part 27

2.7K 156 2
                                    

AUREN DOLE sabon salo
Part 27
Raqiyya bena

Maryam sanye da lab coat dinta fara tas. Ta sanya wani material blue anyi mata gown me kyau ta kawo mayafin rigar ta sanya

Tayi  matukar kyau da ka ganta kaga ainihin bafulatanaji

Babban falon ta iske mummy rike da Aish tana bata abinci

Mummy ina kwana? Ta fada lokacin da take shafa kan Aish, mummy tace lafiya lau Autar mama, dariya tayi tace lallai idan fatima taji maganar nan sai an raba mu

Mummy tace toh yanzu ai kece a gabana maryam ita ba tana gidan mijin ta ba? Dariya maryam tayi tace ni zan tafi Asibity mummy

Mummy tace toh Allah ya taimaka Maryama Amma kifara shiga ki gaida daddyn ku ya ce yana son ganin ki

Maryam tace ok zan shiga

Zaune ta iske shi lankwashe gaban daddy yana famar yi ma daddy magiya akan shidai a maida mashi matar shi

Ta kalle shi fuska a daure tace ina kwana yaya Ahmad, gabanshi ya fadi don shi sam bai ma ji sallamar ta ba, ta matsa kusa da daddy ta zauna tace daddy ina kwana?

Ya amsa fuskar shi dauke da murmushi yace lafiya lau maryama, tace mummy ce tace kana son ganina? Yace eh kwana biyu ban ganki ba shine nace a turo man ke mu gaisa

Dariya tayi tace toh daddy baka zama ne ai shiyasa, yau din ma bansan kana gida ba sai da mummy ta fada

Yace toh nagode maryam kije karki makara Allah ya taimaka kinji? Tace na gode baba .ta tashi ta tafi

Ahmad kam gaba daya a rikice yake tun da ta shigo gabanshi ke tsananta faduwa bai ma san me xaice ba, Daddy yace Ahmad kayi hasarar mata kuma ni bazan taba ce ma maryam ta koma gidan ka ba indai har ba itace tace tana so ba

Bayan wata biyar

Wata biyar kenan da mutuwar auren maryan da Ahmad

Maryam jaye da motar ta kirar matrix fara tass, da ka ganta kaga wadda ke cikin farin ciki da Annashuwa batada wata matsala

Daidai wani katafaren shopping mall ta tsaya, ta cire lab coat dinta a motar ta fito sanye da doguwar riga baqa wadda tayi mata kyau sosai

Maryam fara ce tass kamar yadda kuka sani, don haka duk wani abu me duhu yana mata kyau

Ta rufe motar ta shiga ciki tana tafiya sannu sannu kamar bata son taka kasa, idan ka ganta zakayi tunanin yanga takeyi alhalin hakanan yanayin ta yake

Man shafin ta ne ya qara ta shiga siyowa, tsaye tayi Turus ganin yaya Ahmad tare da zee zee a shopping mall din suna siyayya, zee zee ganin maryam harda wani kama hannun Ahmad take tana maqale wa, shikuma duk sai yaji kunya, karo nafarko kenan da ya fara jin gabanshi ya fadi don wata ta ganshi da mace

Murmushi maryam tayi tace anti zee zee ashe kuna duniya? Rabona daku fa anfi shekara uku, zee zee cikin yanga tace ai sis na bamu labarin ki ai Ashe auren ki ya mutu? Kuma shine kike zaune musu a gida saboda rashin xuciya?

Ahmad kam duk inda jijiyoyin jikin shi suke sun tsinke, whaat? Kar dai ace zee zee yar uwar maryam ce? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un

Jaye hannun shi yayi daga jikin zee zee ya kalli maryam yace maryan ina kika san zee zee? Maryam murmushi kawai tayi tace ai cousin dita ce, itace yayar sister

Wani mumunan faduwan gaba yayi.kafin yayi magana maryam tace toh zee zee ki gaida mamanki da kawu ni zan tafi..

Zee zee kan ta tashiga tsoron yadda yanayin Ahmad ya canza jin ita yar uwar maryam ce, kar dai ya rabu da ita?

A fusace ko Ahmad ya fita daga wajen ya barta nan sororo tana jimami shikuma ya wuce ya ja mota fuuuu ya fita

Maryam zuciyar ta wani irin zafu ta rinka yi mata, yanzu Ahmad harda yar uwar ta saida yayi zinah da ita?  Lallai ya zama dole ta fidda duk wani son shi da takeyi ta baiwa wani chance don tayi auren ta tahuta

Bazata iya zama da miji irin Ahmad ba

Bayan ta isa gida ta zauna tana ta tunanin yadda zata fara kula wani a yanzu, dama mummy ta matsu taga ta fara kula wani

Washe gari kuwa Ta Tura ma Nabeel message cewa yazo tana son ganin shi

Nabeel senior doctor ne a asibitin da take aiki tun ranar da ta fara zuwa ya laqe mata akan yana son ta,ita kuma tace yabari zatayi shawara

Yau kam ta yanke hukuncin fara kula dr nabeel saboda dama dai yana burge ta kawai dai don tana don Ahmad ne ta dakatar dashi

Dr nabeel kuma ba mutumin banza bane don ana shaidar shi a asibitin su shi sam bai kula mata, ba kamar sauran likitoci ba

A hankali a hankali take jin zuciyar ta tafara natsuwa da dr nabeel saboda gaba daya Ahmed ya fita ran ta, gaba daya ta dauka ya natsu bayan rasuwar mami, amma ashe yar uwar ta ma ya koma ma

Ku gafarce ni ina daukan time banyi update ba, insha Allah zan gama duka kafin karshen Azumi
Ramadan kareem


AUREN DOLE sabon SaloWhere stories live. Discover now