part 2

4.8K 220 1
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 2
Rakiyya bena

Ahmad Kokuma ince dr Ahmad, kyakyawan saurayi ne ajin karshe wanda kafin a samu saurayi kyakyawa irinshi toh sai anyi dogon binciki, fari tas tas tas, farin shi yana kama da yanayin farin turawa idan ka ganshi bazaka ce bahaushe bane Sam, toh saide ai yanada jinin larabawa domin kuwa kakar shi ta wajen ubanshi balaraba ce

Yayi karatun sa a bangaren education domin shi ba abinda ke burge shi irin koyarwa, yana son lecturing sosai tun yana yaro abun ke burge shi har ya tashi da wannan raayin

Iyayen shi masu arzikin gaske kuma baban shi dan Sarauta ne, yayan mahaifin shi ne sarkin garin

Kakanshi sarki ne wanda ya auro balarabiya hakan yasa duk diyanta Suke kaman larabawa domin baban dr Ahmad kaman balarabe yake shima dr Ahmad din har sai yafi babanshi kala da larabawan

Mahaifiyar dr Ahmad itama kanuri ce yar maiduguri kyakyawar gaske hakan yasa dr Ahmad sai yafito wani irin kyakyawar hallita

Dr Ahmad ba likita bane, yayi karatu me zurfi har yazama dr na PHD kuma yana Kan hanyar zama professor

Ya fara lecturing a federal university dake garin Kano kafin daga baya ya bude private university me suna al ihsan university a nan garin kano wadda ake biyan makudan kudade domin shigar ta

Dukda shine yakeda makarantar bai hana shi lecturing ba saboda yana son karantarwa kuma yana jin dadin karantar wa

Kyakyawan saurayi a matsayin lecturer hmmm yakuke gani?

Dr Ahmad ya kasance cikin irin mazan nan da basu dauki mace da daraja ba, ya dauki mace kaman sex toy, sam baya kai kanshi ga mace don kuwa akwai ya'yan manya dayawa da ke kawo kansu wajen shi shikuma kawai abinda ke gabanshi shine ya kusance su

Sam Dr Ahmad bai taba soyayya ba, iyaka idan mace ta nuna tana son shi xai kulata har zuwa lokacin da yabiya bukatar shi ya rabu da ita

Dr Ahmad ya kasance me taurin kai, wayayye ne sosai a fannin rayuwa saboda yayi karatu yanada ilimi ya shiga kasashe daban daban amma bai dauki mace a matsayin abokiyar rayuwa ba

Ya dauki mace a matsayin abinda zai kashe shaawar shi kawai, saboda dr Ahmad yanada yawan shaawa sosai

Idan kaga yadda yake walakanta yammatan da yayi amfani dasu Sam bazaka taba tunanin ko magana ta taba hadasu ba balle har wata tarayya ta daban

Amma hakan bai hana yammatan sun daina binshi ba da yawa jin kanshi ke sa suna binshi abinda ke burge su kenan

Yammatan makarantar shi ma da yawan su binshi sukeyi kuma shi kam indai yarinya ta hadu ta kawo kanta sai ya kwanta da ita

Amma yanada taste din yammata sosai don kuwa idan ba mace da ta amsa sunan ta ba baya kula ta, yana shawar mace me kwalisa da wayewa shi kyau bai ma cika burge shi ba saide wayewar mace ko don yasaba ganin kyau ne saboda kannen shi mata ai kyawawa ne sosai

Wannan kenan
****

Maryam ce ke ta faman gugar kayan da ta wanke da safe tanata faman tari saboda sanyin da tasha kuma dama ita sam bata kaunar sanyi

Anty ta shigo dakin tana kallon ta a lalace tace ke dan ubanki har yanzu gugar nan baki gama ta ba? Maryam tace anty wlh inata kokari cikin tsawa anty tace ke dallah yi man shiru yar rainin wayo kin iya maida magana kaman kinayi da warin ki

Anty ta duba wayar ta karfe 6 na yamma ta kalli maryam tace zan fita zuwa wajen dinner karfe 9 don haka ki shirya tare zamuje saboda dinner ce ta manyan mata mafi yawanci zasuje da mai aikin su don rike jaka dole ki shirya muje ki rike man jaka ki jiramu waje har a tashi

Anti tayi hakan ne don ta gallazawa maryam saboda ta san maryam bata shiri da sanyi ko kadan don haka in sun tafi zata barta waje don ta wahala kuma babu ita ba baccin dare da wuri dama wajen baccin daren ne take samun hutu

