters abuu, kullum muna waya da fa'iza tachemun yananan lafiya, kuma kullum saiya tambayeta ranar dazaku dawo"

     "It's owk, zan ganshi gobe InshaAllah"
Abuu ya ansa yana miqewa daga table d'in, dan sosai yakejin gajiya ajikinshi, lokachi d'aya kowa ya miqe daga table d'in suka bar parlourn

*At night*

   
        Ummi takasa bacchi kwata-kwata, tun wurin 11 na dare take nafulfuli har zuwa yanxu da yake 3am, zuwa yanxu taji zuchiyanta yayi mata sanyi bakamar da chan da zuchiyarta taketa harbawa bah, lallai babu makamin daya wuche addu'ah....

      Tana idarda sallar taqara addu'ah sosai sannan ta tashi takoma kan kujera ta zauna, dukda gajiyar dake jikinta amma batajin bacchi ko kad'an, duk kwanakin nan tana tuna haiydar nerh sosai achikin zuchiyarta, tana tunashi nerh like never before, tun yana 4year's daya bar gidan bata ta6a jinshi sosai achikin zuchiyarta kamar yanzu bah, ji takeyi ajikinta kamar yana kusada ita, duk sanda ta tunashi nerh ma takejin gaban nata yana fad'uwa, abun ya dameta sosai saidai takasa fad'awa kowa hakan, sai abuu kawai wanda shima bugawar da zuchiyarta takeyi kawai tafada mishi, amma bata sanar dashi zanchen haiydar bah.....

     Hawaye neh suke zubo mata sosai ah idanunta, tausayin halin dayake chiki kad'ai ma ya isheta, iya rayuwar datayi bayan 6atanshi take addu'ar Allah ya baiyana shi, gashi har yau shiru babu labarinshi,,,,,

       abuu nerh ya turo qofar d'akin ummi ya hango ta akan kujera tanata zubar hawaye, daman yasan chewar dole batayi bacchi bah, jikinshi nerh yabashi hakan shiyasa yazo ya dubata, qarasowa yayi ya zauna agefen gado sannan ya kalleta

     "Ummi menene matsalar, hawayen na menene?"
Da damuwa yayi mata tambayar

     "Haiydar!! kibdiyya!!"
Abunda ta furta kenan kawai tayi Shiru

    Shikanshi abuu Shiru yayi beqara chewa komai bah, daqyar dai ya numfasa yache

      "Kiyi haquri ummi"

      "Nayi haquri sosai abuu, nayi haqurin da banta6a tunanin zan iyayin makamanchinshi bah, amma zuwa yanxu zuchiyata ta raunana, nakasa chigaba da abunda nayi abaya, ina tsoran inkasa chin jarabawar da ubangiji yamun"
Taqarasa maganar tana zubarda hawaye sosai

     "Karkiche haka ummi, kiyi haquri dan Allah, Ki qara akan wanda kikayi, inshaAllah ubangiji yana tareda ke, kuma inshaAllah kinchi jarabawar kin gama"

     "Wannan innocent yaran me abun dariya, me qawazuchin iyayenshi, me suffar muminai, kyakkyawa mesaurin d'aukar karatu, ya 6ache shekara da shekaru, babu shi babu labarinshi, tun ana saka rai har an fidda rai, wannan abun tausayi dame yayi kama"
Kuka ummi takeyi sosai yayinda take furta wannan maganar

   
       "Yarinyata ah hannun 'yan fashi, wayasan irin rayuwar da take chiki, yarinyar dako shayar da ita ba'a gama bah, ah hannunsu zata rayu, da tarbiyar su zata taso nasan dole,,, qila ma bazanso qara ganinta bah idan naganta, dan nasan dole da halin mariqanta zata taso, wayasani ma ko sun kasheta, mutanenda babu imani babu Allah ah zuchiyoyin......"

Kuka nerh me qarfi ya sarqafe mata wnda har takasa qarasa maganarta, chikin hikima da dabara abuu yake lallashinta, daman chan haka take da yawaita zanchen yaransu, amma it has been a while dabatayi maganarsu kamar yanzu bah, kuma ta dad'e batayi kuka akansu kamar na yau bah....

     "Kiyi haquri ummi, inshaAllah zasu bayyana, zamu gansu daransu da lafiyarsu, dakuma ingantacchiyar tarbiya"

    "Haka nake fata nima, saidai Ina tsoran zan mutu ban gana da yarinyata bah, ina tsoran zan mutu banqara jin d'umin haiydar ajikina bah, inaji ajikina bazan qara ganinsu ba har abada, naji ajikina mutuwa zanyi, mutuwa zanyi abuu, mutuwa zanyi, nagama jin hakan ajikina....

     " idan Allah ya baka tsahon rai ka gana dasu kasanar dasu ina sansu, kafad'a musu ina qaunarsu, nafi sansu fiyeda komai aduniya, kasanar dasu haka dan Allah "

Chikin kuka take maganar

      "Ummi dan Allah kiyi Shiru,babu wata mutuwa dazakiyi, kiyi haquri dan Allah"

Kalamai masu kwantar da hankali abuu yachigaba da fad'awa ummi harta haqura tayi Shiru, daqyar ta yarda ta kwanta dukda ba bacchin ma zatayi bah sannan abuu yafiche daga d'akin yana me tausaya mata....

Ummi baiwar Allah, please ummi don't leave us


Vote
Comments
Share and share your views









MEERAH

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now