86 "sweet home"

1K 93 5
                                    

🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳


Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH



8⃣6⃣

🌳🌺😘

Kai tsaye gidan shukuriyya suka kaita suka ajje tareda mijinta haiydar sannan sukuma suka wuche Kano, daka shukuriyya har haiydar babu wanda yata6a tunanin zasu barsu batareda sun tafi dasu bah, dukda chewar daman abuu yache suyi zamansu ah KD tukunna kafin daka baya idan taji ta bakin su umma sai asan abunda za'ayi...

Shukuriyya ranar tazame mata sabuwa fil daka chikin babin rayuwarta, ta dad'e bata tsinchi kanta achikin farinchiki da walwalar RAYUWA irinta yau bah, wannan shine ake chewa ba'a fitarda rai da rahamar ubangiji, haryanxu zuchiyarta ta kasa yardar mata chewar haiydar jinintane, tunaninta shine wataqila zata iya farkawa daga mafarkin da takeyi, duk wasu lokachi saita d'ago ta kalli haiydar dake zaune ah parlourn shima yana saqe saqe achikin zuchiyarshi, la'alla akwai kasanchewar shi jinintane ma yasa wasu abubuwan suka faru ah zaman takewar su, domin ita kanta tayi matuqar mamakin kanta yanda ta dunga 6oye sirrin haiydar kala-kala takasa ko sanarda mashkur bare kuma su umma, tabbas akwai kasanchewar su yan uwa yasa hakan ta dunga faruwa,,,,,

Ta sanadinshi ta 6ata, gashi asanadinta anganshi, shine yashigo chikin rayuwarta yayi mata causing so many pains, wataqila haiydar was meant for something into her life "what's that?" Ta tambayi kanta, daka abubuwan dasuka faru zuwa yanxu she sees noting miracle, hakanan jikinta yabata wataqil akwai al'amarurruka masu zuwa.....

Ahankali haiydar ya taso daga kujerar shi yadawo kusada shukuriyya ya zauna, he wanted to say something amma tears couldn't allow him to talk, shi tunda yake arayuwarshi ma betaba kuka irinna wad'annan lokutan bah

"Shukuriyya!!"
Yakira sunanta

Dashike batasan yin magana awannan lokachin saita saka mishi yatsunta abakinshi alamar yayi shiru, kanta chiwo yake mata sosai saboda kukan datayi yau, ganin ya rufe bakin nashi yasa ta tashi ta nufi d'akin ta....
gidan duk yayi qura saboda sun kwana biyu basa chiki, da qyar tasamu tayi managing ta gyara d'aki d'aya, dukda tanajin yunwa amma kasa gyara kitchen tayi, kwana biyu data saba batayin aiki se yaud'in yazame mata wani iri, kafin ma tagama gyara d'akin duk tayi gumi jikinta harya fara chiwo, lokachin data gama har anfara kiran sallar issha, zuwa tayi ta gabatarda sallolinta saiga haiydar da takeaway, suna gama chi taje ta kwanta saboda gajiyan dake jikinta.

Washe gari tun sassafe ta tashi tayi wanka ta zauna tana jiran fitowar haiydar, ko gyaran gidan ma batayi ba bare ta dafa musu abinchi, she's just missing umma nd she want's to meet them, yana tashi yafito parlour yaganshi ayarda ya kwanta yabari, gabanshi nerh yayi mummunar fad'uwa saboda lokachin da shukuriyya take rashin lafiya nerh kawai yadunga ganin hakan achikin gidanshi, shukuriyya dake tsakar gida azaune jin motsin haiydar yasa ta turo qofar parlourn ta shigo, mamakine yaso ya ishi haiydar ganin shukuriyya dayayi da hijab

"Ina kwana, ka tashi? Sannu da fitowa"
Tafad'a ajere tana kallanshi

Kallo yabita dashi sannan ya ansata, squeezing face d'inta tayi sannan tache
"Gida nake so naje"

"Gida!!"
Ya maimaita

"Eh"
Ta ansashi confidently

"Wani gidan?"
Ta tambaya

"Gidanmu"
Ta bashi ansa

Juyowa yayi ya kalleta ya tabbatar dai she's on her sence, danshi har ynxu memories din abunda suka faru wanchan lokachin suna mishi yawo akanshi, sai yake ganinta kamar sanda take larurar nan, ganin yayi Shiru yasa tache

QADDARAR RAYUWAWhere stories live. Discover now