Maryam tace anty kinsan fa ina mura gashi kuma.... wani wawan mari anty takai mata tareda cewa ke dan ubanki kin isa inyi magana ki tsallake magana ta? Harda maida man magana

Idan kin haihu ga uwarki da ubanki ki bari 9 tayi baki gama gugar nan kin shirya ba kiga abinda zai faru dake

Uncle yashigo yace lafiya nake jin muryan ki tun waje? Anti tace wai yar rainin wayon nan ce nace zata rakani dinner wai sanyi a akwai kuma mura take..uncle ya kalli maryam cikin tsana yace ke kin raina mutane ko? Tsaki kawai yayi tareda fadin toh karki raka ta kinji? Ya wuce abunshi

Maryam kam Allah kadai ya san abinda takeji a ranta amma Sam hawaye basu fita daga idonta no matter how much she try

9:00pm
Anty ta fito daga dakinta sanye da wani hadadden leshi wanda kudin shi zasu kai 35k

Anti dama akwai son karya shiyasa duk abinda ta tara wajen sutura yake karewa don kuwa abokanta duk matan manya ne dakuma manyan matan kansu, itama headmistress ce ta wata primary kusa da unguwar su

Dakin maryam ta shiga rai a bace tana faman fada yadda maryam taki fitowa kafin 9pm

Kwance ta iske ta tana rawar sanyi ta hankado ta da karfi cikin zafin rai tana fadin ke dan ubanki da nace ki shirya mu fita kin shiryawa kikayi?

Cikin muryar ta shakakiyya tace anty wlh banda lafiya sanyi... janyo ta tayi rai a bace tana fadin yau wallahi ko gawar ki ce sai naje da ita dinner

Haka maryam ta sanya hijabi jiki na rawa tana faman numfashi saboda hancin ta daya toshe

Al ihsan event center kano
Wani tsararre kuma hadadden wajen buki ne a garin Kano wanda ainifin shi mallakar dr Ahmad ne

Duk wasu masu ji da kansu nan suke buki idan sun tashi

Motar anty tayi parking jikin jerin manya manyan motocin dake wajen duk wajen babu motar rainawa dai ta anty domin 206 ce d ita

Maryam ta fito kaman zata fadi saboda sanyin da takeji har cikin qashin ta ga wajen da shuke shuke itace duk sanyi yayi yawa a wajen

Anty ta kalle ta a walakance tare da mika mata karamar wayar ta da hand bag dinta tace duk lokacin dana kiraki kizo bakin kofa ki kawo min hand bag saboda bazaa bari ki shiga ba

Maryam dai rakube wa tayi gefen motar sanyi na shigar ta saboda anty ta rufe motar ta tawuce da key

10:00pm
Hall din yacika makil da manyan mutane domin dinner ce akeyi ta auren Fatima bashir dikko, Qanwa a wajen Ahmad bashir dikko family sarauta ga naira? Can u imagine yadda dinner zata kasance? Duk wani mai fada aji a garin yana wajen harda sarki da governor duk sun Hallaro

Amarya da ango suka shigo aka fara gudanar da shagalulukan buki cike da burgewa komai na manyan mutane da wayayyu akeyi

Asp Usman tsaye wajen filin parking yana waya sai yaji nishi a bayanshi kaman wani na faman numfashi

Ya juya don ganin wanda ke wannan numfashi sai ya hango ta lunkume jikin tire mota tana rawar sanyi

Ya isa wajen tareda haska fitilar Qatar shi ya ganta ta nannade cikin hijab din ta sai kukan zuci takeyi don kuwa ta dade rabon da tayi hawaye

Hannu yasa ya dago ta
Wa iyazu billah. Wani zafi yaji jikinta yayi kamar garwashi gashi duk jikinta ya mutu saboda ta galabaita

Miye sunanki ya furta yana kallon ta, sam muryanta bata fita ya gane hakan ne saboda kokarin ta na fada mashi sunan ta amma muryan ta na a shake

Rika ta yayi ba tare da yace komai ba ya saka ta a mota yana fadin ki kwantar da hankalin ki bazan cutar dake ba asibity zan kaiki

11:25
A asibity aka kwantar da ita tareda bata taimakon gaggawa saboda tariga ta jigata sosai nan take bacci ya dauke ta asp Usman ya zauna yana kallon kyakyawar fuskar ta tare da yin nazaruruka masu yawa kafin daga baya ya dauki wayar daya gani a hannun ta don kiran family dinta...

AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now