part 17

2.9K 218 12
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 17
Rakiyya bena

Am sorry readers kwana biyu banyi posting ba saboda bana jin dadi but Alhamdulillah am much better now

Ana saura sati daya bukin DR Ahmad da Safiyya, gaba daya duk wani shirye shirye an Gama shi, gobe ne ma zaa fara events din bukin

An kwashe furnitures din maryam ankai wani part cikin Gidan su Ahmad an gyara mata part daya ita bata ma san anayi ba

Haka dangin amarya sunzo sun kayata gidan safiyya da Hadaddun furnitures, duk da gidan ya hadu dama amma gyaran da aka mashi yanzu na musamman ne

Ahmad zaune tare da abokin shi zaid suna ta shirye shirye shirye akan Bridal shower din da zaayi gobe ma amarya wanda amaryar tace dole sai ango yazo dashi da abokan shi

Zaid yace nikam ban taba ganin ango yaje wannan event din ba

Ahmad yace nima fa ban taba gani ba saboda bukin Fatima ma cikin gida sukayi abinsu ita da friends dinta a bedroom dinta

Yace toh ta raina ka dole tace sai kazo ai😂 Ahmed yace ba ruwanka tayi ta raina ni din, zuwa dai ne sai munje

Zaid yace ah nikam idan naga Dama ina iya cewa ban zuwa kaine ya zama ma dole ai bani ba, sukayi dariya gaba daya

Washe gari
Haka akayi bridal shower a maiduguri a falon gidan su safiyya, ita da abokan ta 5 da kuma abokan Ahmad 5, abun yayi kyau har 3am suka kai suna ta rawa da abubuwa sannan kowa ya nufi kasaukin shi

The next day kuma KANURI Event ne akayi wanda suke kira wushe wushe, Kamar welcome ne akeyi domin Wushe wushe means welcome welcome, wanna event din anayin shi ne don welcoming bride ok groom into the kanuri family

Toh a wannan event din anyi welcoming Ahmad into safiyyas family as a son in law kenan

Amarya da ango sunsha kyau, safiyya ta saka lafaya da jewelries irin na kanuri tayi kyau sosai kaman ka sace ta ka gudu haka ango ya saka gizner dinshi da tasha aiki da malum malum, gashi anata kide kide irin na gargajiya abun dai sai wanda ya gani

The next day ya kama Thursday

A ranar akayi mothers night duk a nan maiduguri din, sai ranar yan uwan Ahmad sukaje don cewa sukayi su ba ruwan su da wannan kwanakin a maiduguri

Anyi buki na kece raini, balle harka da diyan manya, amarya da ango sunsha kyau, da ka gansu kasan suna cikin farin ciki kuma suna kaunar junan su

Su anty Aisha duk sunje bukin dasu Fatima, dukda gefe suka zauna suna kallon ikon Allah yadda Ahmad ke barin kudi, yayi likin kudi sunfi 1mil sannan ya baiwa mawaki Umar M Sharif kyautar mota kirar Corolla S

Ansha buki har kusan asuba sunata abu daya

The next day Friday akayi dinner

Dinner ma an kashe makudan kudade, tun daga decorations din zaka gane ba karamin kudi aka kashe ba 

An sha rawa ba amarya ba Ango, a abokan amarya haka suka saka ta tsakiya sukayi ta kwasar rawa

Amarya da ango ma harda competition din rawa sukayi wanda amaryar ta lashe😂

Ranar Asabar aka daura aure misalin 11am auren daya samu shaidu manya manya ciki harda shugaban kasar Nigeria da gwamnonin jihohi da dama tare da manyan yan kasuwa, UWA uba senatoci da ministoci

An daura auren safiyya da dr Ahmad akan sadaki naira million daya

Misalin 4pm jirgin su a sauka a babban filin jirgin Aminu kano inda motoci babu adadi sukazo taron su daga dangin ango da kuma abokan shi

Kai tsaye gidan su Ahmad aka kaishi suka tarbesu dakyau su anti zulaiha da basu tafi maiduguri ba da su anty babba sune suka tarbi amarya

Mummy tayi mata barka da zuwa tare da huduba akan ta zauna lafiya tare da kishiyoyin ta,  toh nan fa Kan safiyya ya daure don ita bata taba sanin Ahmad yanada mata ba balle har ace kishiyoyi, hakan na nufin ba ma kishiya guda ba kenan?

Bayan sallar isha'i aka raka amarya dakin mijinta, kayatatten gidan dayasha kayan alfarma

Da misalin goma na dare kuma aka shirya zuwa wajen dinner

Waihh ai a maiduguri baayi komai ba

Lallai naira na aiki, Allah ne kadai yasan millions din da aka kashe wajen decorating hall din kawai

An gayyato manyan mawaka su davido da sauran mawakan hausa Dana turanci zuwa wajen dinner din

Amarya ta saka farar wedding gown yayin da ango ya saka black yadi me shegen kyau

Sunyi kyau kaman ka sace su ka gudu

Sai kusan 5am aka tashi dinner kowa ya wuce sai amarya da ango da abokan amarya suka koma gidan ta suka kwanta baccin gajiya

Safiyya kam ai harda mafarkin maganar kishiyoyin da aka mata tayi. Saboda duk duniya idan akwai abinda ta tsana toh shine kishiya

Gajiya ne da taron jamaa yasa bata samu yi mashi magana ba

Washe gari sai kusan 2pm suka farka mummy ta turo a fada masu zaayi walima

Ai daga amarya har ango tirjewa sukayi sukace sun gaji su ba dole sunje ba zaayi walima ai addua ce ko ina suke zaayi masu

Haka kuwa akayi walima amma ba amarya ba ango

A ranar lahadi da dare abokan ango suka raka ango dakin amaryar shi

Barkwanci babu kalar wanda baayi ba, sannan suka yi sayan baki 2.5 mil dayake yammatan amaryar 5 ne aka ba kowace 500k

Toh yanzu fa an watse Anbar amarya da ango daga su sai halayen su zasu zauna

Bayan ya dawo raka abokan shi ya shigo dakin da sallama a lokacin har ta yaye mayafin da aka rufe mata fuska ta zauna tana jiran yadda zata fara tambayar shi akan kishiyoyin da taji maman shi ta fadi?

Ya shigo da murmushi yana fadin amaryar ango

Wani wawan kallo ta aika mashi dashi wanda shi kanshi abun ya bashi mamaki dukda ya lura tunda sukazo kano kaman bata cika sake mashi ba kaman lokacin suna maiduguri toh shikam me yayi?

Ya zauna tare da janyo ta yana fadin amarya Tah lafiya dai ko? Na san still akwai gajiya amma dole mu more this night kam ya fada da tsokana

Ture shi tayi da janye jikin ta tace me mamar ka ke nufi da inyi hakuri da kishiyoyi na? Kanada aure ne Ahmad baka taba fada man ba?

Kallon ta yayi da mamaki. Wai ita bata san yanada aure ba? Ya tsaya yana nazari lallai kuwa fa bai taba fada mata ba don shi kanshi mantawa yakeyi da auren

Ya dan saukar da ajiyar zuciya yace eh inada aure amma... wani mikewa tsaye tayi cikin zafin nama amma me? Har mata biyu kenan kake da ko? Yace no dayan ban aure ta ba tukunna sai ta haihu....

Wani irin kallon mamaki ta mashi, bai aureta ba tukunna amma aurenta zaiyi kenan yake nufi? Tapdi jam lallai akwai aiki kenan dan ita wallahi bazata zauna da kishiya ba wadda ta isko ma balle ayi maganar wata zata isko ta...

Pls comment
Vote and like

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now