part 6

3.2K 171 0
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 6
Rakiyya bena

Maryam tana gugar ranta na mata zafi sosai saboda tana matukar son ganin usman don kuwa bayan Amal duk duniya batada kaman shi

A yanzu shine kadai take gani tayi murmushi saboda son da take masa
Ita kanta tana mamakin yadda a kankanin lokaci take sonshi haka

Amma hakan ai bazai rasa nasaba da batada wani mai nuna mata soyayya kaman shi

Shikuma Usman tun da aka ce masa batanan yasan dawuya in gaskiya ne don tunda yake zuwa wajen sati daya kenan sai an kawo nashi excuse din da zaa saka shi jiran ta

Yau ma gyara zaman shi yayi cikin mota kusan awa biyu yana jiran ta amma shiru sai ya samu yaro yakara aikawa akace bata dawo ba

A hakan ya daure yatafi yana dokin son ganin ta, shidai maryam na bashi tausayi, yana karanto damuwa a tare da ita duk lokacin da suka hadu

7:40pm

Bayan sallar isha'i maryam ta samu ta gama gugar ta gyara ko ina tayi abincin dare, ta zauna tana tunanin ko Usman zai sake dawowa? Walakancin da ake mashi yayi yawa

Sai taji sallamar yaro ana fadin wai usman na kiran maryam

Ai bata jira komai ba ta fita da saurin ta kafin anty tace wani abu, don ita kam yanzu ko dukan ta zaayi sai ta ga Usman don tayi matukar missing dinshi kuma tana son ganin shi

A jingine jikin motar shi ta same shi, tayi sallama tare da gaishe shi

Murmushi yayi jin siririyar muryar ta mai dadin sauraro, dukda a kullum tana shake saboda sanyi da mura amma hakan bai hana sautin ta dadi ba

Yace yammatan usman an wuni lafiya? Ta ce lafiya lau

Yace maryam dama inason muyi magana dake, ta kalle shi bayan mumunan faduwar gaban daya same ta domin tayi tunanin zaice bai kara zuwa tunda ana mashi walakanci

Murmushi yayi tare da cewa, kina sona? Sam batayi tsammanin hakan ba amma cikin sauri tace eh.. Ina.. sai kuma tayi shiru ta rufe fuska alamar kunya

Yayi murmushi wanda har sautin murmushin ya fita

Yace zan turo magabata na maryam inason a daura mana aure saboda gaskiya na yaba da hankalin ki

Nidai ba yaro bane kuma na fada maki na taba aure, inada gida na da komai

Bazai wuce wata daya ba ma idan zaa saka ranar AUREN saboda na matsu in kaiki gidana in kula dake da lafiyar ki, bana jin dadin yadda kullum mura kikeyi alamar baki kula da dokokin likita

Ya fadi hakan ne don yaji me zatace don shi kanshi ya san ba laifin ta bane

Maryam tace toh bakomai na amince ka  turo din

Maryam dadi takeji har kasan ranta, Zata bar wannan rayuwar bautar

Suka dan kara Tattauna wa sannan ya mika mata siyayyar da yayi mata, turare ne da chocolates  da kuma waya Nokia me torch light wadda ya riga ya saka sim ya sa number shi

Yace na san kila bazaa bari ki rike babbar waya ba amma ki man sallama da anty ko uncle in nemi alfarma su bar  man ke kirika wannan in rinka jin muryan ki kafin AUREN mu

Haka akayi taje ta kira anty, ba don ranta yaso ba aka kyale maryam da wayar amma suka anshe chocolates ko guda bata ci ba, dama shi turare bar mata abunta sukeyi idan ya kawo saboda ta rinka fesawa yaji ya dauka komai ma bar mata sukeyi

****
Dr Ahmad zaune a office dinshi yana duba wasu files, wata kyakyawar budurwa ta shiga office din da sallama  tace sir gani

Ya ansa sallamar ta tareda cewa naga message dinki kince kinason ganina shiyasa na ce kizo... yana maganar ne ba tare da ya kalle ta ba

Shiru tayi na dan wani lokaci kafin tace sir na dade ina son ka wlh.. dagowar da yayi ya kalle ta shine ya katse mata hanzari ta kasa karasa abinda takeson cewa

Surar ta ya kare ma kallo kafin yayi murmushi a ranshi yace ba laifi

A Fili kuma yace meet me in room 106 Safara Hotel tomorrow by 8pm and idan kika yarda naji wannan maganar wani waje you'll leave this school, but u can decide whether to come or not

If u decide to come make sure u come on time and if u decide not to come don't ever call my line or text me again..

Yana gama fadan haka ya nuna mata hanya

Ita kuma ba tare da ta ce komai ba ta wuce a ranta tana murnar cin nasara

Domin kuwa itama ai abinda ya kawo ta kenan saboda ta san bazaiyi soyayya da ita ba

Hakan kuwa akayi ta iske shi hotel suka aikata masha'ar su sannan ya bata warning kar ta kara neman shi idan yanada bukata da ita zai neme ta kuma kar ta yadda yaji labarin ance ya taba kula ta

Dr Ahmad kenan. Shi baya da aikin daya wuce zinace zinace, baya neman mace kam amma duk mace ta kawo kanta indai tayi mai bazai barta ta tafi a banza ba, shi kanshi bazai iya lissafa adadin matan daya kwanta dasu ba

A office dinshi condom bai kare wa saboda kar ma bukatar shi ta tashi babu

Ahmad nada yawan shaawa yayi aure kuma yaki yin aure amma kullum yana nan yana alfashar shi tare da walakanta yammata

Allah ne kadai yasan yawan yammatan dake mugun sonshi amma shi kawai bukatar shi itace zina

Cikin masu matukar son shi harda cousin dinshi mami wadda ya maida kaman matar shi

Har ciki ta zubda sau biyu wanda harda fada sukayi akan shi yace bazata zubar mai da ciki ba ita kuma tace sam bazata haifi shege ba

Mami tana matukar son Ahmed shima yana raayin ta saboda itace kawai macen da yake kusanta babu protection kuma yadade yana muamala da ita amma bai rabu da ita ba saide tana shan walakanci kala kala a wajen shi

Bayan wata daya

Murna a wajen maryam Baa cewa komai domin yau ne daurin auren ta da masoyin ta Usman

Su Amal anzo bukin sister dukda kwana daya zatayi yinin buki ta koma saboda ba event da zaayi sai bayan ankai amarya ne zaayi walima

Ba wani taron buki ake ba, saide yan uwan mahaifiyar ta da na mahaifin ta da suka dan zo, ita sam abin bai dame ta ba itadai kawai a daura auren

Duke take tana wanke wanke kayan abincin bukin, oh ikon Allah amarya da wanke wanke

Dayake amal bata gidan sunje can gidan maryam din kai wasu kayan

Uncle yashigo gidan dauke da sadaki a hannun shi naira dubu talatin da kuma goron daurin aure

Ya kiran anty da maryam din sukazo

Yace maryam ga sadakin ki, na daura maki aure

Murmushi maryam tayi ta amsa tare fa cewa na gode kawu, wani sanyi taji ya sauka a ranta dukda batasan dalilin faduwar gaban da takeji ba amma kawai tace maybe saboda an daura mata aure ne

Wani wawan kallo uncle ya mata yana kallon murnar dake fuskar ta sannan yace yawwa na manta ba da usman na daura AUREN ki ba

Naga wanda yafi usman chanchanta shiyasa na bashi

Wani mahaukacin faduwar gaba yazo ma maryam nan take ta Mike tsaye tana ja da baya tana maimaitawa kalmar innalillahi wa inna ilaihirraji'un

Anty ma kanta ya daure amma tabbas taji dadin abin saboda dama tana bakin cikin farincikin da maryam keyi na wannan auren

Daki ta shiga da guda ta turo kofa jiki na rawa ta kira lambar usman, saida tayi ta ringing kusan sau biyar sannan ya dauka muryar shi a wahale yace maryam...

Karo ba farko tun bayan rasuwar iyayen ta da hawaye ya zubo mata duk da wahalar da take sha

Tace Usman karka ce man da gaske ne uncle ba kai ya aura man ba?

Shima hawayen ne a fuskan shi yace sai hakuri maryam, uncle ya walakanta mu  dani da iyaye na don kuwa muna zaune kawai yace ya fasa bani aurenki wai wani AHMAD zai ba

Don haka inason kiyi hakuri maryam uncle ya daura auren ki da Ahmad wanda baima zo daurin auren ba

Wata kara maryam ta saki tare da faduwa wajen a sume..

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now