Part 13

722 42 0
                                    

💠💠💠💠💠

*BAMBANCIN AL'ADU.....* 💥

🌚🌚
💥

*©® 2018.*

*$tσrч____wríttєn.*
*вч*
_★нawwa м.υ {$mαѕhєr}.★_
*~___________________~*
★★★ ★ ★★★
___________________________
___________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/

*вíѕmíllαhír-rαhmαnír-rαhєєm.*
_________________________
_________________________

*SADAUKARWA:-*_Ga mahaifina *LATE ALHAJI MUHAMMAD USMAN KUMO.* Allah чα ѕαdαr dα rαhαmαrѕα gαrєkα tαrє dα ѕαurαn αl'ummαr muѕulmí...ameen 😭._

*TUKUICI:*

*HASSAN ATK.*
*HUSSAIN ATK.*
_AND_
*KING BOY ISAH. 👑*


⏩2⃣5⃣


_______Fad'in irin tashin hankalin da Janan ta shiga a wannan lokacin da labarin ya risketa abune mai wuya,tambayoyi ta shiga jero masa
"To yanzun suna ina..? Basu daiji ciwo ba ko..? Ina baby Inteesaar..?"
Yadda ta rikice yasa har ta mantama da tana shayar da Abul-khair wanda Allah yaso haidar ya kula da yadda yaron yake numfashi da kyar saboda yadda nonon ya toshe masa hanci.
Da sauri haidar ya isa gareta ya d'auke baby'n daga saman cinyanta hankalinsa a d'an tashe,kuka sosai yaron ya saki a lokacin daya shak'i cikakken numfashi gwanin tausayi,a rikice take sosai har lokacin da sauri ta mik'e tana son karb'ansa daga hannun haidar shi kuma sai duba shi yake dad'a yi ko da wata matsalar a tare da shi.
"Karb'esa ki rarrasheshi.."
Haidar en ya fad'a lokacin daya tabbatar babu wata damuwa a tare da jaririn,da sauri ta karb'eshi taci gaba da aikin rarrashi,hankalinta duk ya kasu da son jin cikakken bayani game da had'arin da akace su Zeenat en sunyi,safa da marwa kawai haidar en shima yake yana jiran a sanar da shi hospital en da suke
"Hayatee..! ka zauna dan Allah tsaiwan bare maka ba."
'Dan kallonta kawai yayi amma sam ya gagara zaman,musamman da dama kiran waya kawai yake jira ya fice,yana tsayen kuwa kiran ya shigo wayarsa,da sauri ya d'auka ya karata a kunnensa yana sauraren me ake fad'a,hankalinsa a wannan lokacin har yafi d'azun tashi,ba tare da b'ata lokaciba ya fice da mugun sauri ko sauraron janan dake masa maganar ya tsayata baiba,driver'nsu ya kira dan babu tabbacin ya iya driven da kansa,cikin asibitin Aminu Kano b'angaren emergency suka nufa,dialing number Zee da aka kirashi da ita ya sanarma wanda ya kirashin k'arasowarsa,tuni y'an sanda har sun shiga lamarin,duk inda ka duba mutane ne wasu ana shigowa da su wasu kuma fita,jami'in daya iske haidar tsaye ya mik'a masa hannu after sun gaisa ne ya shiga yima haidar bayanin yadda lamarin ya wakana kana ya k'ara masa da bayanin sun samu mutum biyu a gefen hanya wanda ya had'a da jaririya da kuma namiji,sai dai kuma rashin sa'ar d'aya ce motarsu ta kama da wuta wadda jama'a suka gagara kashewa,kafin su da akawa waya su k'arasa gurin,motar ta k'one k'urmus,wanda dukama had'arin nasu bai wuce 25km daga cikin garin kano zuwa k'auyen na *Tsakuwa Babban gari* dake kan iyakar tafiya a hanyarsu ta zuwa port hacourt.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai haidar yake ambata saboda abunda ya fahimta a bayani d'an sandan yana so ne yace masa basu ga Zee ba kenan kome hakan ke nufi..? kwatanta tashin hanklin daya tsinci kansa a ciki abune mai matuk'ar wahala duba da yadda zancen d'an sandan yake a fili kan tabbacin Zee ta mutu a cikin wutar.
