part 33

2.6K 150 4
                                    

Auren dole sabon salo
Part 33
Raqiyya bena

A office din dr haidar maryam ta zauna kanta a kasa hawaye na zuba a idon ta

Dr yaja numfashi sannan yace ya kuke da patient dina?

Tace ex husband dina ne. ... a takaice tayi maganar

Kanshi ya daure don shi baima san ta taba aure ba

Yace do u love him? No kawai tace..

Yaja numfashi yace why are u here then? U r supposed to be celebrating your wedding by now

Ta danyi shiru sannan tace he is my brother gidan mu daya... daddynshi ne ma zai bada aure na

Kanshi ya kara daurewa

Yace well Dr this is about life and death

Maganar gskya its either ki auri Ahmad or sincerely we r going to loose him

Da sauri ta kalli dr

Yace yes kinga daga farkawa ya kara samun attack. Even now zai iya kara samun wani idan ya farka

We can't keep him unconscious forever kuma ko?

Ta dan numfasa tace I'll think about it kawai ta tashi ta wuce

San batajin tana son auren Ahmad again

Nan ta fara tuna aurenta dashi

First night dinsu wata ya kawo yayi zinah da ita a gidan

Ya auri mata har biyu bayan ita

Tana shekaru bata ganshi ba sam baya tuna yanada wata mata wai ita maryam

Ta numfasa bayan ta tuna yadda ya sake ta ta waya bayan sun kusan shekara biyu basu hadu ba a lokacin

Saida ya ganta yaga ta cika mace zaice yana son ta? Soyayya ko shaawa?

Lokaci daya kuna ta tuna da mummy

Gabanta ya fadi rasss

A ranta tace nasan duk son da mummy take min tafi son yaya Ahmad akaina don shine ta haifa

Idan har ban masu halaccin ceto dansu ba shekaru biyar da suka yi suna bani ingantaciyar rayuwa miye zata saka masu dashi ?

Indai yaya Ahmad ya mutu akan ban aureshi ba wallahi su daddy zasu daina so na ne

Gara ma mummy amma na san yadda daddy ke mugun son yaya Ahmad

Nabeel ta tuna da yaranshi sai kuma ta fashe da kuka

Kanta yayi zafi ta rasa dawa zatayi shawara

Amal ce kawai yar uwarta ta jini a duniya wadda take iya gayama irin wannan matsalar a yanxu don haka ta kira ta tace sister i need your help please

Gida ta nufa ta daura alwala tayi sallah tayi nafila sannan ta roki Allah ya zaba mata abinda yafi alheri a rayuwar ta

Ta dan samu natsuwa kadan sannan ta zauna taci abincin dare

Kusan karfe sha biyu ne lokacin don haka tana gamawa kwanciya kawai tayi

Misalin 9am ta tashi bayan ta koma sallar asuba

Ko 20mints batayi da tashi ba dai ga amal tazo

Suka zauna neman mafita

Amal tace sister gskya yakamata yayi ki auri yaya Ahmad don shine kawai abinda zakiyi ki dan saka ma iyayenshi da yan uwanshi soyayyar da suka baki tsawon shekaru

Ki duba komai baku hada ba na jini haka suka aura ma dansu baya so

Suka rike ki duk shekarun nan suka baki ilimi. Sukayi fushi da dansu akanki

Haba karma kiyi tunanin wani nabeel yaushe kika sanshi? Bakida kamar mummy da daddy a duniyar nan hadda mu da muke yan uwanki kuwa

Ki daure ki faranta masu rai maryam

Tabbas maryam ta san batada kaman mummy da daddy sukuma basuda kaman Ahmad don haka ta yanke shawarar auren Ahmad

Ta kira nabeel tace tana son ganin shi

Nabeel shima tunda yaji abinda yake faruwa yayi niyyan bata shawara su hakura da juna ta auri Ahmad domin yima mahaifan shi hallacci

Taji dadin yadda ya anshi maganar ta kuma yamata addua

Saide ya roke ta akan ta hada shi da amal idan akwai dama domin yaran shi yaga sun shaku da ita

Yana son ya samar ma yaranshi uwa ta gari

Taji dadin maganar dukda ita kanta tasan tana son nabeel tayi ma amal murna kuwa idan ta samu nabeel domin namiji ne mai kirki da sanin yakamata

A ranta tace halin amal na kwarai ne dole ta samu miji kaman nabeel

Sai kuma wata zuciyar tace ke halinki na banza ne da kika samu irin Ahmad? Kowa dai da qaddarar rayuwar shi

A dakin daddy...

Wallahil azeem saide a bayan raina zan aurar da maryam ga wani bayan Ahmad

Mummy tace haba alhaji ita shin maryam kayan wasa ce da zamu rinka wasa da rayuwar ta? Mutun ce kaman kowa

Shekara nawa tana zaune da ahmad a rayuwar kunci

Ganin kake duk gatan da muka bata yakai wanda mijinta zai bata amma ahmad ya zauna zinace zinace da walakanta ta

Haba alhaji na karka bata rawarka da tsalle mana

Ladar da muka samu wajen ceto rayuwar maryam zata lallace idan muka ce sai mun aura mata Ahmad dole yanzu
Munyi mata auren dole a karo na farko don Allah ka batta ta auri wanda takeso

Ko ta auri ahmad indai kwanan shi ya kare to tabbas sai ya mutu

Ribar me zamu samu idan muka tilasta ta komawa inda ta fito? Haba alhaji na

Jikin daddy ya dan yi sanyi amma sam baijin zai iya daura auren maryam da wani don haka yace shikenan hajiya ba damuwa maryam ta auri duk wanda takeso amma zan kira kawunta ya daura mata aure nidai bazan iya ba gskya

Shiru kawai mummy tayi don tasan zafin halin da Ahmad yake ciki ne yasa daddy yake wadannan maganganu

Su fito da niyyan zuwa asibiti maryam ita kuma sun gama magana kenan da nabeel zai wuce

Mummy kanta bataji dadin ganinsu ba sai taga kaman maryam bata damu da halin da dansu yake ciki ba sai kuma ta batsar

Balle daddy da ko kallon su baiyi ba

Bayan nabeel ya gaishe su ya wuce sai maryam tace mummy zan biku asibity

Okay kawai mummy tace

Daddy na jaye da motar mummy na gefe sai maryam a baya

Maryam tace mummy inada magana ppls

Taci gaba da cewa yanzu muka gama magana da nabeel
Sai kuma tayi shiru

Duk sun dauka cewa zatayi akan yaushe zaayi auren ne

Daddy har ya shirya ansar bata akan taje kawunta ya daura mata aure

Sai kawai tace mun hakura da juna na bashi hakuri saboda inason in auri yaya Ahmad don ceto rayuwar shi...
Da sauri daddy ya juyo ya kalli maryam

Mummy ma kallon ta tayi

Sunji dadi sosai daddy sai sanya mata albarka suke

Mummy tace lallai maryam kin cika yar halak. Allah ya saka maki da aljanna kuma ya baki yaya masu maki biyayya  kuma ya sa karkiyi dana sanin wannan  hukuncin naki

Ta ansa da Ameen

Taji dadi sosai yadda ta sanya su daddy farin ciki

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now