AUREN DOLE sabon Salo

8.4K 436 8
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 1

Sanyin ruwan da taji a jikin ta ga tsananin sanyin hunturu yasa ta saurin tashi a firgice tana mutsike idanu, tayi saurin kallon anty saratu dake tsaye a kanta rike da jug din ruwan sanyi wanda har yafara qanqara

Ta Mike tsaye kana karkarwa sabida sanyin da takeji har cikin qashin ta, cikin tsawa anty saratu tace don ubanki tsayawa zakiyi kina kallo na bazaki wuce ki man wanki ba? Ban fada maki karki yadda Rana ta fito baki gama wanke kayan nan ba? Shine kika kwanta kina bacci har karfe biyar na asuba?

Maryam ta kalli anty cikin rawar murya ga tsananin sanyin da takeji sannan tace anty kiyi hakuri inyi sallah...wani was wawan mari anty saratu ta kaiwa maryam tare da fadin dan ubanki Allah yasa hajji ne zakiyi ba sallah ba amma fa sai kin gama man aikin da nasaka ki sannan

Anty ta janyo ta har tsakar gida ta jefar da ita ga kayanta a jike ga kuma sanyin asuba da yake kadawa tare da taimakon iskar iccen mangoro dake tsakiyar gidan

Ta kalli maryam cikin hadewar fuska tareda nuna mata inda kayan suke, tace idan kin cika dan ubanki kibari karfe bakwai tayi baki gama wanke kayan nan ba

Maryam ta kalli tulin kayan wanda kayan mutun 4 ne aciki Wato kayan anty saratu da mijinta dakuma diyansu biyu

Gashi kayan ba kadan ba kowa ya tara nashi wankin sosai, a takaice wankin zai dauke ta awa biyar indai ba jika jika zatayi ba

Ta tashi jiki na rawa saboda tsabar sanyin da takeji har kafafuwanta hardewa sukeyi, ta dauki bucket ta kunna famfon dake tsakiyar gidan ta tara domin fara wankin yayin da ita kuma anty saratu ta shige daki ta kwanta taci gaba da bacci
****

Misalin karfe bakwai na asuba anty saratu ta fito dakin ta zuwa tsakiyar gida inda maryam ke wanki,  ganin ta tayi tana ta faman shanya kayan, ta iso kusa gareta tare da hankado ta ganin ta sauya kayan jikinta harda hijab

Ke dan ubanki harda canza kaya shiyasa baki gama man wanki ba lokacin da nace kigama ko? Saboda kin raina ni shine kika tsaya sauya kaya ko? Cikin dusashiyar muryar ta da bata fita saboda mura ga rawar da takeyi saboda tsananin sanyi, tace anty wlh sallah nayi...ai bata rufe baki ba anty takai mata wawan mari a fuska tareda cewa oh saboda ke ga sallau shine kika ajeman wanki kikaje yin sallah ko?

Aikuwa nan anty saratu ta hau maryam da duka har saida ta barta kwance tare da warning din ta bata minti talatin ta gama wanki sannan taje ta hada masu breakfast

Maryam wadda zuciyar ta tagama bushewa a yanzu hawaye ma basu fita daga idonta ta tashi jiki ba kwari ta nufi wajen bokitin kayan shanyi
  Bayan kaman mintuna 20 ta gama shanya kayan tass, tana tafiya tana dingishi sabida dukan da tasha tunda safe ta nufi kitchen

Doya ta gani a kasa da kayan miya da kwai hakan ya nuna kata abinda zata dafa kenan as breakfast toh amma batasan ya suke son doyar ba kar ta dafa ba daidai ba tayi laifi

Jiki a sanyaye ta fara firar doyar jikinta na rawa saboda wani mugun sanyi da takeji tana tsakan firar doyar zee baby ta shigo rike da waya a hannun ta, tana sanye da Jeans da rigar sanyi ta sanya earpiece a kunne daya alama waka take sauraro ga ta kalli maryam fuska a daure tace ke aje doyar nan ki dafa min indomie da sauri inada lectures by 10am kuma akwai inda zan biya b4 in Isa school I need to leave this house b4 9am yanzu gashi 8 tayi

Maryam ta kalle ta murya a raunane tace haba zainab bakiga anty ta sakani firar doya ba idan na bari kuma taxo ta man fada fa? Wani wawan kallo ta sakar mata kafin tace ke kikasan wani firar doya wallahi karki yarda 8:30 tayi baki gama min indomie ba ranki zai baci...tafita tana masifa

Haka maryam ta kunna gas Ta daura indomie sannan taci gaba da firar doyar

Wannan kenan
****

Ko kallon inda maman tashi take baiyi ba idonshi na Kan wayar shi yace mummm I'm not ready for marriage for God sake

Mummy ranta a bace take maganar tace wallahi Ahmad dole ka fidda mata saboda nagaji da ganin ka ba aure kai ko budurwa ma bakada ita haba

Murmushi yayi ba tare da ya kalle ta ba ko yanzu sannan yace mumm idan time yayi zanyi aure but not now, cikin kuluwa tace sai ka gama tsofewa kenan ace u are 33years babu aure akan me? Ba rasa abin aure kayi ba fa

Dariya yayi tare da mikewa tsaye yana kallon fuskan maman shi da idanuwanshi masu kaman yana bacci koyaushe  yace mum if u are eager get a wife for me but ni banada time din kula mace yanzu
Mummy tace aikuwa next month kana ganin ka da mata

Yana dariya yace ai ko gobe ne bakomai because na gaji da mitan nan naki every day
Wannan kenan
***

Maryam Muhammad
Yar kimanin shekara 17 mahaifinta da mahaifiyar ta dukansu fulanin Asali ne babanta marigayi malam Muhammad malamin adinni ne kuma yanada rufin asiri daidai gwargwado sai mamanta Haj Aisha wadda suke ce ma haj indo, haj indo da malam Muhammad masoya ne sosai wadanda suke burge kowa banda Idris wanda yake yaya ne a wajen malam Muhammad, Maryam ta taso cikin gata da soyayyar iyayenta, tun tana shekara 13 ta haddace Qur'ani Mamarta ta horar da ita sosai wajen ilimin rayuwa dakuma girke girke a matsayin ta na diya mace, malam Muhammad yana kokari wajen kula da duk wani expenses na family dinshi hakan yasa Maryam tayi makaranta me kyau ta boko tana da shekaru 15 ta gama makarantar boko saide kash rayuwa ta mata illa domin kuwa babanta da mamanta suka samu accident gaba daya Allah ya masu rasuwa rana daya, a lokacin wata daya kenan tayi da gama secondary school

Maryam kyakyawar gaske ce, idan nace muku kyakyawa toh ina nufin kyakyawa sosai, domin kuwa saboda kyaun ta ne yasa lokacin da iyayenta suke a raye Sam basu barinta fita ko nan da can domin wanda duk ya ganta sai yayi magana, a makarantar boko ma haka take shan fama yawanci yammatan sun tsane ta saboda kyaun ta, islamiyya kam ai dole nikaf take sakawa

Bayan mahaifan ta sun rasu aka rasa wanda zai dauke ta a family din saboda dai dama ana haushin yadda malam Muhammad ke hanata yawan fita kamar wata yar gold, sai yayan babanta ne da yazama dole ya dauke ta saboda shine babba a dangin mahaifin ta, mahaifiyar ta kuma batada wasu yan uwa na kusa da zasu dauke ta

Tun da ta koma gidan uncle Idris ta zama baiwa, don kuwa komai na gidan ita ce takeyi gashi baa bari ta fita ko nan da can don ma kar tayi saurayi saboda zubin da Allah ya mata duk namiji daya ganta sai yaji yana sonta,  don kuwa saurayin zee baby yana ganin maryam tazo kawo masu ruwa a falo aikuwa ya rikice yace shi maryam  yakeso harda turo iyayenshi, hakan ne yasa suka kara tsanar ta sai muzguna Mata suke har ta canza kamanni, tayi baki ta rame, ta koma wata iri saboda wahala ga kuma rashin samun kwanciyar hankali da bacci

Pls vote
      Like
And comment

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now