part 24

2.7K 167 1
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 24
Raqiyya bena

Maryam tace anyi mami aike kin tuba kuma irin tubar da akeso bawa yayi insha Allah tubar ki ansashiya ce

Muci gaba da yi ma yaya Ahmad Addua kuma Allah ya shiryar dashi shima

Mami tayi shiruuuu

Wani zafi takejin yana ratsa ta

Ta durkusa tana maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihirraji'un

Da sauri maryam ra rike ta tana cewa lafiya anty? Ko haihuwa ce? Mami tace no this is my 8th month

Nan take jini ya fara zuba ai kuwa maryam ta sheka ta kira mummy

Da sauri aka dauki maryam zuwa asibity

Nan take aka shiga da ita labour room saboda premature labour ne ya kama ta

Har kusan awa biyar suna cikin labour room din sai can aka fito domin a saka hannu ayi mata CS

Dr Ahmad wanda duk ya gama rudewa ganin halin da mamin sa take ciki ya saka hannu don ayi mata CS a cire babyn su a ceto ran matar shi

Amma inaaaaa Mami rai yayi halin sa tun kafin a shiga da ita theater room

Ta rasu ba tare da ta haifi abinda ke cikin ta ba

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un

Doctor ya fito ya sanar ma iyalan mami cewa Allah ya mata rasuwa, mutuwar zaune Ahmed yayi

Wani shock ne ya kama maryam nan take ta fadi wajen a sume

Suna fira lafiya dazu yanzu kawai ace mami ta mutu?

Dr Ahmad kam saida anka taba shi, juyawa yayi ya kalli Aish dake kwance a jikin fatima tana bacci hankali kwance

Jin yake kamar ya kuwwata, ya tuna lokacin da zai fito daga gidan da safe mami na zaune kan gado tana sanya ma Aish riga

Ya kalle ta yace mai ciki ayi sauri a haifo mana kayan mu, tayi dariya tace toh kuyi Adduar Allah ya kawo shi lafiya

Yayi dariya kawai ya ce toh amin, zan aiko a ansar min diyata idan na gama lecture na zuwa anjima

Tace toh ai gara ka aiko a dauke ta kar ta dame ni

Wani irin ihu Ahmad ya saki tare da faduwa kasa yana kuka kamar karamin yaro yana fadin maaaaaamiii

Karar da ya saki ce ta tayar da Aish daga bacci itama ta kama kuma daga ka gansu ka ga abin tausayi

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now