Kimanin wucewar wasu awanni da suka d'iba tare cikin asibitin wanda zuwan haidar en ya bada damar da aka shiga da su don tabbatar da samuwar cikakkiyar lafiyarsu bayan taimakon gaggawa da suka samu kafin zuwan nasa,sun jima sosai suna jiran a fito dasu kana daga bisani kuma likitocin suka fito bayan gama aikin.
Tare suka shiga d'akin da Sadeeq en yake wato mijin Zee sun tarar da shi yana bacci sai kafafunsa dake sak'ale a sama hannunsa na dama a nad'e shima duk da bandages sai y'an kukkujewa da ba'a rasa ba a jikinsa,wata nurse ce ta shigo d'auke da Inteesar ta mik'a musu ita kana ta k'ara musu bayani da babu wani rauni ko buguwa data samu yarinyar tana cikin k'oshin lafiya,amsarta haidar yayi dai² lokacin da aka sake turo k'ofar aka shigo,dad ne ya shigo wanda suna had'a ido da haidar take hawaye suka shiga sakkowa a fuskar haidar en,duk iya dauriya da jarumtar da yayi a d'azun ganin yarinyar da kuma shigowar dad tuni suka k'arasa karya lagonsa,hak'uri dad ya shiga bashi da bashi baki amma ina zuciyar haidar ta riga da ta gama narkewa abun har ba'a cewa komai,dad ne ya amshi Inteesar daga hannunsa sannan bayan sun gaisa da police en,yayima dad bayanin abunda ya sani da kuma abunda yaji daga bakin mutanen da suka fara kai musu agaji,daga nan dad ya sallami polisawan sannan suka fice dan komawa gida a kuma san halin da ake ciki kasancewar har zuwa lokacin babu wanda ya san abunda ke faruwa a gida sai janan,bayan wucewar wasu y'an sa'o'i suka k'araso jikin kowa a sanyaye cikinsu,dai² lokacin da suka k'araso gida Inteesar ta farka daga baccin da take nan ta shiga rera kuka,kukan jariri yasa mom dake d'aki da duk abun duniya ya gama binneta fitowa da niyyar dubawa saboda zaman d'aki ya fara isarta zuwa yanzun dama kuma ba sabawa tayi ba kawai dai ta tsiri hakan ne dan kawai ta gujewa had'uwa da Matar mijin nata,sakkowanta yayi dai² da lokacin da itama Annah ta k'arasa cikin parlour'n tana k'ok'arin amsar Inteesar a hanun dad tana jero masa tambayan inda suka samo yarinya jaririya gashi sai kuka take da alamun yunwa a tare da ita duba da yadda taketa k'ok'arin danna hannunta a baki,karb'arta tayi tana ta son rarrashinta amma abun ya gagara dan kuwa kusan zamu iya cewa abunda take yi a banza,k'ok'arin neman abunda zata bawa yarinyar ta fara inda su kuma su dad suka zauna jigum babu mai iya magana tsakaninsa da haidar,duk wani k'ok'ari kam Annah tayi shi sai dai har lokacin Inteesar tayi kukan har ta gaji muryanta ya zamana ko fita baya yi,kallon su tayi da damuwa nan itama mom ta nemi guri ta zauna tana yatsina fuska da son jin labarin yadda akayi suka samo jaririya
"Dan Allah Alhaji kuyi mana bayanin inda mahaifiyar yarinyar nan take,kunga muna shiga hak'k'intata gaskiya,dubafa kaga yadda saboda kuka har muryanta ya dashe,dan Allah ya kamata mu taimaka mu maidata gurin mahaifiyarta idan tsintartama kukayi muje ayi cigiya ko Allah zaisa a dace...Gaskiya baran iya jure ganinta a wannan halinba ni dai..!"

BAMBANCIN AL'ADU.! (COMPLETED)✔Where stories live. Discover now