🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳
Written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*
2⃣7⃣
🌳🌺😘
Washegari
Sosai maganganun shukuriyya sukeyiwa haiydar yawo ah kunne, haryau ya kasa daina mamakin batun aurenta datayi mishi, da tunanin maganar ya tashi daga bacchi, saboda haka sai yau d'in yakasanche komai nashi ah takure yakeyinshi, zuwa yanzu shida kanshi yafahimchi kishi kawai yakeyi, kishin wanda ya auremashi matarshi, haushinshi ya faraji dukda bai sanshi bah, amma saiyaga yayi mashi shigo-shigo ba zurfi, awani bangare na zuchiyarshi kuma idan ya tuna chewar ya mutune sai yaji tausayin mijin nata da kuma tausayinta duk ya rufeshi, da wannan alhinin ya wuni yau batareda ya fita ko soron gidansu bah, ko sallah mah achikin gida yakeyi, dan sosai yakejin zafi achikin zuchiyarshi, kuma yasan ba lallai idan yafita ya iya controlling zuchiyar tashi bah, dan haka mah yayi zamanshi agida harzuwa dare yayi kwanchiyarshi, da tunanin shukuriyya fal ah ranshi....
Itama shukuriyya d'in yau bata kasanche mata rana me dad'i bah, saboda chiwon kai d'in har yanxu yananan, kuma kukan datayine da kuma rashin barchin dabata samu bah, kakache ta juyo ta kalleta lokachin data saka abinchin karin kumallo ah gabanta, wanda yayi ah qallah awa d'aya amma bata ta6a shi bah, kuma da alama batada niyyar chi
"Shin baxakichi abinchin bane bah yau?"
Kaka ta tambayaShiru shukuriyya tayi batareda tache komai bah, saima hawayen daya fara gangarowa ah idanunta
"Laa'ila ha'illallahu, muhammadur rasulillahi, sallallahu alaihi wassallam"
Kaka tafad'a tana tafa hannayenta
"Oh ni maryama!! ina zan saka kaina da wannan shagwa6a66iyar yarinya, ache babu dama ayi miki magana sai kuka, shin daga kanki aka farayiwa mutum mutuwa nerh, bakanki Farau bah fah, kuma ba kanki qarau bah, me kukan naki zai anfaneshi dashi, shin baxakiyi mishi addu'ar dachewa bah, mumafah nan duk ita muke jira"
Kaka tafad'a tana nuna shukuriyya da d'an yatsa, tafad'i hakanne saboda tasan mafi yawanchin kukan shukuriyya tanayinshine idan ta tuno margayin mijinta
Madadin shukuriyya tayi Shiru saita qara fashewa da wani kukan, kaka che ta qarasa inda take sannan ta janyota jikinta da nufin lallashi, ji tayi jikinnata zafi rauu, dagowa kaka tayi ta kalleta sannan ta dago habarta tache
"Shin kinji irin yarda kika sakawa jikinki zazza6i kuwa, ashe duk bakin danake baki baxaki haqura bah, haba takwara tah.....
Lallashinta kaka ta dunga yi danufin tayi shiru, sai data jima tana kukan sannan tayi shirun, amma saidai zazza6in yananan"Kichi abinchin toh"
Kaka ta fad'a tana janyo mata kwanan abinchin gabantaTure abinchin tayi da hannu, nufinta baxatachi bah kenan
"Baki da lafiya nerh?"
Kaka tafad'a tana dubanta da kulawa"Qirjina nerh yake mun chiwo"
Shukuriyya tafad'a tana dafe wurin da hannunta hade da rintse idanunta, saboda yanda taji wurin yana mata zugi, kwallah tana zubo mata kuma at thesame time.."Ohh ni y'annan, anya ba ulcer che dake bah kuwa, amma ache bakida wani chiwo kullum sai chiwon qirji, kiramun yayan naki yaxo yakaiki asibiti, wannan chiwon qirjin nafara gajiya dashi"
Kaka tafad'a tana miqawa shukuriyya wayarta dake hannunta"Ki kyaleshi kaka, akwai magunguna nah ah daki idan nasamu nachi abinchi xansha, xanji sauqi inshaAllah"
Taqarashe maganar hawaye na zubo mata"Sam baxe yiwu bah, kallai fah yanda kika wani zuge lokachi daya sai kache wata bishiyar zogalai"