Part 6

970 46 0
                                    

💠💠💠💠💠

*BAMBANCIN AL'ADU.....* 💥

🌚🌚
💥

*©® 2018.*

*$tσrч____wríttєn.*
*вч*
_★нawwa м.υ {$mαѕhєr}.★_
*~___________________~*
★★★ ★ ★★★
___________________________
___________________________
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE NOVEL'S GROUP@web.facebook.com

*вíѕmíllαhír-rαhmαnír-rαhєєm.*
_________________________
_________________________

*SADAUKARWA:-*_Ga mahaifina *LATE ALHAJI MUHAMMAD USMAN KUMO.* Allah чα ѕαdαr dα rαhαmαrѕα gαrєkα tαrє dα ѕαurαn αl'ummαr muѕulmí...ameen 😭._

*TUKUICI:*

*HASSAN ATK.*
*HUSSAIN ATK.*
_AND_
*KING BOY ISAH. ??*

⏩9⃣

________Ya jima kafin ya samu yayi bacci saboda damuwan dake manne cikin zuciyarsa,tunaninsa anya kuwa mom data furta wad'annan kalaman akansa zata iya aiwatarwa ko kuwa,wata zuciyar ce take rinjayansa akan ba gaskiya bane hakan kawai dai tana yi masa barazana ne akan yak'i amincewa auren *JANAN*,haka ya gama sak'a da warwara akan halayen na mom yayi bacci cike da fargabar me gobe zata haifar..

B'angaren mom kuwa bayan dad ya sallami *HAIDAR* ba k'aramin b'aci ranta yayi ba da abunda alhajin yake mata a y'an kwanakin akan yaron,ita a nata ganin hakan sam bai kamata ba a matsayinsu na iyayensa da kowanne yake da iko da shi ai ya kamata itama a bata nata hak'k'in,amma akan me dad zai bari d'an nasu ya auri matar da ba musulma ba,kuma tsabar gulma wai sunanta *MARYAM* saboda rainin wayo don kawai ayi tunanin musulma ce,kuma ko bama haka ba ai samata sunan cin fuska ne ga ainahin mai sunan a wato (Nana Maryam mahaifiyar Annabi Isah A.S),haka dai mom tayi ta fama da nata sak'ar inda a k'arshe tayi nasarar watsi da tunanin had'e da shirin bacci abunta....

Shima dad a nasa b'angaren yaso yiwa matar tasa nasiha game da sha'anin abunda yake faruwa,sai dai ganin tayi wearing wani fuskan yasa shi jan bakinsa ba tare daya furta mata komaiba ya dai barta har zuwa lokacin da zata sakko,amma kam tabbas ya k'uduri aniyan nusar da ita hanya,idan kuma ta kafe tofa lallai shima zai koma gefe ya zama d'an kallo har zuwa lokacin da Allah zaiyi hukuncinsa.....

********

Lokacin sallah da taga yayi yasa ta fitowa daga d'akin nata tana sake d'aga kanta sama dan tabbatarwa,a wani y'an robobi da suke d'iban ruwa idan zasu shiga band'aki ta d'auka tana nufan toilet en nasu na gargajiya,bayan ta gama abunda ya kaita ta fito,nan ta tsuguna a tsakar gidan tana alwala duk abunda take tana yine tana tuna yadda *HAIDAR* ya koyar da ita cikin y'an kwanakin da suka gabata,har ta zo shafan kai,Annah ta gani tsaye gabanta tana kallonta da wani irin yanayi a fuskarta,not minded taci gaba da abunda take yi har ta k'are sannan tayi hanyan d'akinta,Annah dake tsaye nan bata iya magana ba ta mara mata baya,lokacin data shiga tuni *JANAN* har ta tada sallah,magana Annah tayi tama *JANAN* amma ina bata ko kulata ba,ganin haka ran Annah ya b'aci,sunkuyawa tayi ruku'u nan ko Annah ta dunk'ule hannu ta d'irka mata duka a baya,duk da taji shigar dukan hakan baisa ta sallame ba,mamaki Annah tayi ta fama da shi,gefenta ta tsaya tana k'are mata kallo har ta idar,ganin tayi sallama yasa Anna cikin hargagi ta fara magana
"Keeee! *JANAN* me kika aikata haka...?"

"Sallah fa nayi Annah...!"

Yamutsa fuska Annah ta sake yi saboda jin an ambaci abunda bata sani ba
"Mene shi en kuma to...?"

"Annah..! yana daga cikin nau'ikan bauta ne da *UBANGIJI* yafi so..."

Juya maganar *JANAN* ta shiga yi a ranta ganin zata bawa kanta wahala kuma dai ita bata san wani *BAUTA* da kuma *UBANGIJI* ba bare ta gane ma'amar abunda suke nufi ta kalli y'ar tata
"Me yasa kike irin wannan abun da naga kina dungurawa a k'asa...?"

BAMBANCIN AL'ADU.! (COMPLETED)✔Where stories live. Discover now