11

1.7K 97 6
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳


Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH* 😘



1⃣1⃣

                

Wata biyu da auransu babu abunda ya ragu sai ma abunda yaqaru, domin shukuriyya ko hira bata zama suyi, tskaninta dashi shine idan sun hadu awajen chin abinchi, dan ko zama batayi ah falo, idan ma yaje dakinta ba wata magana takeyi masa bah, amma duk da haka yanayi mata uzuri, yana ganin akwai yarinta sosai akanta, dan haka betaba fushi da ita ba, wani lokachin mah dariya take bashi idan tayi wani abun nata .

                    
ranar wata talata shukuriyya tana daki azaune abunta tana sana'ar ta wato tagumi da tunani, kamal kuwa yana kitchen yana faman dafa musu fried rice, ga miet pie daya tsiri yayi wai yana sha'awa, aikuwa yayi kacha kacha da kitchen din, duk yabata kwanukan dasuke chiki, gashi jikinsa duk ya bachi da flour, hakanan yahada abinchin ya ajje kan dining table, ya koma kitchen din yawanke kwanukan daya bata, sannan yafara hada meat pie din, yafara gasawa kenan yaji ana knocking kofar falo, dasauri yafita daga kitchen hade da tambayar "waye?" akache "niche", jin muryar mache ne yasashi qarasawa da sauri ya bude, gaba daya mah yamanta daga kitchen yake, yana bude kofar yaga umman shukuriyya, bude baki yayi yana murmushi hade dayi mata sannu dazuwa, ita kuwa mamaki ne ya isheta, kallansa takeyi daga sama har qasa hade da amsa gaisuwarsa sama-sama, ganin kallan da take masa ne yayi yawa yasashi kallan jikinsa, sai yanzu mah ya tuna da yarda yake, asanyaye yadago idanunsa yana kallanta kamar Wanda aka zarewa laka,
    " Kamal!!!"
umma takira sunanshi
     "na'am umma"
kamal yabata ansa
"kokawa kakeyi da buhun fulawa nerh?"
ai kafin yabata amsa sukaji qauri daga kitchen, dagudu Kamal yakoma kitchen din, yamanta yana gasa Abu, dasuri yaje yakashe yadawo parlourn, yashigo yana murmushi yache
"wlh umma namanta na daura Abu ne shine yafara qonewa,, bara nakira shukuriyya batasan kin shigo bah"
yafada hade da wuchewa dakin shukuriyya, yana shiga yache kizo ga umma tazo, ita kanta saida gabanta yafadi, batasan zatazo bah, "nashiga uku" tafada hade dah dafe qirjinta, jiki asanyaye ta tashi ta fita parlour .

                 🌳🌺😘

shikuwa kamal yana fadamata yajuya ya koma parlour, yaje yazauna ah qasa umma na zaune kan kujera suna ta gaisawa irin tasu ta sirikai, ita kuwa umma gaba daya jikinta yayi sanyi, tunane-tunane barkatai kawai takeyi aranta, toh shukuriyya ta chanja halinta ne da har zata asirche Kamal yazama bawanta yakeyi mata girki?? kokuwa sabani suka samu yakeyin abinchin dazaichin dakansa??
tunane tunane takeyi sosai aranta yayin da suke gaisawa da Kamal, chan saiga shukuriyya ta fito jiki asanyaye, tana fitowa kamal ya tashi yabar falon, dakinshi yatafi yafada toilet dan yayi wanka, shukuriyya tana qarasawa parlourn da gudunta da dariya fal aranta tafada kan umma tana mata sannu dazuwa, umma kuwa binta kawai takeyi da kallo ta amsa mata, shukuriyya tache
"umma gaskiya nayi fushi wlh shine sai yau zakizo?"
umma tadan tureta da wasa tache
" kajimun fitsararriyar yarinya nikike fadawa haka"
gaba daya sukayi dariya sannan suka gaisa sosai, tanata tambayar kannenta da kuma yayanta mashkur umma tache
"mashkur dinne mah yakawoni"
shukuriyya ta bata rai tache
"Shine be shigo ba umma kika barshi ya tafi koh? "
umma tache
"yache bazai shigo bah zan tilasta masa saiya shigo ne"
aikuwa taqara bata rai, umma tache
" wasa nakeyi miki yache zai shigo amma sai yazo daukana"
sai sannan tadan saki ranta tana tayiwa umma surutun yaushe gamo itama umma sai tayata takeyi tana dariya .

               🌳🌺😘

chan saiga kamal ya fito da shirinsa na fita, yadan durqusa yache
" umma bara naje na dawo"
umma tache
"To Kamal adawo lafiya"
yache " Allah yasa"
sannan yatashi yabar falon, umma tajuyo takalli shukuriyya tache
" haka kike tarbar baqin naki idan sunzo ko ruwan sha babu, kokuwa saisun roqa kike basu?"
wannan karan tana magana ne fuskarta adaure, babu alamun dariya sabanin dazu, aikuwa shukuriyya tasha jinin jikinta, miqewa tayi takawo mata ruwa da lemo tadawo, umma ta tsiyayi ruwan tasha sannan ta dago ido takalleta tache
" daman haka kikewa mijin naki idan zai fita kibishi da wadannan kwala-kwalan idanun naki, babu adawo lafiya babu wata addu'ah?"
shukuriyya dai datasan batada gaskiya bata qara chewa komai bah
"Ba magana nakeyi miki bah"
wata razananniyar tsawa umma ta dakamata sai da hanjin chikinta suka kad'a, zata iya chewa tunda take umma bata taba yimata wannan tsawar bah, dasauri ta kada kanta tache
"ah ah"
umma tache
" qarya namiki kenan?"
nanma tache
"ah ah,,, yaune kawai fah banche masa bah"

( ni meerah nache su shukuriyya anfara qarya kenan )

umma tache
"meyasa?"
shukuriyya tache
"babu komai"
umma tache
"yayi kyau, kin kyauta, me kika dafa agidan naki?"
ae sai idan shukuriyya yaqara fitowa waje, itada ko ruwan shayi bata taba dafawa bah
"" amm.. umm.. earhm.. amm ...."
Kame kame tafarayi, kana ganinta kaga mara gaskiya, gashi bawani iya qarya tayi bah saita rasa meza tache umma ta miqe tanufi dinning dinsu, flaskses tagani, tana bude daya taga fried rice, dayan kuma farfesun kaji ne ga kuma juice na kankana akan table din, rufe flask din tayi sannan tawuche kitchen, zuwa tayi ta Tarar da meatpie din dayayi Wanda yafara qonewa shukuriyya kuwa na biye da ita abaya tajuya takalleta tache
"Tarbiyar da nayi miki kenan shukuriyya? mijinki shiyakeyi miki girki?"
chikin tsawa take maganar ai kawai saiga hawaye ah idanun umma
" yaushe kika zama haka? haka kikaga inayi? mekika maida kanki? tarbiyyar danayi miki kenan? Mekika dauki aure?"
hawayen baqin chiki ne yake xuba ah idanun umma yayin da take wannan maganar, fita tayi tabar kitchen din ta koma falo ta zauna...
tarasa mah mexatache mata, shukuriyya kuwa duk hankalin ta yariga yagama tashi, itama kukan takeyi tana bawa umman tata haquri, sai chan umma ta nisah chikin sanyin murya tache
"Sabani kuka samu da Kamal dinne?"
"ah ah"
shukuriyya ta ansata
"bakida lafiya ne yake miki girki?"
Nan mah "ah ah" shukuriyya taqara bata ansa
Umma taqara chewa "kekika che yayi miki qirkin?"
"ah ah" nan mah taqara chewa
chikin tsawa umma tache
"dan ubanki ki bude baki kimun magana banche ki dunga kadamun kanki bah, kokuwa sa'ar kicheni daxan dunga tambayar ki kina chemun eh ah'ah,"
gaba daya shukuriyya ta gama rikichewa, umma tachigaba da chewa
" mekike tsammani idan ache sirikarki che tazo yanzu bani bah? tazo ta tararda danta yana yimiki girki, mekike tsammanin zai biyo baya, kokuma ache wasu yan uwannashi ne sukazo, kina tunanin zasu zuba miki ido ki dunga wahalar musu da dansu, toh barikiji infadamiki konida bani na haifeshi bah bazan bari ki wahalar dashi bah bare in bari ki wulaqantashi, sam baze yiwu bah, idan bakya sansa shikenan sai ah raba auran, bazai yuwu kidunga chutar dashi bah, gashinan duk ya rame, daka ganinsa baya chikin kwanchiyar hankali, kekuwa gashi sai qiba kikeyi abunki, to bazan lamunta bah, dan haka tunda kinqi magantuwa nizan san abunyi, zanje nasamu mahaifinki ayi komai ah gama"
chikin bachin rai umma take wannan maganar, shukuriyya kuwa kuka takeyi sosai, umma ta tashi chikin zafin nama zata tafi sai shukuriyya ta riqe qafarta chikin shassheqar majina take magana
" dan Allah umma kiyi mun rai, karki fadawa abba, karku rabani dashi, wlh inasanshi"
kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita yayinda take wannan maganar, sai sannan umma tazauna ta kalleta sosai tache
"Shikenan, amma kiyimun bayani dan nakasa fahimtar komai, meyasa Kamal zai dunga maki qirki? kema gakinan kowa yaganki yasan bakya chikin kwanchiyar hankali dukda qibar dakikai, duk duniya bakida Wanda zaki fadawa matsalarki idan baniba dan haka ina saura ranki, kifadamun meyake faruwa"
shukuriyya tayi ajiyar zuchiya tache , daman ...........

Ta kwashe komai tafada mata, tundaga zuwanta gidan da kuma abunda Kamal yake mata har zuwa yau.            
umma tayi salati ta Sanar da ubangiji, tache
"Meyayi miki zafi shukuriyya? Ina ganinki kamar me hankali ashe bakida shi, idan wanine yafadamun yaushe zan yarda"
umma tayi Shiru tana kallanta sannan tache
" meye dalilinki shukuriyya ?"

                   🌳🌺😘

IG.      @ cuttieemaria

MEERAH
              

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now