🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳
Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH
8⃣9⃣
Ranar ma shukuriyya ah dakin ummi ta kwana, dafarko ummi zatayi mata magana amma sai ta qyaleta kawai da nufin gobe saisu tare ah side d'in haiydar d'in, tunda daman komai sabo aka zuba a wurin nashi, haka sabbin kaya suka zuba musu....
Shima haiydar a side d'in yan'uwanshi ya kwana, d'akin A~li suka tafi dukansu, haka suka zauna sukayita hira har wurin asuba, sosai haiydar yaji dad'in zama dasu, har baya san sudaina yin hirar, sai wuraren asuba sannan suka nufi d'akin su, shikuwa haiydar bayan ya idar da salar asuba miqewa yayi ya kwanta akan gadon A~li yana saqe-saqe aranshi, daga qarshe ma bacchi yayi gaba dashi....
Almost a week kenan dasuka dawo gidan hisham da zama, kullum shukuriyya chikin yin waya suke da umma, musamman ma hanifah, sai yanxu ma suke qara chigaba da hirarsu nada kamar dachan dasuke gida, kullum akwai kalar labarin da hanifah zata bawa shukuriyya, musamman ma gameda auran mashkur, wani abunma idan hanifah ta fad'a saidai kawai shukuriyya tayi dariya abunta, dan daman tariga ta saba da gulman ta kala-kala...
Lafiya kullum qara samuwa take awurin shukuriyya, kamar bata ta6a wani chiwo dachan bah, it was on Friday ranarda goggo tazo dakanta ta d'auki shukuriyya takaita side d'in haiydar, sai masifan wasa takeyi wai yarinya da aurenta an rabata da mijinta, haka dai kowa yayita dariya goggo taja shukuriyya ta ajje, sannan tache hira ko chin abinchine kawai zai dunga kawo ta wurinsu amma dai ta dawo d'akin mijinta kenan, shukuriyya chikeda kunya haka ta zauna ah dakin, sai bayan goggo da qannenta sun fita sannan ta tashi ta zagaye d'akin tas tana dubawa, wurin yayi kyau sosai, dukda ma kwanaki sunzo amma bata mishi kallo sosai kamar na yau bah, hotunan ta dana haiydar da aka saka ad'akin ta dunga bi tana kallo, musamman ma na haiydar dan sune suka chika d'akin, tundaga yarintarshi hotunan har zuwa sanda yafara wayo, kyakkyawan yaro dashi fari tas kaman wani aljani, sai yanxu take qara ganin tsantsar kyau irinna haiydar, wani hotanshi daya saka irin suit dinnan na yara ta tsaya tanata kallo, hannunta takai ahankali tafara shafa fuskar hotan
"tsarki ya tabbata ga ubangijin da yayi wannan halittar"Tafad'a achikin zuchiyarta, hannunta data shafi hotan takawo bakinta tayi kissing, kamar daga sama taji motsi ah bayanta, dasauri tajuya sukayi ido hud'u da haiydar, rud'ewa taso tayi dan tana fargabar ache yaga abunda tayi, miskilin kuwa se yayi kamar bega abunda tayi ba ya wuche ya zauna akan kujera abunsa, qarasawa kusada shi tayi ta zauna ah kujerun dake kallanshi sannan ta gaisheshi, "bazan ansa bah" yafad'a chikin sigar wasa, haquri ta tsaya bashi kafinnan dai yache ya haqura....
Tun ranar shukuriyya takoma apartment d'in haiydar da zama, kamar dai yanda goggo ta fad'a chin abinchi nerh da hira ke kaita chikin yan uwanta, dukda chewar ma tunsafe idan tashiga chikin gidan bata fitowa sai dare, tana wurin ummi da sisters d'inta suna hira, mafiya yawan lokachi kuma tana wurin Nene, sosai takebawa Nene lokachinta, she just want to understand the woman, and it seems lyk tagama fahimtar ta, ita kanta shukuriyya har yanxu batayi figuring out laifin Nene bah, tana ganin kamar duk abunda Nene tayi daidaine, kuma tayi shine akan gaskiyarta, kawai dai tad'auki hukunchi me qarfine, kuma da alama sunsamu misunderstanding nerh sosai alokachin, if not duk abun bekai ache anyi irin wannan rayuwarba, even though tana ganin laifin Nene ta wani fannin data saka qafa tabar yaranta batareda ta damu dasu ba harna tsahon shekaru, sannan still bayan ta dawo tachigaba da ignoring dinsu, wannan nerh kawai selfish act na Nene daya bata haushi gameda ita, but as of now tana ganin tunda har tayi nadamar abunda ta aikata yakamata komi yadawo normal position dinshi.....
It was after issha shukuriyya na zaune ah parlour tareda haiydar, hirar Nene tafara mishi ahankali, saidai ta lura bayasan hirar tata gaba d'aya, saboda yanda yayi mata Shiru yake game dinshi awaya batareda ya kulata ba....