part 26

3.3K 182 6
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 26
Raqiyya bena

Mummy ta kalli Ahmad fuska daure tace ka sake ta? A maraice yace no mummy ban sake ta ba

Mummy ta kalli maryam tace yaushe ya sake ki? Maryam ta cire wayarta ta gwada ma mummy message din

Kallon shi tayi fuska daure tace shine don ka raina ni zakazo kana ce min wai wani bai saku ba? Saki ko ya saku tunda har kayi shi yanzu inhar maida maryam zakayi saide in ta amince

Tashi kawai tayi ta wuce maryam tabi bayan ta

Ahmad kuwa zaunawa yayi yana maimaita kalmar innalillahi wa inna ilaihirraji'un

Zuciyar shi sai tafarfasa takeyi

Surar maryam kawai ke dawo masa a rai

Ya san yana ganin hadaddun mata yana muamala dasu amma maryam daban ce

Meyasa bai kula ba sai yanzu?

A cikin zuciyar shi kuwa yayi alkawalin ko ta wane hali sai ya mayar da maryam matar shi

Ya rasa gane son ta ne yakeyi ko shaawar ta?

Mummy ta kalli maryam tace, karki damu maryama kinji? Kina gama idda kika samu mijin ki aure zamuyi maki

Ahmad ba alkhairi bane a gareki tunda kinka ga haka ta faru

Na tabbata maryam insha Allah zakiji dadin rayuwa zuwa gaba zaki samu wanda ke sonki kema kina son shi kiyi auren ki

Mukuma kici gaba da daukar mu iyayen ki

Maryam sam bata san me keyi mata dadi ba, wani son Ahmad ke ziyartar ta a lokacin

Gaba daya kalaman mummy basu ma shigar ta

Yanayin Ahmad kawai take tunawa

A fili kuwa sai tace ma mummy toh nagode mummy Allah ya saka da alkhairi

Ta shiga dakin ta tarufe kofa ta zauna tana tunanin yadda zata fara rayuwar ta a yanzu da batada aure

Tun lokacin da tasan kan ta a kuntace rayuwar ta ta taso

Saurayi daya ta taba yi a rayuwar ta kuma aka raba ta dashi karfi da yaji

Koda aka mata aure kuma ta samu yanci harda zuwa makaranta amma batada freedom na koda magana da saurayi ne saboda tana da aure

Shiru tayi kawai ta koma ta kwanta tana nazarin yadda tayuwar ta ta kasance

A bangaren Ahmad kuma

Tunda ya fita daga falon ya shiga part dinshi inda Aish take da me kula da ita ya rungume ta jikin shi yana faman sauke numfashi sannu sannu

Aish cikin gwalancin ta tace dada ina chokulet ina? Dayake dada take kiran shi

Ya dago jajayen idanun shi ya kalli Aish, mami ya tuna da ita

Mami ce kawai macen da ya zauna da ita tana son shi tsakani da Allah shima yana son ta

Ya tuna safiyya da yaso sosai amma ta walakanta shi sam ko labarin ta bai kara ji ba

Maryam ko chance din zama cikin rayuwar shi bai bata ba fiye da shekara biyar da auren su amma ko maganar minti biyar bai taba yi da ita ba

Yanzu kuma lokaci daya kawai yace ya sake ta

Wata zuciyar tace kuma gashinan ka kamu da son ta..

Yayi saurin karyata zuciyar shi da cewa shaawar ta dai nakeji... bana son ta mami kawai da Aish nakeso..

Kukan Aish ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya fada

Ya kalli Aish yace lafiya Aish? Kuka kawa taci gaba da yi

Shi sam bai san tayi ta mai magaba ba baya jin ta saboda ya fada duniyar tunani...

Yace oya sorry baby I'll get you chocolate kinji? Ta dan yi shiru sannan tace i will go with u dada

Haka ya dauki diyar sa ya kama hanyar fita gidan

Suka yi shopping dinsu ya dawo ya aje ta wajen mummy sannan ya tafi zuwa wajen sabuwar budurwar shi zeee zeee wadda suke sheke ayarsu a yanxu

Shin ina su anty saratu

Sun dade suna kashe kudi akan Ahmad ya auri zee zee amma inaa

Sun dai samu sun tura ta yana zaman iskanci da ita don shi sam bai ma san ta hada wani abu da maryam ba....

AUREN DOLE sabon SaloTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon