part 32

2.5K 144 1
                                    

Auren dole sabon salo
Part 32
Raqiyya bena

Emergency aka kaishi sai aman jini yakeyi

Da sauri aka shiga dashi aka fara duba lafiyar sa

Shiru har kusan awa 6 baa fito ba

Mummy na zaune gefe hankalin ta duk ya tashi. Dan ta guda tal namiji kenan ya zatayi da ranta? Dukda tana purnishing dinshi saboda ya gyara halin shi amma ai tana son abinta

Maryam kuma tana tsaye a gefe duk kwalliya ta dame da zufa da hawaye an cire head

Haka su anti zulaiha dasu fatima duk kowa an rude da anti babba sai kuka suke

Zuwa yanzu kowa ya fidda rai don ganin yadda aka shiga dashi jini na fitowa daga bakin shi

Can kusan asuba. Karfe biyar na asuba likitocin suka fito a gajiye don tsaye suka kwana kan shi

Dr nabeel ya kalli maryam da ta rakube gefe duk ya tausaya ma amaryar tashi

Yabar abokan aikin shi suyima mama bayani shikuma ya isa inda take

Ya kalle ta tayi wani zuru zuru yace haba babyna wannan kukan fa? Ta daga kai ta kalleshi da hawaye fal a idon ta

Tace bai mutu ba ko? Yayi murmushi yace bai mutu ba baby

Dr haidar ya ce yana son ganin mummy da daddy a office

Suka bishi suka zauna suna ta fargaban abunda zaice

Ita mummy gaba daya tunanin ta cewa zaayi HIV gareshi

Daddy ma dai nashi tunanin bai wuce haka ba

Dr yace gskya dan ku yana bukatar kulawa sosai
Bansan yadda akayi kuka bari har ya samu wannan illar haka ba

Na farko dai ya kamu da ciwon zuciya domin dazu bugun zuciya ya samu shiyasa ya fadi

Sannan kuma ga ulcer tayi mashi yawa sosai domin ulcer ce ta saka shi yake aman jini

Kamar dai yakai 2weeks bai sa abinci a hanjin shi ba. Akwai dai abunda yakeci wanda yake sustaining dinshi amma ulcer tayi mai mugun kamu

Munyi mai allurai dai yanzu da karin jini da ruwa an samu bugun xuciyar nashi ya fara komawa normal amma dai gskya dole sai an guji bacin ranshi sosai da duk abunda zai bata mashi rai

Idan har wani abu yake bukata a gaggauta samar mashi idan har me samuwa ne don hakan ne kawai zai ceto rayuwar shi

Kuma yanzu muna fatar ya farka ba tare da ya fada depression ba don dama dai he is depressed

Ku gode ma Allah Ahmad ya rayu domin mutun guda duda ne ke rayuwa bayan samun attack irin nashi

Ko yanzu akwai yuwar sake samun attack din indai har samuwan abunda yakeso zaiyi wuya

Kuma gskya bazanyi alkawarin zamu iya ceto shi ba idan ya kara samun irin wanann attack din

Mummy kam kuka kawai take yana magana

Daddy yace dr kunyi mai test na komai lafiyar shi lau bayan wannan?

Kallon daddy dr yayi da mamaki. Alhaji ban gane ba? Ai ba lafiyar shi lau ba domin kuwa wannan babban cuta ne

Daddy yace ina nufin kun gudanar da HIV test da sauransu lafiyar shi kalau?

Dr yace eh alhaji munyi mai HIV test saboda patients din HIV suma suna samun irin wannan attack din saboda damuwa. Saide shi bayada HIV shiyasa muka gane tabbas wani babban alamari ne ya saka shi cikin wannan yanayin saide Addua kawai

Daddy yace toh mun gode dr

Dr yace zamu bar shi a asibiti for atleast a week under observation 

Sukayi ma dr godiya suka wuce

Tsayawa sukayi ganin nabeel yana rarrashin maryam yana bata magani don ta rage stress

Mummy ta ce maryam ku tashi muje gida muyi sallah muyi wanka mu huta sannan mu dawo

Haka akayi

Sai kusan sha biyun rana suka dawo saboda da sukayi sallah kowa bacci sace shi yayi saboda an kwana baayi bacci ba

Dr nabeel ma yana gida sam bai dawo ba shima kwanan yakeyi

Yau ne yakamata ayi mothers night amma gashi wannan abun ya faru 

Sam baa ma yanke shawarar me zaayi ba tukun

Har yanzu Ahmad bai farfado ba

Suka zazzauna a wajen dakin kowa bai cewa komai

Nabeel ya shigo da yaranshi suka sheka suka rungume maryam suna mummy we missed u

Ta dan shafa kansu. Tana son yaran har ran ta

Amal ta shigo itama ta kalle ta tace sister ya mai jikin? Maryam tace Alhamdulillah yana ciki

Suka gaisa ta samu waje ta zauna

Yaran sun dan saba da amal don haka maryam ta bar mata su ta shiga don ganin patients dinta

Dayake asibitin da suke aiki ne

Sai bayan sallah azahar sanan ta dawo

Nabeel yana office dinshi

Yaran kuma suna tare da amal har yanzu. Suna ganin ta sukayo inda take

Abinci ta aika aka siyo don su mummy ma komai basuci ba

Shi daddy ko magana sam bayayi

Nabeel kuma a office tunani yakeyi yanxu daga auren zaayi kenan? A ranshi yake tunanin sai wata zuciyar tace indai dattijan mutane ne kamata yayi su daura maku auren ku ko babu taron buki tunda an saka rana gashi har tazo. Wata zuciyar tace koda yake da ba wasa bane. Bari dai muji yadda zaayi

Da yamma misalin shida na yamma mummy da daddy suna tafiya cikin mota zasuje gida

Daddy yace auren nan bazai dauru gobe ba. Mummy tace meyasa?

Akwai abunda nake nazari...
Amma dai...

Dakatar da ita yayi. Sai an sallami Ahmad zan samu natsuwar yin hakan

Karfe tara na dare Ahmad ya farfado

Sunan maryam radam a bakinshi

Sai kiran yake mummy don Allah karku aura mata kowa in ba ni ba wallahi zan mutu in ban aure ta ba wallahi na tuba don Allah abar bukin nan

Mummy  da daddy da su maryam duk suna wajen dakin don haka yana fara surutan suka shiga gaba daya

Cak ta tsaya jin abunda yake fadi

Whaat?

Bata taba sanin tana son nabeel ba sai yau don tunanin rabuwa dashi kawai yazo mata sai ta fashe da kuka

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un take fada a ranta

Da sauri aka kira dr haidar yazo aka mashi allura suka fita

Dr haidar yace ma mummy da daddy. Wacece maryam? Suka nuna maryam dake zaune a gefe tana kuka

Yace ahh dr maryam tamu? Let me talk to her...
   Ya isa wajen ta yace dr meet me in my office

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now