part 11

3.2K 180 5
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 11
Rakiyya bena

Ahmad kam sam baya wani jin banbancin akan zaa kawo amarya don ba tsarin shi bace ita kuma baida ma niyyar kusantar ta kaman yadda yasaba kusantar duk macen data gifta gabanshi

A ganin shi maryam tayi mashi kankanta sosai kamar kanwar shi Fatima yake gani dukda baima taba ganin ta dakyau ba sau daya ya taba ganin ta ma

Dakyar abokan shi su zaid da Ibrahim suka sa shi dole zuwa siyen baki yanata fada da cewa sam bazai je wadannan yaran su raina shi ba

Kaza suka siya da drinks na rakiyar ango, ba tare da ya sani ba sukayi spilling drink dinshi da maganin kara desire kaman yadda abokan ango keyi ma ango
***
Karfe 10 na dare

Su jamila, nasma tare da amarya maryam ne a kayataccen dakin da yaketa zuba kamshin dadi

Ango tare da rakiyar abokan sa suka shigo har dakin amarya tasha babban mayafi, dukda fuskan ta ba arufe take ba amma kanta a sunkuye yake don haka baa ganin fuskan ta

Sukayi sallama suka zauna, akayi barkwanci irin na abokan amarya da abokan ango dukda ba sosai ba saboda su kansu sun san kananan yara ne

A ransu suna kara tausaya ma maryam saboda sunsan Ahmad shege ne.. balle kuma sun yimai Hadi na musamman

Sauri sukayi sukace su nasma suzo a sauke su gida don sun san bomb din da suka hada

Ko rakiya Ahmed bai masu ba, Kamar koyaushe wayar ce a hannun shi

Ya dan daga kai ya kalli inda maryam ke dunkule a ranshi ya dan ja tsaki, ya zaayi amarya ta wani dunkule kanta cikin mayafi haka?

Ita dayakamata ace ta saka sleeping wears masu tada hankali asha amarci

Ba tare da ya kara kallon ta ba yace maryam ne sunan ki ko me? Ta dago kai ta kalle shi jin yadda yayi maganar watoh bai ma san sunan ta ba kenan yake nufi

Ba tare da ya kula ba yace, nasan an daura mana aure amma hakan bai sa kika zama mata ta ba, ki kiyaye duk abinda zan fada maki yanzu

Bana son kina shiga harka tah..
Karki yadda inyi abu gidannan ki nuna wai ke matata ce kinada rights akaina
Ba shiga daki na..
Ba ruwanki da baqi na, duk wanda zan kawo gidan nan bance kiyi magana ba
Bana cin abincin masu aiki.. na san mama zata dai bani abinci yanzu saboda ke don haka kisani dole ki man abinci safe Rana da kuma dare

Yana gama fadan haka ya Mike tsaye sannan yace, duk abinda kike bukata kina iya man magana, ban tsane ki ba amma bana son ki

Ki dauka kaman da yayanki ki kike zaune bana son raini don haka ki kiyaye, ya fice ba tare da jiran yaji abinda zata ce ba

Itakam maryam mamakin duniya ne ya cika ta, tapdi ta fada a ranta lallai inada aiki babba

Tashi tayi ta fada bandaki tayi wanka ta canza kaya zuwa doguwar rigar bacci maroon colour wadda ta fitar da hasken fatar ta sosai

Ta shafe jikin ta da turare sannan ta yi adduoin ta takwanta bacci abunta tare da tunani kala kala akan mijinta

A bangaren Ahmad kuwa yana shiga daki magani yafara aiki, gaba daya yashiga hayyacin sa

Ba abinda yakeso irin ya kasance da mace yana tsananin bukata, amma fa ai ba dai maryam ba don tayi mashi karama ko zai mutu yanzu bazai iya kula ta ba

Saida abun yakai mashi karo har yafara fita hayyacin shi ga ciwon mara daya addabe shi

Ya janyo waya yakira mami wadda take kwance tana tunanin wane hali masoyinta yake ciki dashi da amarya ta san Ahmad da yawan shaawa ta san bazai raga ma yarinyar nan ba

Ya yi amfani da matan banza ma balle matar sunnan shi balle taji anata fadan yarinyar kyakyawa ce

Tana cikin wannan tunanin sai ga kiranshi ya shigo wayar ta, hello mami pls kizo gida yanzu inada bukatar ki sosai, na baki 10mints

Ya kashe wayar ba tare da jiran abun da tace ba

Ta rasa ma me zatayi tunani? Ahmad bai taba kiranta harda ce mata pls yana shawwanta ba sai yau

Ba tareda tunanin komai ba taja mota sai gidan
Kai tsaye dakinshi ta shiga tare da rungume shi tana tambaya lafiya?

Haka ya rungumo ta yafara aika mata da sakwanni irin na ina bukatar ki

Itama ta mayar masa da martani suka shiga aikata alfashar su

Da safe bayan maryam ta gama sallah da karatun ta tafito dan shirya ma mijinta breakfast kaman yadda yayi umarni

Tayi mamakin ganin masu aikin har sun fara share share, tace dama nan kuka kwana amma? Sukace eh dama nan ne zamu rinka kwana ga dakin mu can suka nuna mata

Tashiga kitchen sanye da babban hijabin ta saboda kayan bacci ne a jikin ta

Kubra ce ta tayata aikin yayin da talatu ta zauna gyaran gidan saboda mutane da yawa da suka shigo kawo amarya jiya wajen ya lalace

Ta hada kayataccen breakfast ta jere a dining lokacin 10am ta kusa

Don haka taje tayi wanka kaman yadda mummy tace tarinka yin kwalliya da ado don jawo hankalin mijinta

Ta sanya jalabiya saboda taji ance yanason jalabiya

Bata damu da warning din da yabata ba zuwa kawai tayi ta zauna Kan dining tana jiran shi

Misalin 11am sai gashi yafito rungume da mami da niyyar raka ta wajen mota zata wuce gida

Sam baiyi tunanin haduwa da maryama ba a lokacin, tana zaune kan dining a babban falon da zasubi su wuce

Kallon ta suka tsaya yi da mamaki saboda gaba daya sun rude ganinta

Itama ta rude da ganin mijinta rungume da wata wadda batasan ko wace ba, mamaki yasa ta tsaya kallon su sororo

Shima kallon ta yakeyi suka kasa wucewa kokuma sakin juna

Maryam a ranta sai maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihirraji'un takeyi saboda yadda takeji a ranta

Mamakin duniya ya ishe ta ace daren farkon ta mijinta da wata ya kwana kuma a cikin gidan ta sannan kuma yafito a gaban ta rungume da ita...

A hankali ta furta ina kwana yaya Ahmad..

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now