part 30

4.2K 229 43
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 30
Raqiyya bena

Maryam tace mu ba wani event da zamuyi kinsan ustazai muke, fatima tace tabdi jam ai dole ku aje ustazancin ku mukam mu sha buki wallahi

Mummy tace gskya kam don bukin maryama ta dole ayi shagali
Maryam tace kai mummy harda ke? Mummy tace harda ni mana sai munyi shagalinmu gaskiya don bazamu yadda ayi aure shiru shiru ba

Maryam dariya kawai tayi don bata gaddama da mummy amma kam ita ba event din da takeson ayi sunfi son ayi walima kawai

Duk da dai taga alamar shima nabeel yana da son bidia

Ai Ahmad gaba daya mutuwar zaune yayi, sam baya da wani abun da yake jin dadin shi a lokacin

Gaba daya ya rasa duniya yake ko lahira
Shin dama haka so yake?

Tambayar da yayi ma kanshi kenan, tabbas indai haka so yake toh shi bai taba son kowa ba kenan

Har mami da yake ganin kamar yana son ta gskya baya sonta indai haka so yake

Ya tashi kamar kazar da kwai ya fashe ma a ciki yafita falon zuciyar shi na mashi zafi

Part dinshi ya koma ya kwanta yana maimaita kalmar inlillahi wa inna ilaihirraji'un

Nan take yaji zazzabi na neman rufe shi
Sai ya kira abokin shi doctor don ya bashi magani

Aunawar farko da aka ma BP dinshi ya hau sosai

Doctor yace meke faruwa haka abokina?

Kaga yadda BP dinka ya hau? Calm down pls karka sa kanka cikin wata matsala

Likitan dai ya bashi shawarwari sannan kuma ya rubuta mashi magunguna ya tafi

Haka fa Ahmad ya zama abun tausayi gaba daya ko makaranta baya zuwa saide ya saka wasu lectures sukayi taking over courses din da yakeyi

Kullum yana gaban Allah yana neman gafara da neman sauki

A gafarce ni pls zanci gaba something come up yanzu i have to stop it yanzu
Thanks

Duniyar tayi mashi kunci

Sam bai taba tunanin soyayyar wata yarinya zata sa yayi sanyi haka ba, shi ganin yake yanzu ko mace dubu aka samu bazasu burgeshi ba

Maryam kadai ce a ranshi ita yake so kamar ya mutu yakeji akanta

Bayan sati biyu

Ahmad ya ladabtu sosai don kuwa har mummy ta fara tausayin yadda ya koma

AUREN DOLE sabon SaloDonde viven las historias. Descúbrelo ahora