🌳 *QADDARAR RAYUWA* 🌳
Written by 🌺 CUTTIEEMEERAH
8⃣0⃣
Dagudu yaqarasa kanta yana kiran sunanta da qarfi, daidai lokachin duka mutanen gidan sukayi kanta atsaye, jijjigata yakeyi amma ko motsi takasayi, da alama ta riga ta suma awurin, d'aukarta yayi gaba d'ayanta ya sakata ah kafad'arshi yafita da ita, ah motarshi yasakata sannan yayi sauri yashiga gaban mota yaja yanufi asibiti, suma gaba d'ayansu mota suka shiga suka bi bayan mashkur ah motochinsu, kowa yana fatan Allah yasadai lafiya, haiydar yafi kowa shiga tashin hankali saboda yasan yanayin dasuke chiki
Babban asibitin dake KD suka nufa, suna zuwa akayi emergency da ita, mashkur yaso shiga wurin amma suka dakatar da kowa awurin sukache ajirasu tukunna, lokachin ma har anyi kiran sallar maghriba, hakan yasa suka tafi sukayi alwala sukayi sallah sannan suka dawo suka fara kaikomo awurin, tunda doctors d'in suka shiga basu fito bah, hakanan suma siblings d'in nata basu gaji da kaikomo sun zauna bah, mashkur da haiydar kana ganinsu kasan tashin hankalin dasuke chiki ba qarami bane bah, saidai umma da Abba sunkasa fahimtar yanayin da mashkur yashiga akan fad'uwar tata, saisuke ganin wataqila harda tension d'in dayake chikine na daxu yasa yakasa nutsuwa....
Abangaren mashkur kuwa yakasa zaune yakasa tsaye, he just hope babu abunda yasamu shukuriyya bcous he don't think he can bear it anymore, kowa wurin addu'ah yakeyi, sai wurin 11 na dare sannan wani chikin doctors d'in yafito, yana fitowa sauran dasuke azaune awurin suka miqe, shikuwa mashkur da haiydar daman ah tsaye suke saisukayi saurin qarasawa kusada doctor d'in
"How's her health??"
Mashkur ya tambaya da zafi yana huchiAjiyar Zuchiya likitan yayi sannan yache
"Actually I can't say a word about her health, were still working on it"
Yafad'a calmly"And what are you outside for?"
Mashkur ya tambaya kamar ze maidashi chikin d'akin
"Calm down Mr man, calm down please"
Doctor d'in yafad'a yana dafa girjin mashkur, d'auke hannunshi mashkur yayi daka girjinshi ya hullar gefe yana me takaichin rashin jin halin da take chiki, kallansu doctor d'in yayi sannan yache"Ammnn!! Am very sorry, munyi iya qoqarin ganinmu wurin ganin mun cheto rayuwarta wanda shine abu mafi mahimmanchi, chikin yardar Allah dai yanxu tana chiki akwanche kuma tana numfashi, saidai am very sorry to say bata chikin hankalinta, hasalima har yanzu bata dawo yanda muke tunani bah, saidai we're still working on her, abunda yasa nafito daman naga yakamata kusan halin da'ake chiki ne"
Shiru yayi bayan yagama fad'in haka, mashkur dake gefenshi ya lura da chewar akwai wani abu da doctor d'in yakesan yafad'a hakan yasa yache
"What again?"
Ya tambaya har yana hararsa"Am very sorry to say, chikin dake jikinta ya fita"
Yana gama fad'a yajuya chikin d'akin, hannu biyu haiydar ya d'aura akanshi bayan yagama jin zanchen doctor, chikin da shukuriyya tagama qwallafa ranta akanshi shine ya zube? Ya shukuriyya zataji idan taji chewar babu shi?, hawayene suke gangaro mishi daidai sanda yake wannan tunanin....
Hankalin kowa saida yatashi awurin dasukaji wannan maganar, ahankali suka chigaba da mata addu'ar Allah ya tashi kafad'unta sannan yabata haqurin rashin abunda yake chikinta, ganin mashkur beche komai ba kuma yanata kaikomo yasa umma ta fahimchi chewar yasan tanada chiki sannan dole akwai wani abu aqasa"Mashkur!!"
Umma ta kira sunanshi, juyowa kawai yayi ya kalleta batareda yache komai bah, shi duk mutanen dasuke wurin haushi suke bashi including his own mother, ganin batache komai ba yasa yad'auke kanshi daga kanta yachigaba da kaikomo awurinShi mashkur ma gaba d'aya surutun nasu 6ata mishi rai yakeyi, kamar ya koresu duka daka wurin haka yakeji,,, ahaka sukayita zama awurin kowa da abunda ke chikin zuchiyarshi kafin wurin 2 na dare doctors d'in suka fito, mashkur nerh yayi kansu sannan yache
"Ya ake chiki?""She's fine please"
Babban chikinsu yafad'a"Kubiyoni office!! We need to talk"
Yana gama fad'a yayi gaba abunshi, bayanshi iyayen nata sukabi tareda haiydar da mashkur akabar sauran qannennasu mata dakuma haniff da hanifah awurin....
Suna shiga office d'in suka zauna ah kujerun dasuka gani yayinda mashkur da haiydar ke tsaye agefe suna sauraranshi, dube dubenshi yayi kafin ya d'ago ya kallesu daidai sanda yake chire glasses d'in dake fuskarsa, ajiyar zuchiya yayi sannan yache
"Munyi nasarar cheto rayuwarta, saidai munkasa fahimtar matsalarta, ina shawartarku daku d'auketa kukaita babban asibiti achikin birnin Kano wato gamji dake airport road ah kano, inshaAllah idan kukaje chan za'a dache, tasamu miscarriage sannan munyi mata dukwani taimako daxamuyi mata na gaggawa, inshaAllah idan kukaje chan bakuda matsala"
Doctor Yafad'a yana relaxingShiru duka wurin sukayi sannan mashkur yache
"Zamu iya tafiya yanxu?"
"Ah'ah!! Tukunna dai, kubari sai zuwa safiya inshaAllah"
"Why not now?"
A~li yafad'a da hanzari"Gaggawa daga shaidanne, kubari ta huta tukunna, she need a rest saboda ta wahala matuqa wurin fitar chikin, and she's still bleeding"
"Subhanalla!!"
Mashkur yafad'a yana jingina da bango ajikin wurinJiki asanyaye dukansu suka tashi suka bar office d'in, suna fitowa sadiiq yakira wani doctor daya sani achikin gamji sannan yache mishi anjima da safe zasu kawo musu patient,,,,,
duk Daren babu wanda yayi bacchi achikinsu, settling yanda tafiyansu zai kasanche washegari kawai sukayi.....Tun wurin 6 na safe aka sallemesu daga asibitin sannan suka tafi Kano, suna isa suka wuche asibitin kai tsaye, daman already sunyi making duk wasu arrangements kafin su qaraso, hakan yasa suna zuwa aka kar6eta sannan akayi emergency da ita, jininta suka fara aunawa dan tanada buqatar jini sosai ajikinta saboda har yanzu bleeding takeyi, tundaga wurin awan jinin babban likitan dake wurin suke aiki atare yaso ya fahimchi halin da take chiki, saida yagama tattara duk wani lissafinshi sannan suka fito daga lab d'in, dashike sunche suna buqatar jini duka mazan sunzo wurin domin ah aunasu, amma doctor d'in yache su barshi babu buqata, doctor d'in dakansu suka samar mata da jinin da aka saka mata, duk wani Taimako na gaggawa saida suka bata sannan yadawo office yazauna yasa aka kira masa siblings d'in nata......
Vote, comments, share and share ur views
MEERAH