part 10

3.4K 168 1
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 10
Rakiyya bena

Washe gari tun da safe kamar kullum maryam na karanta Al'qurani sai ga mummy ta shigo dakin

Ta zauna gefen gado tana jiran ta kai aya, bayan ta kai aya ta rufe Al'qurani ta juyo ta kalli mummy tace ina kwana mummy?

Mummy tace lafiya lau maryama, nazo ne in maki nasiha irin wadda mahaifiya zatayi ma diyar ta idan zata aurar da ita

Na san bakida kowa da zata maki wannan nasiha idan bani ba, don haka ki saurara dakyau kiji abinda zan maki, yadda nayi ma su Aisha dasu Fatima haka zan maki saboda ina jinki a raina kamar su

Ni surukar ki ce amma kuma tamkar diya ta tacikina na dauke ki

Maryam zaman Aure sai anyi hakuri, zaman da mukayi dake na sati daya na gane kinada shiru shiru da rashin son yin magana toh lallai ki gyara dole sai kin fara magana kina fadan raayin ki akan wasu abubuwan, shiru bazaiyi ba

Ahmad nice na haifeshi da cikina amma zan iya ce maki na rasa gane takamaimai halin shi saboda baya ma sakewa da mu

Kullum zaki ganshi yana dannar waya idan kinga yana fira sosai toh da antin shi Aisha ce kokuma Fatima

Dole ki zage damtse ki janyo raayin shi ta hanyar kwalliya da kisisina irin tamu ta mata

Bamu sani ba ko yanada yammata a waje amma dai ki tabbatar koda ace yanada yammata kin kwace su daga gareshi

Zamanin mu zinah tayi yawa sosai maryam, namiji da aure da ba aure sai kiga zinah yakeyi ba abinda ya Dame shi

Bana zargin Ahmad amma na dade ina tunanin shin lafiya Ahmad baya da shaawar in aure? Kinga akwai Alamar tambaya ko?

Don Allah maryam ki kwato man d'a na daga halaka idan har yana cikin mazinata kece zaki fidda shi yanzu ta hanyar biya masa dukkanin bukatun shi na aure, ki rinka yawan kallace kallacen yanayin da rayuwar yammatan waje take
Yadda suke dressing kema kiyi ma mijinki, yazama duk abinda zai gani a waje yana da shi a gida

Ki kula da abinda yafiso a jikinki kuma ki rinka gyara shi koyaushe

Na lura kinada tsafta sosai, kuma na san kin saba da aiki, dukda akwai masu aiki biyu a gidan toh kisani Ahmed baya cin girkin me aiki

Ki gyara gidanki da jikinki da abincin ki, insha Allah xakiji dadin zaman auren ki don na san Ahmad ba maketaci bane

Koda ta gama maganar maryam hawaye nata zuba a idon ta, ashe zan samu wannan gatan? Ta fada a ranta sannan ta bude baki sannu sannu tace nagode sosai mummy insha Allah zanyi abinda kikace kuma nagode sosai da soyayyar ku a gareni

Mummy tace toh zuwa magrib zaa kaiki kiyi kokari ki shirya kafin nan kuma kiyi amfani da magungunan da antynku ta ce kiyi amfani dashi

Cikin jin kunya maryam ta ansa da toh tana bin mummy da kallo har ta bar dakin

Kwantawa tayi Kan gadon a ranta tana tunanin yadda rayuwar ta tacanza lokaci daya, lallai addua bata faduwa kasa banza ana ganin an rabata da masoyinta gashi Allah ya musanya mata da masoya dayawa

8pm
Gidan su Ahmad cike yake da yan uwa da abokan arziki ana shirin raka amaryar zuwa kayataccen gidan ta na dr Ahmad

Daddy ya aika da driver a dauko su anty saratu wanda suke ta murnan zuwa suga halin da zasu iske maryam a gidan

A hanya suka hadu da motocin da suka dauko amarya, sukaga driver yashiga cikinsu ana ta gudu an dauko amarya motoci sunfi 20

Mamaki suketa yi tun da sukaga motar da aka aiko daukar su kirar 406 wadda itace karamar mota duk gidan anyi hakan ne don kar su zargi wani abu sai sun iso amma sunata mamaki

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now