part 5

3.2K 168 0
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 5
Rakiyya bena

Amal ta taya maryam har suka gama dafa indomie din sunata labari

Anty ta shigo kitchen ta isko amal na taya maryam amma sai sunyi hakuri da amal har ta wuce dole sai ta kama ma maryam aiki

Ita amal kamar tafison maryam akan yan uwanta uwa daya uba daya

Sukuma iyayenta sunfi sonta akan duka diyan shiyasa duk abinda takeso suke kyale ta amma basu ma son tazo hutu saboda tana hanasu azabtar da maryam yadda sukeso

Dayake a school of nursing duk hutun ta bai wuce sati daya in tazo ta koma

Yanzu ma aminiyar ta ce zatayi aure shiyasa tazo bukin ta kwana biyu zatayi ran Monday zata koma

A ranar maryam ta samu saukin azabtarwa tasha magungunan ta ta kwanta bayan sunyi labari da amal
***

Washe gari
Tun da safe kaman kullum aka tada maryam don yin wanke wanke da share share

Amal bacci take don haka maryam ce kawai tayi wanke wanken da shara ta fara fete Irish sai ga amal ta fito itama da dauki wuka suka kama tare

Ta lura maryam dakyar tana numfashi alamun sanyin na damun ta gashi dama ba lafiya gare ta ba

Amal tace sis kije daki har sanyin nan ya rage mana bari kawai in gama aikin

Maryam tace no sis bari kawai ai naji sauki I can manage

A haka dai suka gama hada breakfast

**
Dr Ahmad a dakin maman shi suna fira mummy tace kaikam kaji kunya wlh yanzu baka jin kunya harda Fatima da ke 18years tayi aure ta barka

Dariya yayi yace haba mummy miye ne wani abun kunya ai ita mace ce

Mummy tace wlh Ahmad dole in maka AUREN DOLE dariya yayi yace AUREN DOLE fa kikace mum kamar wani mace

Mummy tace ai 1month ka bani kace in maka aure

Ahmad yace ok no problem nidai make sure she's beautiful and me hakuri, yafada yana dariya

Salamatu me aiki tashigo dakin tace hajiya kinyi baki Amal ce abokiyar hafsatu

Murmushi mummy tayi tace Allah sarki amal ai na dauka bazata zo sallama ta ba tunda aminiyar ta tayi aure

Ahmad yace ai Amal da Hafsa kam suna ji da junan su

Mummy tace ai gashi har mun kulla xumunci da iyayen ta ko shekaranjiya maman ta tazo dinner din hafsatu

Ahmad yace ai banga Amal ba wajen dinner na dauka ai batazo bukin ba kinsan halin school dinsu

Mummy ta tashi tana dariya tace tapdi ai kam amal ba abinda zai hanata zuwa bukin hafsatu ranar dinner din ai abokan ta dayawa basuzo ba saboda sunata shirin bridal shower din da sukayi after dinner cikin dare..

Mummy ta iske Amal zaune falo tareda maryam zaune kan kujera

Mummy tace ah amal sannu da zuwa

Suka gaisa amal tace mummy wai sako zan daukar ma hafsatu dakin ta..

Dariya mummy Tayi tace aww ni da dauka kinzo sallama ta ne tunda gobe zaki koma ashe da abinda ya kawo ki

Amal tayi dariya tace mummy kiyi hakuri dole zan dawo ai

Mummy ta kalli maryam dake sunkuyar da kai tunda suka shigo, tace amal wannan fa? Amal tace cousin dita ce da tadawo gidanmu two years ago, tunda ta dawo gidanmu na koma sokoto shiyasa bamu taba zuwa ba sai yau nace tazo ta rakani gidan hafsatu shine ta aiko mu nan

Mummy kam kyaun maryam da natsuwar ta yatafi da hankalin ta, ta san diyan ta kyakyawa ne amma kam maryam daban ce ga kuma natsuwa sosai a tatare da ita

Nan take ta yanke hukuncin bibiyar halayen maryam don kuwa ta samar ma Ahmad mata
Toh fa

Ahmad ya sauko dakin mummy zai fita gidan..suka gaishe shi ya ANSA da sakin fuska yana tambayar amal ya karatu sam bai ma ga maryam ba ya fice abinshi
Suka dauki abinda zasu dauka suka wuce gidan hafsat inda suka wuni sai yamma sukayi sallama da aminiyar Tata sannan suka wuce gida tare da mata fatan zama lafiya

Bayan sati daya

Wanki ne maryam ke ta yi tun asuba har yanzu kusan sha biyu na rana

Mura kam kamar koyaushe sanyi ya kamata sosai sai rawar sanyi take, don tunda Amal ta wuce wani sabon gallazawa ya tashi

Gashi tana multi tasking
Wanki takeyi tareda girki saboda ba wanda zaiyi abincin rana idan ba ita ba

Ta gama wankin da kyar jikinta sai rawa yake ga yunwa ga aiki

Tunani guda takeyi Allah yasa ta gama aikin ta duka kafin sanyin idaniyan ta yazo
Tun sati daya daya wuce ASP Usman kullum sai yazo zance wajen Maryam duk da basu so amma tsoron suke ya gane gallazawa da suke mata ya kama su gashi wata rana ma da uniform yake zuwa fira
Ya fada ma maryam AUREN ta yakeson yi, tsaf ya lura ba dadin gidan takeji ba don haka ya shirya tsaf don AUREN ta cikin kankanin lokaci

Ta gama girki da wankin gaba daya saida ta tabbatar da tagama komai sannan ta tashi ta shirya tayi wanka ta fesa turaren da usman ya kawo mata

Anty tazo ta ganta zaune waje tana jiran shi tsuki taja tare da fadin anji kunya walahi yaushe yaushe kika sanshi da zaki zauna jiranshi, maza ki tashi ki kwashe shanyar nan kifara guga tunda bakida aikinyi

Maryam ta tashi tafara kwashe kayan sai ga yaro yayi sallama wai usman na kiranta

Ranta yayi wani sanyi tana sauri taje ta kai kayan daki tafito don wannan lokacin ba abinda maryam ke son gani irin Usman, ko don batada wanda zataso ne sai shi? Wani mugun so take mashi cikin kankanin lokaci

Fitowar da zatayi da sauri bayan ta kai kayan saide taji anty na ce ma yaron kaje kace batanan an aike ta

Maryam ta tsaya turus tana kallon anty, bayan yaron yafita anty ta juyo ta kalli maryam tace ba firar da zakije baki gama man gugar nan ba

Ran maryam sai suya yake amma dayake rabon ta da hawaye tun bayan rasuwar iyayen ta gaba daya ta manta yadda hawaye suke saide zuciyar ta tarinka suya

Maryam ta juya zuciyar ta na zafi tashiga dakin tafara guga

AUREN DOLE sabon Saloحيث تعيش القصص. اكتشف الآن