🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳
written by 🌺 *CUTTIEEMEERAH*
0⃣3⃣
Alhaji Ibrahim shine asalin sunan Abba wato mahaifin su mashkur, shi dan asalin garin katsina ne, yazauna tareda mahaifansa, malam aminu shine sunan mahaifinsa sai mahaifiyarsa mai suna maryam, ya taso ah qarqashisu ah garin katsina, shikadai ne d'a daya tilo agurinsu, yayi karatun allo kuma yana zuwa primary ah wanchan lokachin, tun yana yaro yakeda san neman na kansa, yanasan iyayensa, yana san farinchikin su, lokachin daya fara tasawa ne wani alhaji maqochinsu mutumin kirki yafara tafiya dashi chikin garin Kaduna dan achan yake nasa kasuwanchin, Ibrahim yakasanche mutum mai amana da ruqon gaskiya kuma Allah yasah yashiga garin Kaduna da kafar dama...
shekaru sunja sosai izuwa wannan lokachin hankali yakamashi sosai, lokachin kasuwanchi yanata bunqasa, yana samun rufin asiri daidai qwarqwado babu laifi, yana taimakawa yan'uwa da abokan arziki, musamman mah iyayensa, lokachin ne ya gurfana ah gaban iyayensa inda yakeso aje ah nemomasa auran hauwa'u, ( matarda ya dade yanasan aura ) lokachinda mahaifansa sukaji wannan batu sunyi farinchiki matuka, domin hauwa'u yar manyan mutane che tanada tarbiyya ga ilimi da girmama na gaba da ita, kowa yasanta da wannan halin, kasanchewar su ah karamin gari kowa yasan gidansu gidan manyan mutane ne, ba bata lokachi aka bashi auranta kasanchewar yanada sana'ar yi,kuma bashida makusa ta kowani side, kuma ansan irin san dayake tsakaninsu...
bayan daurin aure yadauki matarsa daga katsina xuwa kaduna, kasanchewar achan yakeyin kasuwanchinshi gaba daya, gida ne yakama na haya, dakuna ne kanana ba manya bah guda biyu sai karamun kitchen da bandaki da dan karamin tsakar gidansu, gida kam yayi daidai rufin asiri, hauwa'u mache che ta gari hakan yasa komai ibrahim zaiyi dan ganeda komai nashi saiya nemi shawarar ta, sunkasanche chikin farin chiki da girmama juna .
bayan wata tara da kwana goma da auransu, wata ranar laraba da safe bayan tagama shirya musu abinchin karin kumallo taje tayi wanka tafito, hauwa'u nagani da chiki tsoho haihuwa yau ko gobe tana tafiya da kyar, tun jiya da daddare takejin jikinta babu dadi, daga katsina babu yanda ba'ayi da Ibrahim yakaita gida ta haihu achan bah amma sam yaki, yache saita haihu tukunna tazo tayi wanka ah gida, bayan tazauna ne taji bayanta yariqe salati kawai takeyi tariqe bayanta tarasa me yakemata dadi, anan ne tafara juye juye saiga Ibrahim yafito daga daki dashirin sa na fita kasuwa, hango hauwa'u dayayi ne tana murkususu yasa shi karasawa inda take da saurinsa, koba'a fada bah yasan haihuwa che, dagudu yafita yaje makota yanemi taimakon maqochinshi daya taimaka masa matarsa zata haihu ah kaita asibiti, aikuwa shima dasurinsa yakoma yadauko motarsa aka dauketa sai asibiti, yana zaune lafiya da kowa hakan yasa besamu wahalar samun wanda zai kaita bah, alokachin ko tayar keke bashida ita, bayan wasu awanni Allah ya sauketa lafiya ta haifi danta namiji mai kamada mahaifinsa sak, bayan an sallamesu daga asibiti suka dawo gida, daman sun Riga sunyi shirinsu na tafiya katsina, babu bata lokachi suka kama hanya domin achan hauwa'u zatayi zaman jego, bayan isarsu katsina kowa yayi farin chikin ganinsu chikin koshin lafiya sai barka ake shigowa ana yimusu daga makota, baba malam da hajiya maryam kuwa ba'a magana , farinchiki fal zuchiyoyinsu suna ganin dansu kwara daya ah duniya yafara tara musu jikoki, ballantana baba malam shida ya fitar da rai dasamun d'a ah duniya yau gashi shine harda jika, dayake kafin ya auri hajiya maryam ya auri wata mata, bayan tsahon lokachi dasuka dauka babu haihuwa tanemi takardarta kuma yabata, bayan sun rabune ya aurin hajiya maryam, itama sun dade da aure babu haihuwa, harsun gama fitarda rai kafin Allah yabasu Ibrahim wanda har zuwa yanzu Allah baibashi wani bah, amma Alhmd yanzu gashi har jikoki sunfara taruwa , lokachin da sukaje katsina baba malam bashida lafiya sosai jikinsa babu dadi, ga chiwo ga tsufa abun ya hadar masa da yawa, jaririn ne ahannun babamalam yariqe shi sosai yana masa addu'ah, bayan yagama masa addu'ar yamiqawa Ibrahim shi , ibrahim yache inaso amasa huduba babamalam, baba malam yache wani suna kakeso arada masa? Ibrahim yache sunanka nakeso amasa huduba dashi baba malam, aikuwa baba malam yaji dadin abunda dansa yache, akayiwa jariri huduba da Alameen, amma sunche zasu dinga kiransa da mashkur, kwana hudu da haihuwar mashkur Allah ya karbi ran kakanshi, kuma mai sunanshi wato malam aminu, kowa yaji rasuwarsa agarin nasu, bayan anyi jana'izarsa akadawo akafara zaman makoki, bayan kwana uku akayi radin sunan mashkur, ba'ayi taron suna bah saboda ranar ne akayi sadakar ukun babamalam, bayan sadakar bakwai Ibrahim Yakoma kaduna gurin kasuwanchinsa yache idan matar sa tayi arba'in zai dawo daukarta, idan yaso saiya zauna har ayi arba'in din mahaifinsa sai su koma kaduna gaba daya....bayan sadakar arba'in din babamalam Ibrahim ya hada kan iyalansa suka koma kaduna, Ibrahim yanemu guri yazauna akan kujera ya kalli matarsa hauwa'u chikeda murna yache
" hauwa'u kalli d'an da Allah ya bamu yana kama dani sosai, yabanishi sannan yah dauke mun mahaifina, nayi farinchiki samun d'a ah wannan lokachin kuma nayi bakin chikin rasa mahaifina, amma dukda haka na godewa Allah, yanzu na tashi daga ibrahim nakoma Abba kema kuma kintashi daga hauwa'u kinkoma umma, lokachi daya sunayenmu sun chanja, idan bamu godewa Allah bah waza mu godewa?"
umma tache
"qwaraikuwa Allah shine abun godiya kuma muna godiya agareshi"
*6 YEARS LATER*
abubuwa dayawa sun faru ah wadannan lokachi, chiki kuwa harda bunkasar arzikin abba, babu laifi yakara samun rufin asiri fiye da dah domin ynzu yasayi gidan da yake chiki yazama mallakinsa, abba yazama babban mutum haka zaliqa Umma tazama babbar mache, mashkur kam ya girma tubarkallah kyakkyawa dashi gwanin sha'awa yaro me wayo .
Hajiya maryam kuwa wadda yanzu suke kira da kaka tana katsina har yanzu abunta, dan babu yanda abba beyi ta dawo Kaduna bah taqi, domin achewarta mafarinka shine asalinka, dan chewa tayi babu inda zataje zata zauna da danginta ah katsina, chikin yan uwa kafin nata lokachin yayi itama, haka abba ya hakura ya barta achan saidai yawan ziyara da kyautatawa da yake yimata .
Ah tsahon wannan shekaru shida umma bata kara haihuwaba, mashkur ne kadai danta, kuma daga ita har abba babu Wanda yasa damuwa ah ransa domin sunsan wasu Allah bai basu bah kwata-kwata, dan haka godiya suke qara yiwa ubangiji kullum abusa wannan ni'imar da yamasu, kuma daman ubangiji (S.W.A) yache idan kuka godemun sai inkara muku .
mashkur ya taso shidaya agidansu, yana samun kulawa da tarbiyya agidansu sosai, haka zalika yana qishin kanwa, watarana suna zaune gaba dayansu mashkur yache wa mahaifinsa
" abba "
abba yache
" na'am mashkur"
mashkur yache
" yau da muna dawowa daga school mukayi fada da hamza ( hamza abokinshi ne ) sai yayansa habu ya taremasa, kuma ya zaneni suka tafi suka barni, abba ni meyasa banida yayan da zai dunga taremun fada?"abba yayi dariya yache
"ai Kaine babba agidan nan, bakada Yaya saidai kuma qanne"
mashkur yache
"abba toh ina qannena? inaso nagansu in dunga tare musu fada Nima"
abba yache
"sunanan zuwa da yardar Allah"
mashkur yache
"wallahi abba bazan dunga bari ana tabasu bah, tunda nima haka akemun"duk abunda akeyi Umma batache komai bah karo nafarko da taji wani abu aranta gameda rashin kara haihuwa, abba ya fahimchi haka dan haka ya dakatar da hirar yache
" mashkur!! jeka dauko holiday homework dinka ka fara tunda kaga tafiya katsina zamuyi"
chikin murna da zumud'i yatashi yache
" abba yau zan gama duka, idanyaso gobe sai mutafi koh?"
yatambaya abba, abba yache
" eh"
yana dariyaganin yarda mashkur din yaketa tasalle, aguje yatafi daki yana chewa gobe zan je inga kakaaaa ........
MEERAH