part 21

3.2K 184 6
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 21
Rakiyya bena

Ahmad rungume da kyakyawar yar sa mai kama dashi sak, da ka ganta ka san Ahmad ne uban ta tabbas, ya kalli mami yace kinsan wai babyn nan tana kama dani sosai kuwa? Mami tayi murmushi tace ai haka kowa yake cewa fa

Yace idan na kalle ta wani son ta ke kara shigana saboda daga gani ba tambaya an san jini na ce

Itadai murmushi kawai tayi tana dannar waya, ya kalle ta yace do u decide any name for her?

Tace nice uban ta? Dariya yayi sannan yace ai toh shawara ce bakomai ba

Tace toh banyi ba, u should choose any name for her da kanka ko da talatu ne

Kallon ta yayi yace u r not serious, Her name is Aisha tace toh yayi shikenan baban Aisha

Ranar suna yarinya taci suna Aisha suna kiran ta Aish

Anyi buki budiri sosai, harda maryam taje barka ta kai masu kayan babies dayake tareda mummy sukaje

Kwana biyu da suna itama Fatima ta haihu, aka dauko ta gida wajen shan ruwan zafi

Bayan suna kuwa mami ta tare gidan su Ahmad  a dayan part din da ke kallon na maryam duk da yafi na maryam girma amma kalar su daya da komai

Ita safiyya sam bata san mami ta tare ba don ta dauka ai sai bayan Arba'in xata tare

Haka ya shirya tafiyar sati daya na karya yace mata zai tafi Enugu state wajen wani conference don ya san idan yace Abuja zata iya cewa zata bishi

Bata kawo komai ba kuwa ta raka shi har wajen mota ya tafiyar shi bai tsaya ko ina ba sai Airport inda ya shiga jirgin da yayi booking wanda ya gwada mata ticket

Yayi pictures sosai ya tura ma safiya sannan ya fito ya tafiyar shi zuwa wajen matar shi da diyar shi da yake missing sosai

Wani mugun so yake ma Aish wanda shi kanshi bai dauka zai so ta hakanan ba

Mamaki yayi ganin maryam zaune a part din mami suna ta lafta fira maryam kuwa na rungume da Aish

Hannu kawai yakai ya dauki Aish gaban sa na dukan uku uku kamar koyaushe idan ya hadu da maryam, ya kalli mami yace maman baby ya kike? Tace lafiya lau

Yace jikin ba matsala ko? Tace eh sai kawai ya wuce ciki abun shi dauke da babyn shi

Maryam ta muke tsaye tace toh nikam zanje wajen mummy sai na leko gobe ko ? Mami yace alright dear sai goben thank u ina gai da mummy kinji?

Mami tace hope dai nan zaka kwana? Tare da mu

Yace ba ma kwana daya ba, sati zanyi maku a nan ko kofar gida banzan je ba

Dariya tayi don bata yarda ba, ta san jidalin matar shi

Yace am serious fa naga kina man wani kallon banza, ya fada yana dariya

Itama dariyar tayi tace hmmm lallai wani abu sai Aish don na san wannan kwanan ba nawa bane nata ne

A daren ranar safiyya ta kwana tana zazzabi ta kirashi ta fada mashi yace bari ya kira mata likita

Ya aika abokin shi likita yace yaje ya duba ta ya mata test da allurai da niyyar da safe zaizo

Pregnancy test din da aka mata yazo positive, dr Muhammad ya kira abokin shi tun da asuba ya fada mashi kyakyawan labarin cewa safiya nada ciki don ya san Ahmad da son yara

Aikuwa murna wajen Ahmad baa cewa komai,  ya zauna yana ce ma Aish ta kusa samun kane very soon

Dr Muhammad na fada ma safiya tana da ciki aikuwa ta bata fuska, wane irin ciki kuma? Tace ma dr Muhammad kar ya fada ma Ahmad cewa tanada ciki okay kawai yace mata don shi dama baya son safiyar nan saboda rainin wayon ta

Ai kuwa dr Ahmad na fita itama ta fita ta siyo abortion pill wanda Dama ta san shi ta taba amfani dashi

Ta kuwa sha shi ta zubar da cikin nan a cewar ta bata shirya haihuwa ba sai Ahmad ya gama dokin wannan Aish din da aka Haifa mashi

Yayi ta kiran ta bai samu ba yana son yayi congratulating din ta dole ya hakura, yana son zuwa gidan ya gan ta amma kuma for now yafi son ganin Aish dinshi

6days later

Kwance ya iske ta Kan kujera tana dannar waya hankalin ta kwance domin cikin har ya fita

Ta taso ta rungume shi tana fadin welcome my love, yace thanks dear ya jikin ki? Tace am fine now

Duk kwanakin nan sai firar cikin nan sukeyi da ita shi sam bai san ta zubar ba, sai da dare da yake neman kusantar ta amma tana bleeding har yanzu

Mamaki ya cika shi yace babe dama ana bleeding ne in akwai ciki? Dan tsuki taja irin na I don't care dinnan tace baby am sorry ni fa na zubar da cikin nan saboda am not ready for it

Wani wawan kallo ya mata alamar wasa dai kikeyi, tace cikin nuna rashin damuwar ta, ba fa wasa nakeyi ba naga ne kana ta rawar kai akan wannan yar shegen shiyasa nace bari in bari ka gama b4... wani wawan mari da ya wanke ta dashi ne ya sa ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki

Me nayi maka da zaka mare ni? Are u this stupid safiyya? Ubanwa yace ki zubar man da ciki? Ta kalle shi tana kara mamakin shi

Cikin ba a jikina yake ba? Ban tashi ba shiyasa na zubar ta fada cikin tsiwa

Shakure ta tayi ta hada da bango yace better tell me wasa kikeyi kafin in kashe ki wallahi

Cikin zafin nama ta fincike shi tana fadin nace na zubar kayi abinda zakayi bazan haifi da ka hadashi da wannan shegiyar diyar taka ba wajen soyayya...

Aikuwa ya hau ta da duka yana fadin ko a mafarkin ki karki yadda ki kara ce ma diyata shegia don ba shegia bace da uban ta kece dai shegiyar don duk yar halak bata zubar da ciki da uban shi

Bakin ta ya rufe ta kwanta sai kuka takeyi saboda ba karamin buguwa tayi ba, shikuma ya fita da tsananin bacin rai yaja mota a guje da niyyar komawa gidan su wajen mami

Kiiiiiiiiii......wani mumunan hatsari Ahmed ya hadu dashi wanda Allah ne kawai zai fitar dashi..

Pls comment
Like and vote

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now