Part 4

1.2K 51 0
                                    

💠💠💠💠💠

*BAMBANCIN AL'ADU.....* 💥

🌚🌚
💥

*©® 2018.*

*$tσrч____wríttєn.*
*вч*
_★нawwa м.υ {$mαѕhєr}.★_
*~___________________~*
★★★ ★ ★★★
___________________________
___________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER & HUBBEEY NOVEL'S GROUP@web.facebook.com

*вíѕmíllαhír-rαhmαnír-rαhєєm.*
_________________________
_________________________

*SADAUKARWA:-*_Ga mahaifina *LATE ALHAJI MUHAMMAD USMAN KUMO.* Allah чα ѕαdαr dα rαhαmαrѕα gαrєkα tαrє dα ѕαurαn αl'ummαr muѕulmí...ameen 😭._

*TUKUICI:*

*HASSAN ATK.*
*HUSSAIN ATK.*
_AND_
*KING BOY ISAH. 👑*


⏩7⃣


________Ganin suna neman shid'ewa daga shi har ita da suka zama bak'i a harkar daya zama ko numfashima da kyar suke shak'ansa yasa *JANAN* k'watan kanta da k'yar daga hannun *HAIDAR*,kallonta kawai ya d'anyi da mamakin abunda ya aikata,sai dai kuma ko babu komai hakan da yayi ya d'an rage masa wani kaso na damuwan dake tare da shi a lokacin,d'an kallonta ya sake yi har lokacin idanunta na a rufe ta kada bud'esu,hakan da tayi duk da baya cikin yanayi mai dad'i sai daya d'an saki murmushi ta gefe d'aya.
Lips enta da suka sauya kala kamar tasa lipsick ya kalla,dad'a kyau suka masa a hakan sai yaji kamar ya koma yaci gaba da abunda yake,sai dai kuma bai kai k'arshen tunanin nasa ba muminar zuciyarsa ta kawo masa ziyara tana sake tunasar da shi haramcin abunda yake k'ok'arin aikatawa,har ya runtse idonsa yana neman tuba a gurin Allah,text en mom ya fad'o masa,tunawan da yayi wanda idan har ba idanunsa ne suka ga ba daidaiba kuwa ai ta sanar masa an d'aura masa aure a yau.
To amma da waye hakan ya faru...? mugun bugun daya ji zuciyarsa yayi yasa shi yin saurin lalubo wayansa yana shiga inda yasan zaiga sak'on nata gaba d'aya tunaninsa ya b'ace,binsa ya fara yi a hankali kamar yadda aka turosa,har ya isa gurin da take fad'in
_"Ka bar ganin kun had'a baki da ubanka an d'aura maka aure yau wannan bare sani fasa nawa k'udurinba ka dai ji na fad'a maka...!"_
Again ya sake tuno dai² inda take fad'in
_"ina so ka tabbatar tare da kwana da sanin aurenka da *FARISAH* babu fashi,duk k'iyayyar da kake gwada mata sai ka aureta ko kak'i ko ka so tunda ita ta nunamin tana sonka,duniya baka matar data wuce ta....!"_
Juya maganganun biyu ya shiga yi a zuciyarsa yana son gano wani abu dake k'unshe ciki,kansa ya d'an dafe kad'an yana dad'a rufe idonsa,da sauri ya bud'e yana fad'in
"Alhamdulillah alaa kulli haliin...!"
Rasa abunda zaiyi yayi a lokacin,shin farin ciki ya kamata yayi ko bak'in ciki...? rasa na zab'a yayi saboda kowanne ciki yana jinsa a zuciyarsa,kuma matsayin kowanne 50/50 ne a gurinsa,farin cikinsa a lokacin gujewa auren *FARISAH* da yayi,bak'in cikinsa kuwa yadda maganar mom ke masa barazana idan bai yarda ya auri *FARISA'R* ba zata tsine masa kuma Allah ya isar mata nononta daya sha,tashin hankaline ya sake bayyana a saman fuskarsa tunaninsa bai wuce samun mafita akan case en nasa da mom ba,shi babban abunda yama fi damunsa shi ne yadda mom take neman bad'awa idanunta toka akan abun duniya,bayan tasan su kansu idan ta duba ai basa cikin sahun wad'anda zasu nemi wani abu a gurin wani,idan batun kud'i nema to ko mahaifin *FARISA'R* duk dukiyar daya tara baza a tab'a had'a shi da nasa mahaifinba wato *ALH.MUHAMMAD MAJI DA'DI*.Kawai dai wani ak'ida ne had'e da son bin ra'ayin zuciyarta nak'in talaka data riga ta sawa ranta k'iyayyarsa wanda har yau ya rasa gano dalilin mom na yin hakan.
Idan har ba mantawa yayi ba kuwa kuma a hasashensa,babu akan yarinyar da mom ke fad'in sun had'a baki da dad sai *MARYAM* dake kusa da shi a lokacin,idanunsa a kulle still yake ta faman sak'a da warwara had'e da juyayin kalaman mom a kansa,farin cikin da wani gefe na zuciyarsa keyi ne ya disashe sakamakon kalaman mom da suka mak'ale can k'asan zuciyarsa.Yinin ranar bai samu damar fita duba aikin daya kawo suba,nan cikin d'akin ya lalace kamar majinyaci zuciyarsa cike taf da zullumin abunda zai tarar daga gurin mahaifiyar tasa........

BAMBANCIN AL'ADU.! (COMPLETED)✔Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt