104 "truth! sad & symptoms"

849 68 7
                                    

🌳 QADDARAR RAYUWA 🌳


Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH


1⃣0⃣3⃣

         Kusan duk itache  tamusu parking d'in kayansu, babu wanda yakejin ze iya yin hakan achikinsu, kwana sukayi basuyi bacchi ba suna miqa kukansu ga Allah, musamman su A~li wanda sukaji maganar daga sama, dan ko lokachin da usiii yafad'a musu yanda doctors sukache ah asibiti ba qaramun shock sukaji ba, harma suka kasa gasgatawa saida suka karanta.....

     Kuka kam sunsha kamar sunga gawarta nerh, ko magana babu wanda yake iyawa, saidai shukuriyya tayita rarrashinsu tana basu haquri, kowa yana zaune gefenta, dazarar ta tashi wani ze bita, gani sukeyi kamar idan tabar kusadasu zata mutu.....

 
 
        Washegari dasafe suka kama hanyar airport, duk tsarabar dasukayi shukuriyya bata manta ko d'aya ba saidata taho dashi, itake basu courage d'in duk wani motsi......

      Kafin ma suzo Nigeria mashkur yakira Abba yasanar dashi komai, sunsha kuka sosai suma, musamman ma umma, wanda tunda take bata ta6a ganin tashin hankali makamanchin wannan ba, dashike ya sanar dasu chewar zasu dawo Nigeria nerh saikawai suka kama hanyar Kano batareda sunyi wani shiri ba, harda su haniff aka tafi dukda chewar akwai makaranta.....

      Sunsauka lafiya lau, drivernsu nerh yaje ya d'auko su ah airport din, kowa jikinsa ah sanyaye haka suka qaraso gida, koda suka isa farinchiki nerh ya lilli6e shukuriyya ganin su umma ah gidan, da gudu hanifah tazo ta nannad'e ta tana fushin bata tafi da itaba sai daru take mata, banda dariya babu abunda shukuriyya keyi, tabbas hanifah bazata ta6a girmaba, ganin umma na zubarda hawaye daga nesa yasa ta fahimchi chewar ansanar mata da komai, ita ahakanma farinchiki tayi, atleast zatayi ta kallan umma kafin ta koma gidanta na gasiya, ah daddafe aka gaisa sannan sukachi abinchi kowa fuskarsa babu annuri, dukma basu chi abinchin ba, shukuriyya che kad'ai tachi me yawa sai kuma su haniff wanda basu San wainar da ake soyawa bah....

     ah d'akin ta dake side d'in Nene shukuriyya taje ta kwanta, twins d'inma duk suna wurin umma dake side d'in ummi, achewarta tagaji tanaso ta huta, tana shiga d'akin ta rufe qofa tahau gado ta kwanta, bataso tayi tunanin komai shiyasa duk abunda yazo ranta take kawar dashi, bacchi 6arawo kam yayi gaba da ita.....

     Tun kafin kiran farko ta tashi daga bacchin, dayake tasaka abun aranta sai take ganin kamar harta mutu nerh, achikin bacchinta kuwa tayi mafarkin mutuwarta har babu adadi, wani bin ta ganta achikin makara, wani lokachin kuma taga har an sakata ah kabari, hakadai tayita bacchin me chikeda fargaba wanda ta kasa farkawa se yanzu, ahankali take qarewa kanta kallo, ganin bata fahimchi abunda takeji ba yasa ta tashi ta kunna fitilar d'akin sannan ta qarasa jikin mudubi, skin d'inta duk ya chanja, yayi wani green dashi, duk jijiyar jikinta kuwa tayi yellow, abun gwanin tsoro takoma kamar wata kalar horror, chikinta kuwa yaqara girma kamar sanda takeda chikin twins wata 7, dukda ma tayi tsammanin hakan amma saidata tsorata, ta dad'e ah tsaye sannan taja jikinta ta nufi toilet, brush ta d'auko ta saka toothpaste sannan taqarasa sink taa kunna famfon, ruwa ta zuba ajiki sannan tafara brushing, tana gamawa tayi yunqurin futarda kumfar daga bakinta, tana zubarwa ta zuba ruwa abakinta ta kuskure madadin ruwa ya fito sai jini, qara zuba wani ruwan tayi abakinta still jini nerh ta qara fita, saveral times tayi hakan amma jini be Dena fitowa ba, komawa tayi ta jingina da bongon dayake toilet tana zubarda hawaye, ta dad'e tana kuka, batayi tsammanin ta dad'e ah toilet dinba saiji tayi ana knocking qofar toilet d'in

      "Shukuriyya are you ok?"
Taji muryar zara da tun dazu suka shigo d'akin

     "Yea I am"
Shukuriyya ta ansa sannan tayi wiping tears d'inta ta fito daga toilet

    "Hey! Gud morning"
Shukuriyya ta furta tana qarasawa kusada taju tana pecking nashi ah goshi

     "How you doing tajuu na?"
Ta tambayeshi kaman ze ansa mata, dariya yaketa mata kaman  yasan metake fad'a, lokachi d'aya zuchiyanta ya karaya, tafi tausayinsu fiyeda kanta, yanda takejin tausayinsu ko tausayin kanta batayi, takai hannu zata d'aukeshi kenan kulu ta tsanyara ihu, arazane shukuriyya ta juyo tayi saurin ansarta daga hannun usiii

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now