part 15

3.2K 177 3
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 15
Rakiyya bena

A wani hadadden Gurin cin abinci tace a ya same ta

Ya iske ta tayi masu booking table guda ta zauna dannar waya, ya kirata yace gashi ya iso sannan ta fito ta ta tarbe shi suka koma ciki

Kallon ta yakeyi sosai yarinyar tayi mashi, shi bazaice yana sonta ba amma ta shiga ran shi yana mugun shaawar ta

Ya dan yi gyaran murya sannan yace safiyya why d u decide sending me your nude pics every night har 1month?

Tayi murmushi cike da kwarewa, da ka ganta ka ga cikakkiyar yar bariki abin da yake so

Yadda take maganar yana kara mashi shawar ta da son kasancewa tare da ita

Tace kawai na san ta hakan ne zan janyo raayin ka tunda baka kula ni.. kuma ni bazan iya hakura dakai ba ,ta fada tana kashe ido

Yayi murmushi yace amma kinsan kin azabtar dani ko? Yar dariya tayi sannan tace ai nafika azabtuwa ni da nake jiran reply dinka kullum amma shiru kaman anyi ruwa an dauke

Ya dan yi shiru yana nazarin ta, safiyya ta hadu, gata black beauty ga shape din kwarai fatar ta kaman madara sai glowing takeyi

Gashi ta waye sosai yanayin dressing dinta da yanayin maganar ta ya tabbatar mashi da cewa safiyya ba karamar wayayya bace

Yace safiyya how old r you,  ta lashe kasan kyawawan lips dinta sannan cikin salon jan hankali ta mayar da muryar ta zuwa muryan shagwaba tace  i am just 22 I hope ba cewa zakayi na maka karama ba

Murmushi yayi 22? Wow yace a ranshi lallai an gamu an dace, she is just perfect

Shekarun ta basuyi yawa ba kuma basuyi kadan ba, kaman dai yadda yakeson mace...

Wayar shi ce tayi ringing ya duba, sis mami ya gani a screen kaman yadda yayi mata saving

Ya dauka yace hello mami yaya? Tace yaya Ahmad pls ka zo man da apple dan Allah, inata craving dinshi har na kasa yin bacci

Murmushi yayi yace ok gani tafe yanzu in kawo maki, shidai kam yana son cikin shi sosai

Safiya ta kalle shi ganin yafara kokarin tashi tace ba dai tafiya zakayi ba my doctor? Ya dan Sosa keya sannan ya sake mata yaudararren murmushin sa

Yace dole in tafi lalura ce, sis dita ce da take da ciki wai apple take son ci

Tace ou ayyah toh Allah ya raba lafiya... ya ansa da amin

Ta raka shi har wajen mota ya shiga ya wuce itama ta shiga tata motar ta wuce

A gida kuwa

Da kyar maryam ta shawo Kan mummy ta nuna mata addua zata masu insha Allah komai xai wuce kuma kar ta yi fushi da Ahmad don fushin ta ba karamin illa bane ga rayuwar shi

Haka sukayi ta saka mata albarka suna kara mata karfin gwiwa sannan suka wuce ta raka su har wajen mota, ganin babu motar shi amma ga motar mami nan abun ya basu mamaki saide suka kyale ba tare da sun kara cewa komai ba akan maganar suka tafi

Daga Fatima sai amal aka bari a gidan tare da maryam

Suka dawo babban falon suka zauna suna fira suna kara bata hakuri

Maryam tace ai ba komai bane wallahi, kinga yaya Ahmad tun ranar da aka kawo ni gidan nan tare da wannan matar ya kwana a gidan nan amma ba wanda na fada ma

Kuma yanzu na san bazaku tona mana asirin gida bane shiyasa na fada maku don in ji sauki cikin rai na

Kuma ina ma yaya Ahmad addua kullum Allah ya fitar dashi daga wannan halin

Fatima tace wallahi yaya Ahmad bai samun mace ta gari da ta fiki maryam, Allah ya kara baki hakuri shikuma ya bashi ikon ganewa tun lokaci bai kure mashi ba

Amal tace amma fa ba wannan ba, dole ne fa ki daura damarar kwato mijin ki wallahi

Yadda na lura kaman yaya Ahmad yafi son irin yan barikin matan nan, don tunda ya kula wannan gimbiya mami kinsan taste dinshi kenan

Dole ki mayar da kanki yar bariki a gidan ki Don janyo hankalin mijin ki

Fatima tace kuma gashi su mummy suna maganar ta koma makaranta, da suna cewa makarantar shi zaa sama mata admission amma ina ganin tunda yanzu bai da time dinta gara a tura ta Nile Abuja

Can Zata kara bude ido sosai kuma bazai rinka ganin ta ba sai bayan lokaci lokaci

Har sai lokacin da ta zama cikakkiyar mace fiye da tunanin shi

Maryam tace kai Fatima anya kina ganin hakan zai yi? Kawai in koma Abuja in bar mijina? Toh da wa zan zauna a can?

Fatima tace ai anty zulaiha can take, kuma akwai diyar mijin ta zahra Wadda take hannun ta itama a Nile din take

Gata wayayyiya ce kuma ba irin wayewar nan ta iskanci ba, sai ki rinka zuwa weekend kawai

Maryam kam numfashi kawai ta ja bata ce komai ba tanata sake sake a ranta

Ahmad ya shigo ta kofar falon dauke da leda a hannun shi ta apple din da aka saka shi sawowa

Yace ah Fatima kina nan? Tace eh ina nan yaya suka gaisa sosai sannan suka gaisa da amal itama ya wuce ciki

Mami jikin nata kam sai a hankali tana fama da laulayi sosai

Ko apple din da taci ma Aman shi tayi yanata tausaya mata

Ya fito da ita rike a hannun shi jikinta yayi zafi sosai da niyyar kai ta asibity

Haka suka bi ta gaban su maryam dake zaune suka wuce, sukam binsu kawai sukayi da kallo

Sai bayan da yakai ta cikin mota sannan ya dawo yace maryam dan Allah kisa a share dakina mami tayi amai...bai ko jira ansar ta ba ya tafiyar shi

Su kam ikon Allah kawai suke kallo, maryam tayi murmushi tace ai bazai yuwu me aiki ta shiga dakin mijina ba, bari dai in tashi in share...

Fatima tace kam bala'i karuwa ma ta shiga balle me aiki? wallahi indai ina gidan nan baki sharan aman mami wallahi

Fatimar ce ta saka me aiki taje ta share Aman ta gyara wajen fess

A bangaren mami kuwa cikin ran ta tariga ta yanke hukuncin ita da zina har abada, ta yadda dai kam ta haifo shege indai hakan zai da Ahmad ya aure ta

Amma ta riga ta yanke hukunci kuma tayi nadama sosai akan zina, sai istigafari take ta yi sosai

An bata bed rest saboda yanayin jikin ta. Don haka ya kira yan uwanta ya fada masu cewa mami a asibity zata zauna har sai cikin ta yakai 5months

Ansha fada kam mai martaba kaman zai rasu akan bakinnciki, ta basu hakuri sosai sannan suka yafe mata

Ahmad kuma yayi alkawarin zai bata dukan kulawa sannan zaa daura masu aure ranar da duk ta haihu

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now