*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA**🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}**Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
90to95
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*SIS AYSHA MAMAN HUDA😍*A Majeed shuru yayi ba tare da yace mata komai ba, ganin kaman ya maidata wata Sauna tana magana baya kulata yasa ta matsa kusa dashi tana fadin A Majeed tun muna mu biyu ka sakeni, kallon ta yayi cikin fushi tare da fadin kin ci darajan abu guda biyu amma da yau saina sakeki kaman yanda kika bukata, cikin gadara tace bana son inci darajan komai ni nafi karfin kace naci darajan komai wlh sai dai ni ince kai ne ke cin daraja ta da iyayenka, domin kasan mahaifina shine No 1 a kasar nan dan haka yau ko mai kasha sai ka sakeni tas ya sauke mata mari tare da fadin bansha komai ba zan nuna miki cikin hayyacina nake, saki dai kike bukata koh? Shuru tayi hannunta nakan fuska tana mamakin marin da yayi mata gashi taga kaman zai iya sakin nata domin duk wannan abun da takeyi cika baki ne bawai so take ya saketan ba, ganin karya aikata yasa tabar falon da gudu tana kuka, shima ganin haka yasa ya fita daka gidan gaba daya domin kanshi yaji yana juya mai har ga Allah yana son Zainab sai dai a yau ya fara ganin halin nata mara kyau da Mum dinshi ke fada tana Dashi, wanda shi a da komai ta mishi baya ganin laifinta duk da kuwa tana mishi abunda yafi haka, kodan yau ta taba Mum dinshi ne yasa har yaga laifin nata, tabbas hakane domin yana son Mum dinshi fiye da yanda mai karatu yake tunani, dan tsaki yayi tare dajin haushin wannan kawar Zainab din wai mother inlow are wicked, tunda yabar gidan sai dare ya dawo a falo ya ganta taci uban kwalliya da English wear, top din da tasa gaba daya ta kameta kirjinta duk a bude abunda A Majeed yake masifar so kenan duk da ba wani girma nata suke dashi ba amma tasan yana rudashi, da sauri ta nufeshi tayi hugging dinshi tana kuka tare da fadin am So sorry my swt, kara matseta yayi tare da shafa bayanta cikin kunnan ta ya rada mata stop crying my baby, cikin kissa tace Baby yanzu baka So na ka canza min ta dan janye jikinta daka nashi,A Majeed da ya riga ya fara fadawa da sauri ya matsa kusa da ita yana fadin ba haka bane baby I..... Da gudu ta tafi dakinta tana kuka da sauri ya bita a kwance ya ganta akan 'katon gadon ta tana faman kuka nan hankalinshi ya tashi ya shiga rarrashi dagata yayi ya fara kissing dinta tare da shafata tako ina itama tuni ta fada ranan dai A Majeed yaji dadi domin rabonshi da wani abu ya hadasu harya manta duk da wani lokacin daki daya suke kwana, Zainab ita da kanta tasan samun namiji irin mijinta zaiyi wuya ga kyau ga kudi duk da kudin ba matsalanta bane domin tana dasu wanda bata san nawa ta mallaka ba ma,ita burinta ta sami mijinta ita daya a kullum tana tsoran yaje jalingo ko Egypt kasar mum dinshi kar yaga balarabiya yace zai aura ko Mum dinshi tace ya auri wata daka danginta, domin balarabiya ce kawai zai aura take ganin zata yi kishi da ita dan tasan suna da kyau amma babu wata yar Nigeria da zatai gigin auran mata miji ma ta zauna lfya, domin tana matukar kishin mijinta dan zata iya aikata komai a kanshi sannan bata son yana yawan sex da ita dan a ce wanta yana saurin tsufar da mace hmm tabdi jam ban taba jin haka ba sai a wajan zee🤣.
Mum tayi shawara da Maryam akan mai ya kamata tayi ma indo dan rayuwanta ya in ganta, Maryam ta bada shawaran a sata a wata makaranta na mata wanda ba suyi karatu ba mai suna NEVER GIVE UP IN LIFE, za kayi karatun wata biyar zasu koya ma boko yanda zaki kula da kanki da tsafta da sauran su, Amma ko wanne fanni2 ne Maryam tace a sa aysha a fannin boko dana girki, Mum tayi na'am da batun kuma taji dadi sosai sannan kuma idan mutum ya gama za'a bashi certificate na primary school sannan idan an fara waec da mai bukatan ci gaba da karatu suna da center mutum yana biya yayi amma in za kayi waec sai ka zauna harna shekara daya Kana karatu in kuma primary certificate ne wata biyar, Mum tace aysha shekara daya za tayi domin zata ci gaba da karatu, mum tasa anyi ma indo komai da komai, fara zuwa kawai ya rage shima cikin satin nan zata fara zuwa,.

VOCÊ ESTÁ LENDO
TAMBARIN TALAKA
Contolabari ne akan wata yarinya marainiya da tasha wahalan rayuwa da yanda dan uwanka zaiki yaron dan uwansa sai nasa.