part 20

3.3K 187 2
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 20
Rakiyya bena

Ya fito daga cikin mota waya rike a hannun sa, kyakyawar fuskar shi dauke da faraa

Kai tsaye babban falon gidan ya shiga inda mommy ke zaune suna fira tare da maryam da su anty zulaiha, tun da maryam ta zo Abuja bai shigo gidan ba yau kwanan ta uku sai yau

Yayi sallama dauke da faraa yanata washe baki, Dukan su kallon shi sukeyi mummy tace lafiya dai ko kake faman wangale baki? Ba ko kunya cikin tsananin nuna farin cikin shi yace mummy Mami ce ta haihu

Gaban maryam yayi wani irin dukan uku uku,  ta daga kai ta kalle shi tana kara mamakin rashin kunya irin na Ahmad

Shi sam baya kunyar abun kunya

Ace don an Haifa maka shege ne kake rawar jiki haka?

Mummy tace masha Allah toh Allah ya raya me aka samu? Yace Baby girl ce

Anty zulaiha kam ko kallon banza bai ishe ta ba, ace gaban maryam yake fadin an Haifa masa dan shege wanda kowa ya san da cikin nan sai bayan auren su aka same shi

Shi kam a zahiri bai ma lura da maryam ba, ya bude picture din baby da aka tura mashi yazo yana gwada ma mummy

Mummy ta amsa ta kalla tare da kara cewa toh Allah ya raya

Ya tashi jiki na rawa yace zanje in ga baby, maryam sai a lokacin da saukar da ajiyar zuciya tace Allah ya raya yaya Ahmad

Sassanyar muryar ta yasaka shi tsayawa Cak ya juyo don ganin wacece, gabanshi yayi mumunan faduwa lokacin da ya kalli maryam

Shi sam bai ma gane ta ba kallo daya saida yayi nazari

Kallon mamaki ya tsaya yimata, wai wannan kwailar ce ta canza haka? Yayi saurin danne zuciyar sa dake masa dukan uku uku tare da kawar da kanshi ya tafi ba tare da ya ansa ba

Ita kam ran ta ya sosu kwarai amma mommy ta janyo fira don kwantar mata da hankali

Mummy tace duk abinda yakeyi ki bar saka bakin ki kinji maryam dita? Ki rinka kyale shi

Zai yi hankali nan gaba

Ko ina bai tsaya ba sai asibity wajen mami, tana kwance tana bacci saboda ta wahala sosai

Ya duka ya dauki baby dake kwance Kan gadon babies dake dakin

Yace masha Allah Allah ya raya man ke, muryar shi ta sa mami bude ido a hankali tana kallon shi, duk duniya batada abinda takeso irin Ahmad

Wani sanyi taji ganin shi da tayi, a hankali ta fara kokarin tashi zaune ya matso yana ce mata sannu mami

Ta kalle shi yadda yake rungume da jaririyar kamar yar sunna yadda yake murna

Hawaye ya silalo mata a ido tana kallon shi taji tana wani irin mugun son shi kamar ta kuwwata

Yace thank you mami for this beautiful gift nagode sosai, tace saura alkawarin mu Ahmad

Ya zauna gefen gadon tare da janyo hannun ta yana kallon ta cikin ido, yace mami insha Allah gobe zaa daura mana aure, I can't wait to make the mother of my child my wife..

Bazan iya saka diyata ta tashi separately da baban ta ko maman ta ba, I want her to have a complete family

Wani dadi taji ya ziyarci zuciyar ta, tace thank you very much Ahmad

Hakan kuwa akayi

Washe gari da safe misalin karfe 10 na safe aka daura auren Ahmad da Maryam(mami) a Kan sadaki naira dubu dari

Daurin auren bai samu babban taro ba mutanen cikin gidan kawai suka daura, inda sarki ya baiwa kanen shi mahaifin Ahmed auren

Murna a wajen mami baa cewa komai kamar ta zuba ruwa kasa ta sha, ta dade tana jiran wannan ranar

A ranta take cewa inda ta san sanadiyar haihuwar zata aureshi ai da bata zubar da cikin ba last time

Amma koma miye ta gode ma Allah da ya sa ta auri muradin ta

Toh amma ana wata ga wata domin kuwa yar gaban goshin Ahmad ta saka shi gaba akan sai ya sake ta don bazata zauna dashi ba

Shikuma sai lallashin ta yakeyi shi kam yana matukar ji da ita

Ya rungume ta yace haba wifey kema kinsan bazan iya sakin ki ba ko? Kinsan yadda nake ji dake, na fada maki mami ba nan zata zauna ba a gidanmu zasu zauna in da maryam take kuma kinsan dai ban taba rashin kwana gidan nan ba tun da maryam ta dawo haka ko yanzu I'll always be here with u

Maryam matar iyayena ce, mami kuma mamar diyata ce, kece kawai mata ta sai yadda kikayi dani

U promise? Ta fada tana kallon shi, yace I promise u naki ne ke kadai bani ba wata sai ke kadai

Sai a lokacin da dan hakura duk da sai da ta kafa mashi sharuda babu adadi, ciki har da rashin ansa kiran kowace cikin su a cikin gidan ta sai in yafita can kuma bai isa ya kwana ba gidan ba

Sam bata san Ahmad ko dan iska yafita zama ba tunda ko da auren nasu ba daina muamala yayi da matan waje ba balle mami da ya saba da ita sosai kuma yana missing dinta

Shi Kan shi ya san yayi hakuri watanni bai kusanci mami ba don ya riga ya saba da ita, yanzu ma hakuri zaiyi kawai ta gama jinin haihuwa

Wannan kenan

Shin ina su anty saratu?

Anty saratu kam hankali ya kwanta tun da ta gane cewa mijin maryam ba ruwanshi da ita har ma yayi aure abun shi

Duk hotunan auren shi zee ta gwada mata su wanda sukayi ta gani a Instagram suna ta murna, yanzu kawai kokarin da sukeyi su samu yadda zasuyi su sa a sake ta

Amal kuwa ta gama makarantar har ta fara aiki, ta hadu da wani likita dr sameer a asibitin da take aiki kuma ya nuna yana raayin ta

Saide babansu yace bazaayi mata aure ba sai lokaci daya da zee tunda itace babba don haka ana nan ana jiran zee ta samu mijin aure

Anty saratu a gaban boka tana bashi complain akan rashin samun mijin zee har yanzu, boka yace kar ta damu zaa samu miji bada jimawa ba, anty saratu tace yawwa boka maganar maryam har yanzu fa shiru baa sako ta ba

Boka yace kullum tana dauke da Qur'an tana karantawa shiyasa aikin mu bayayi amma mijin ta a sake yake don haka zan bada magani a tabbatar mijin ya shaki kamshin shi tabbas zai sake ta,

Anty saratu tace ni idan son samu ne ma inason idan ya saki maryam ya auri zee mana, boka yace toh zaa iya aiki amma sai kin bada Rabin million

Tunani tayi kafin tace toh shikenan zan kawo bada jimawa ba boka ka bani sati biyu

Bayan anty saratu ta koma gida ta zaunar da zee tace toh fa zee zama bai gan ki ba, suger daddies dinnan naki dole ki samu ki anso 500k  ko ta halin kaka saboda boka yace zaa bada 500k don son nakeyi idan anyi aiki mijin maryam ya sake ta ya aure ki

Wani tsalle zee ta daka sannan tace mummy bakisan yadda nake admiring mijin nan na maryam ba, cute guy wlhy dole ne in samo 500k dinnan.....

Vote
Comment
And like

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now